← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 130

Sashe 80

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin kaskantar da kai yace "hjya dan Allah kiyi hakuri wlh yarinyar nan baita kadai take ba tana da iska, tunda ta dawo dede nabata labari take kuka tanaso tazo ta baki hakuri kiyi hakuri dan girman Allah"

Hjya tai banzar dariya "hehehe he! khalil nifa na haifeka nafika sanin duniya nawa kake yanzu, to wannan karyar batai ba sakarai solombiyo bawan mata, katashi kaje ka saketa saki ukku zaka mata ringissss dan kai daita har abada wlh"

yayi shiru ranshi na zafi tabbas jamila batai ba amma he love her kuma tausayinta yake dagayin aure se saki, kuma shi yatsani ma saki kuma bayason yabawa wata danshi ko diyarshi dan baya da tabbacin zata rike shi amana tundade jamilar yarinya ce kuma tanasonshi maybe ta gyara, yanajin tsoro kar yakuma samun wadda tafi jamila hauka shide yasan yayi missing yayi missing mace me tsada,

Murya sanyaye yace "hjy ayi hakuri de aduba ajanye maganar sakinnan she's very young kuma kiduba baatashi yi mata aure ba amma akabani ita, iyayenta bazasuji dadi ba, kiyi hakuri hakan baze kara faruwa ba ,kiyi hakuri kodan cikin jikinta taci albarkacin shi Allah mafa yatsani Saki hjy "

hjya ta zaro ido "Allah ko ustaz alaramma ash sheik khalil, toni ina ruwana da iyayenta aida nasan basu yi mata tarbiyya ba da bazanje ba, tobari kaji wlh tallahi seka saketa dole karabu daita ko kazaba koni koita shasha "

Khalil ya dago fuska Yakalleta yace "haryanzu hjy baki lura ba? Baki fahimci abinda ke faruwa ba, ni bawani so na musamman nakewa jamila ba,akan wanda nakewa faseelat hjy ki tuna baya mana yakamata ace kin dau darasi Dan Allah kiyi hakuri karki matsa na saketa kinga fa siyama na wurinsu abun ze zama matsala, zanwa jamila magana zata zo tabaki hakuri kuma bazata kara ba "

Hjy tace "aikoni nadauki darasi amma nariga nagama daukar shi daga gun jamila de, kuma su sako min siyamar seme shikadai ne autan maza kai seka saketa fa seka Saki jamila dole yarinya mayya marar tarbiyya me zaai daita yo wlh danma cikin jikinta ya tsufa da se abarar dashi dan gudun hada zuria da mahaukata "

Hawayen bakin ciki ne suka zubowa Khalil ya share hawayen yace "nide hjy kimin uzuri akan wannan kimin alfarma kibarni daita,dan Allah "

Ta tabe baki ta dora hannu a gemu tace "to ita kazaba kenan to Allah yayi maka albarka kayi dede katashi kabarmin gida katafi can gun matarka karka sake dawomin anan inde ba sakinta kai ba "

Ta juya ta shige daki khalil yabita da kallo, sosai yaji tausayin kanshi yasa hannu ya share hawayen fuskarshi ya mike ya bita daki yana zuwa ze shiga da karfin tsiya tace "karka shigominnan ka koma can wurin matarka kada insake ganin ko meka ma dakai anan"

Yayi tsaye cikin rashin abunyi, itako ta shige bedroom, yayi kusan 15mnt a tsaye sannan ya juya ya fita jikinshi a mace,

Tuki yake yana neman mafita koda yaje school kasa komi yayi dole ya koma gida, ya samu jamila nata kokarin yin girki his favorite shinkafa da wake da salad da yaji,

Beko tsaya amsa sannu da zuwa da take mishi ba ya shige daki ya haye gado,

Wani mugun zazzabi ya rufeshi yaja zanen gado ya rufa,

Jamila ta biyoshi tazo tai tsaye murya sanyaye tace "yaya baka lpy? Me yasameka? Inkawo maka magani kasha sannan ka kwanta"

ya yaye zanen yanajin haushinta yace "ba dama haka kikeso ba to ga irinta nan seku kasheni ku duka ku huta "yakoma ya rufa

Ta fiddo ido waje "yaya bangane ba fa mekake nufi "

yamata banza tagaji da surutu ta koma kitchen,

masassara yake amma tunanin mafita yake tunani yayi yaje yasamu kawu manu suyi maganar yaje yabawa hjya hakuri maybe adace,

Dan gaskiya beyiwa iyayen jamila adalci ba in ya saketa daita kanta jamilar saboda tana da gaskiya itama,da wannan shawarar ya tsaya anjima ze koma dukda de yasan ba saurarenshi zatai ba amma ze gwada saa,

atanadar min barka da salla ta fan's 🤣zan zuba ido jiran jin alert ran salla jibi... 🤗😁
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*

7⃣0⃣

*Dedicated to my lover (Mrs Ibrahim)* *I love you badly😍,Allah yabawa teeman mu lpy*

Hankali tashe yayi zaman dirshan agabanta ya rungumota jikinshi wasu tsokoki yagani a gun ya saki kara yana kuka yake girgizata "faseelat dan Allah karkimun haka karki bari cikinnan ya fita "

Faseelat ko batasan halin da take ciki ba don hankalinta ya dade da barin gangar jikinta ya cigaba da kuka yana kara ya kuma rungumeta tsam a jikinshi difff numfashin faseelat ya dauke wanda shi besani ba,

Aisha jin karar shi tayi yawa yasa ta dakata da chatting da take ta zaro ido waje tace "innalillahi karde ya kashemusu diya? "ta ajiye wayar ta fita daga dakin da gudu ta nufi dakin faseelat, tana zuwa ta murda handle ta tura kofar, abunda tagani seda hanjinta suka motsa jinin har yakusa kawo bakin kofar dakin ga faseelat zindir rungume a jikinshi yanata rusa kuka da ihu,

Aisha ta zaro ido ta rufe baki da hannunta dake rawa tai tsaye takasa shiga ciki ,

Amira naganin Aisha ta gudu itama ta biyo bayanta tana tafiya ahankali saboda tsoron da takeji zuciyarta nata harbawa da karfin tsiya,

Fahad yana ta kuka besan ma Aisha ta shigo ba yakasa temaka wa faseelat ya kaita asibity don baya cikin hayyacin shi,

Bazato Aisha taga jini gabanta, se sannan ta kara zaro ido tai cikin dakin dasauri ganin jinin daketa zuba, ta bude wardrobe din faseelat ta zaro shirt da single zane ta iso wurin da suke jikinta nata rawa tace"yaya kasa mata kayanta ka kaita asibity jininta ze kare "

Fahad ya dago face duk hawaye yace "Aisha ta mutu ko? Na kasheta wayyo Allah na "

Aisha ta dafa shi tace "bata mutu ba yaya kasa mata kaya mutafi asibity jininta na zuba "ta mika mai kayan,hannunshi duk jini yana rawa ya amsa ya rikesu ya dago fuskar faseelat yaga ko numfashi batayi yakara rikicewa yana kiran sunanta da karfi,

Aisha na tsaye hannunta yakasa barin bakinta duk ilahirin jikinta nata rawa kunsan jini beda kyan gani bare wannan da yayi yawa,

Amira tana dari dari ta shiga dakin ganin abinda ke faruwa yasa ta firgita ta fiddo ido waje zuciyarta takara gudu wanda har kirjinta yake dagawa sama,

Kamar ance ta kalli kasan ta, ta ga jini har yazo kafanta ,ta sulale wurin a sume,

Aisha batasan da shigowar amira ba tana ta kallonsu ,kamar ance ta kalli kofa ta hango amira kwance cikin jini,

Aisha tafasa kara da gudu ta isa wurin amira tana kuka ta tallabo ta ta rika tapping face dinta "amira! Amira !! "shiru amira bata amsa ba idanunta a rufe,

Aisha na kuka ta dauketa batako kara waigen su fahad ba tai waje ko mayafi bata tsaya dauka ba se key data dauka akan kujera tafita ta shiga mota tabar gidan takama hanyar asibity, tana tuki tana kuka,

Karar da Aisha tayi ne ya medo fahad tunaninshi sauri sauri yasawa faseelat riga ya dora mata zanen ya daukota ya fito yasata a mota gidan baya ya shiga ya figi motar, megadi bema ida bude gate dinba fahad ya fita da motar da speed up,

tuki ne kawai yake amma hankalinshi baya tare dashi da temakon Allah suka isa alhayat prvt hospital,

Ya bude motar yana kuka ya dauko faseelat dake lifeless tana ta bleeding ya shiga daita da gudu,

nurses suka tarbeshi aka dora ta akan gado aka tukata zuwa emergency room, fahad ya zube akan gwiwowinshi ya rufe fuska da tafukan hannaye yana kuka me ban tausayi da karya zuciya,

Itama Aisha a asibitin takawo amira dan akwai specialist doctors a asibitin suna kokari sosai wurin gudanar da aikinsu, anbasu room ansawa amira ledar ruwa an kuma yi mata alluran bacci don ta samu hutu, Aisha na zaune gefenta tai tagumi lokaci to lokaci hawaye na zubarmata ,

ya omer yana da wani friends da suka hadu a facebook tun yana Niger da yadawo Nigeria sun zama friends sosai dan suna kawowa juna ziyara akai -akai tun yana Niger yake dora pics dinshi da faseelat a facebook page nashi, friend din seda ya taya omer yafada mishi matar aure ce sister dinshi ce , duk da haka friend din yayi saving din pic din saboda sun burgeshi sosai ,shima yakan dora pics din kuma omer nagani sede ya mishi godiya,

a asibitin yake aiki karamin likita ne ya kanyi dressing small injures allurai har da magani yakan bada, ya fito daga office dinsu yaga anwuce da faseelat akan bed gashi awarwatse fuska a kumbure ga jini duk ajikinta, inda besan ta sosai ba baze iya gane ta ba ,
Hankalin shi ya tashi ba tsayawa ya fiddo waya ya dannawa omer kira,

Omer da yagama waya kenan da fadilarshi kiran abokinnasa bello ya shigo wayar, ya dauka da murmushi kan fuskarshi yace "likita manyan gari yau antuno dani kenan"

Doctor bello da becika hayaniya ba kamar de omer sede har ma yafi omer shiru shiru, muryarshi very cool yace "hold on, yanzunnan naga ankawo wata patient me kama da sisternka tana ta bleeding I don't know ko idona ne se naga kamar ita "

omer dake kwance ya tashi zaune kanshi na sarawa gabanshi na faduwa yace wa bello "waya kawota mace ko namiji? "

Bello yace "namiji wani dogo fari kyakkyawa yana da saje, shima de hankalinshi a tashe dan se kuka yake"

omer ya bata fuska kamar ze kuka zuciyar shi a cunkushe yace "itace wlh dan Allah kadubamun room da zaakai ta gani nan zuwa yanzunnan"

difff yakashe kiran ya dafe kai yanajin kamar yayi kuka kamar an tsikareshi ya tashi yayi dakin ummi dasauri da key dinshi a hannu ,
Chapter 80 · 0% Book details