← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 130

Sashe 13

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitarshi ta tada faseelat daga bacci, ta tashi tafara yan gyare -gyaren gidan har ta gama ta shiga toilet tayo wanka, tana fitowa ta danyi shafe-shafe sama-sama ta saka riga da sket na atamfa jar atamfa tayi mata kyau sosai dukda de bawani makeup sosai tayi ba ta fesa perfumes ta haye saman gado ta jawo wayarta tabude data, messages nagama shigowa tafara shiga group din "mijina aljannata"wanda maman amira tabada aka sakata saboda ana matukar karuwa sosai saboda firarsu da posting da ake musu duk akan mallake mijine,

kwatsam se taga message din maman amira tace "I'm back friends thanks for your dua,mundawo lpya se kunzo ansar tsaraba"

Faseelat tai murmushi tayi mata magana a PC "anty barka da dawowa, inafatan kundawo lpya"

Bayan yan sakonni maman amira tabude message nata ta tura mata "lpya lau faseelat ya kk"

Faseelat tace "lpy ta lau ina diyata amira?"

Maman amira ta dauki pic din amira dake bacci ta turawa faseelat tace "gata tana baccin safe"

Faseelat tabude pic din "wow "tafada ta dade tana kallon pic din itade Allah ya sanya mata son amira, ta turawa maman amira "sleeping angel knan anty amira tafi ki kyau sosai kamar bake kika haifeta ba "

Maman amira ta tura mata smile face tace "nabaki ita ,ai amira duk daddinta ta dauko don harma ya fita kyau "

Faseelat tace "Allah sarki"

Maman amira ta tura mata pic dinsu ita da mijinta da amira a kasar waje

Faseelat na ganin pic din seda ta mike zaune ganin handsome man din da ke acikin pic din tadade tana kallonshi, sannan taturawa maman amira "wow kunsha kyau wlh, anty kinyi dacen miji "

Maman amira tai dariya tace "nasani faseelat shiyasa nake mutuwar son shi kuma nake kokarin faranta mashi rai kullum ,kema Allah yabaki kamar shi.

Faseelat tai murmushi "anty kenan aini jiya aka daura min aure "

Maman amira tace"kice amarya kike to Allah yabada zaman lpya da kazantar daki, bari na sauka se munkara haduwa"

Faseelat ta tura mata "amin anty to semun kara haduwa"

Itama se ta kashe datar ta, ta koma ta bude picture dinsu maman amira tana cigaba da kallon mijin Nata, yana dariya ya dan rike kumatun amira, itama maman amira ta riko hannuwanshi dikkansu sunata dariya, ta sa hannu ta shafi pic din tace "my dream husband "
Ta kure mijin da kallo ,fari ne sosai sumar kanshi baka kirin tasha gyara yana da dogon hanci da idanunshi farare matsakaita labbanshi tabi da kallo they are pink in color, tabi fararen hakoranshi da kallo dariyar ta mugun yi mashi kyau,se kawai ta Saki murmushi, se kuma ta tuna da fuskar nata mijin, Wanda so daya ta taba ganin dariyar shi, ta kuma tuna darensu na jiya, tadanyi shiru tana nazari tama saka wayar a key, cikin ranta take tambayar kanta miya hana khalil kusantar ta jiya? Romance only amma shikenan tana karantawa a novels yanda maza keyin release kenan har ya samu gamsuwa a taba ta kawai, tai shiru can tace "maybe dan yana farin shiga ne zuwa gaba nasan ze fahimta"
Ta tashi ta koma falo ta bude pic dinsu maman amira tai zooming fuskar mijinta ta cigaba da kallonshi.

Khalil na shiga gida dangi wadanda basu tafi ba suka fara zaulayarshi "ango kasha dadi ina kabaro amaryar "ko ansasu beba ya shiga wurin hajiyar,

Hjyar na wanka se ya zauna jiranta har tafito, tana zama ya duka gaisheta ta amsa tana kallon fuskarshi so take tagano wani abu amma bata fahimci komi ba tace "ya kwanan faseelat? "

Yace "lpy lau "

tace "yayi kyau, dama bari nai agama biki kadan natsu tukunna inmaka maganar, kai ne zaka cigaba da zama a shagon mahaifinka saboda ni ban yadda kabarwa wannan yaron shagon shi kadai ba, donhaka nakeso ka rika zama da kanka shagonma se yafi bunkasa. "

Tunda take magana yake kallonta, zuwa yanzu yagama gano hjy batason faseelat, yace "amma hjy kinsan ina zuwa school kuma da na dawo dole ina bukatar hutu, gaskiya hjy bazan iya ba, kibari zansamu wani yaron se inhada su da salen "

hjy tuni tacika tai ta tum tace "khalil ni kake fadawa cewa bazakaiyaba? Ni khalil? Lalle Kayi aure ai dole ka nunamin ka girma"

Hankali tashe yace "hjy kiyi hakuri Dan Allah ki fahimceni wlh abubuwa cabe min zasuyi "

Hjy tana banka masa harara tace "jira kaji khalil kai ba kai girman da zaka bijerewa abinda nasaka ba, dole ko kaki ko kaso se kayi Kana jina ai"

Khalil yace "naji hjy sede senan da sati zanfara zuwa lokacin na koma school tunda ina hutu yanzu"

Ta ballamai harara "ni zaka fadawa kana hutu? Toni bansan wannan ba goben nan zakafara fita sakare kawai "

Kamar zeyi kuka yace "to hjy "ya mike ze fita yasan inhar yana son zaman lpya toyayi yadda tace kawai inba haka ba yabani da masifar ta, don duk ta sauya ko dan wasan da suke na uwa da da anbari saboda aurennan.

tace "a, a ina zaka? Dawo kazauna gashi can ana hadama amarya breakfast se katafin mata dashi "

Ya dawo ya zauna ba dan ya soba, shi gabadaya kanshi ya kulle besan taya ze shawo matsalar hjy ba, ya daga kai ya kalli agogon bangon da ke dakin karfe takwas da minti 5, so yake ya koma wurin faseelat amma ba hali, yana nan zaune aka gama abincin, aka zubo shi a cooler har siyama tafita hjy takirata "jeki zubo ma yayanki yaci nashi anan "

Khalil ya dago yana kallon hjy, ya daure yakama bakinshi yayi shiru aka zubo mishi ya fara dan tsakura.

ummi kau sama-sama tai bacci tunanin ta kacokam ya tafi ne akan faseelat, ya daren su ze kasance, har garin Allah ya waye, zuwa yanzu zuciyar ta nabata faseelat na bukatar temako saboda abubuwan da take tunanin Sun auku, tagaza hakuri taje ta samu fatouma ,tabata wasu magunguna a leda tace
[7/12, 10:59 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*

1⃣8⃣

Tace fatouma" kede ba yarinya bace dukda bakiyi aure ba amma zakiiya gane wasu alamu in wani abu yashiga tsakanin namiji da mace, kije gidan faseelat inde kinga wani sign to kibata wadannan magungunan duk jikinsu da bayanai tayi amfani dasu,amma wannan karkibata keda kanki nakeso ki dafa mata shi ta shiga nasan ita bata iya komai yanzu"

Dije tashigo dakin tace "haba yaya, fatouma zaki aika gyara ?ai abun ba na yara bane ba, bani ke fatouma i tafiyarki ni da kai na zani, maybe ma Tana can ita tana sanaar kuka".

Fatouma sam bataji dadi ba taso taje tayo ganin Kwam tana tuttura baki tabar dakin .

Dije ta sabi hijabinta tanata sauri ummi tace "wlh dije jiya banyi barcin kirki ba inata tunanin faseelat, tundazu nakeso nakirata amma se nafasa Don karta kara tadamin hankali "

Dije tagama kimtsawa tace "nide natafi ki kwantar da hankalinki insha Allah lpyarta lau "tafita zuwa gidan.

Mashin na ajiye ta tafara kwankwasawa ,faseelat na tsakiyar kallon pic din mijin maman amira gabanta har wani dukan ukku ukku yakeyi taji ana buga gida, tai sauri ta ajiye wayar tatashi taje tabude kofar, wa zata gani ta rungume dije tana jawo hawaye, dije ta jaye ta daga jikinta tace "miye kuma na kuka? Daga zuwa na karkisa inkoma "

Faseelat ta share hawayen tai tsaye dije tace "to nan zaki barni muje ciki mana"

Faseelat tai gaba tana tafiya, dije tabi tafiyarta da kallo tanaso ta gano wani abu amma lpya lau ,suka Shiga ciki,

Suna zama dije tace "ina megidan? "

Faseelat tace "bayanan ai ya fita tunda safe"

Dije tace "halan jiya bemaki komi ba ?"

Faseelat ta dukar dakai tana jan yatsa dan kunya ta girgiza kai,

Dije tai shiru tace "to yanzu de ga wadannan magungunan da zaran ya kusanceki kiyi amfani dasu,sannan faseelat plss kirike sirrin mijinki da gidanki ko umminki bakomi yakamata kina fadamata ba kinaji ai?kuma ki kula da jikinki, ke me kyau ce Allah yamaki kira, karkiyi sake kidage kindega yadda yaya take dukda ta tsufa, amma bata daina gyaran kanta ba, daga karshe kiyi hakuri da yadda kikasami mijinki kinsan kowa da irin yadda Allah ya halicceshi, ko yaya yake kiyi hakuri duk sadda ya nemeki ki amsa kira, kinsan malaiku na tsinewa macen da mijinta ya nemeta taki, da wadda take cewa tana haila, ki kula sosai, mu kuma yau dinnan in Allah yayadda zamu koma nasan se munzo suna kuma"

Faseelat tafara hawaye ,

dije tace "nide yanzu ma zantafi seki tayi ke daya, "tamike tsaye, faseelat tai sauri ta rungumeta dije na aikin rarrashi tasamu tabar gidan.

Bata dade da fita ba khalil yashigo faseelat na zaune tayi tagumi tana kuka yana shigowa tai shiru, tana goge fuskarta, silver cooler dake hannunshi ya ajiye ya je wurinta,

Ya zauna kujera daf da tata kanshi kusa da fuskarta yace "lpya faseelat? "

Tai shiru yace "I'm sorry natafi nabarki hjy ce ta kirani ga breakfast tace akawomiki "

Faseelat ta mike kurum batare da tace komi ba ta nufi kitchen ta dauko plates da spoons ta kawo tana cikin zubawa yace "ki zuba kici kawai ni naci abinci "

Tadago ta kalleshi ta meda kanta tazuba ta zauna tanaci asannu, ita faseelat cin abincinta yanajan lokaci koya takejin yunwa bata iya cin abinci da sauri ba, Yanzu haka yunwa takeji saboda rabonta da cin abinci tun jiya da safe, tanacin abincin ya kuramata ido tundazu yake kallonta gabadaya shaawarshi tagama tasowa ,

Itade cin abincinta kawai takeyi bata ko kallon wurinsa, ta dauko spoon zata kai baki ya rike, takai duba wurinshi yana mata kallonnan me ban haushi ya zukunna gabanta ta sakarmashi cokalin ya debo abincin ya kai bakinta tai sauri ta sadda kai, yace "kunya ta kikeji ne? Bayan munzama daya nazama ke kinzama ni "

tai shiru ta kyaleshi yakura wa tudun boob's dinta ido can zuwa ya ajiye spoon din yace "it your food I'm leaving the room"

ya tashi dakyar yajanye jallabiyar jikinshi yajuya ya tafi toilet,
Chapter 13 · 0% Book details