← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 130

Sashe 53

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Seda akaiwa ruwan da zatai wanka, hadin turare me kyau sannan ta shiga tayi wanka tafito aka mata wani makeup din again tasaka green din atamfa wadda da kaganta kasan ankashe kudi, ta mata kyau sosai mayafinta black,

Ganin akwai time friends suka fara nasu hudubar telling her yadda zata zauna da tunkiyarta,

5:30 tana gaban baba babba shi ba waazi yayi bama sede akirashi fada, yana fadamata tayi hakuri da yadda ta samu mijinta da yanayin zaman gidan beso ta kuma dawowa zawarcinnan, tai ta kuka daga nan yamata addua lokacin motocin kai Amarya sunzo,

Fuskarta a lullube dije tasata mota suka tafi gidanta, motoci birjik harda wadanda basu sami mutane ba,

lokacin da suka shiga gidan yanmatannan inba guda ba ba abinda sukeyi,

Suna shiga main falo na gidan suka kara muryoyinsu, su anty kulsum na zaune se wani kallon banza suke masu har aka shiga ciki,

Aisha tunda taji kugin motoci ta tashi ta shige toilet ta rage idonta ta fito ta haye gado tana jin mugun bakin ciki,

Faseelat na zaune kan bed so daya ta daga kai takalli room din takoma cikin mayafi,

Ba a tarbi yan kai amarya da komi ba dukda de daga hotel akai musu order abinci amma anty kulsum tace bazasu ci shiba,

Bayan anyi Maghreb akasake wa amarya kwalliya ta zuwa dinner, kwalliyar da tafi duk gayun da tai haduwa ,ta saka white gownt dinta da black head se net shima white wanda ta rufe kai dashi,

Sunata daukarta pics karfe 7:15 akazo daukarsu friends nata suka fito daita akasata a motor da fahad ango ke ciki ,
Saura suka shishshiga suka nufi City Hall,

Tunda ta shiga fahad ya rasa natsuwarshi kamshin turarenta ba normal kamshi bane ,ya matsa ya yaye net din fuskarta ta kalleshi ta sakar mai lovely look,

Kusan rudewa yayi ganin yadda takoma, yana ta kallonta yace "u look gorgeously cutie"

Batace komi ba ya jawota jikinshi asking her "kinci abinci kuwa? "

Ta girgiza kai ya harareta yace "why? "

Tai masa rada saying "my stomach is full of happiness "

Yayi dariya "really? "

Tai nodding kai ya dauko holandia, kamar yasani be sha ba,

Yana kallonta yace "oya open your mouth and drink some of it "

Ta girgiza kai tace "nakoshi fa plss kabarni "

Yace "noo I Insist kisha koda kadan ne"

Ya bude murfin ya dora mata a baki ta dansha kadan yace "ko kefa "

Sabeer dake driving yana kallonsu ta cikin glass yace "da akwai mutum fa karkumanta "

Da faseelat da fahad sukai dariya, suna makale har aka isa hannunsu sarke da na juna suka shiga hall din ana ta masu tafi ,

Suka hau high table shi kuma yana sanye da yadi black anmasa kwalliyar golden, hular shi ma black and golden color,

Suna zama akafara daukarsu pics, batare da wani bata lokaci ba MC yafara gabatar da abinda yakawo su,

Kowa na zaune akan seat dinshi maaikata birjik sunata serving nasu, abun burgewar ga fararen fata nan cikin coat dinsu sunyi attending event din,

Acan gida anty kulsum ta matsawa Aisha akan tazo su tafi dinner din taki cikin jin haushi tacewa sauran "kutashi mutafi tunda haryanzu bata waye ba aikije ki nunawa duniya kina murna "

Suka tafi cikin motar anty kulsum din,

sadiya dabata jeba dukda de batada wani shekaru tace "anty gwara da bakije ba ai kazantar da baka ganiba tsafta ce "

Lokacin da suka isa su fahad na yanka cake, ya dauko cake din yana binta da mayen kallo yasakamata abaki,

Ta dan gutsuri kadan ta debo ta mika mashi abaki ya bude ya amshe yasa hannu daya ya rike hannun nata yana lashewa yana kallon idonta,

Cikin burgewa da smiling a faces din mutane suke masu tafi,

Anty kulsum ta kumsa ta juya ta kalli nadiya tace "kina ganin abun haushin da nike gani? "

Nadiya taja tsoki tace "ina gani mana anty "

Kulsum tace "ji nake kamar in matso shegiya inta jibga "

Nadia tana dariya tace "temakamana anty kar yaya ya maki rashin M "

Suka samu seat suka zauna suna kara baza ido suna lura da abinda ke faruwa a cikin Hall din,

Bayan wani lokaci aka kira Amarya da ango kan stage don su cashe su nuna farin cikinsu,

Wata love tone aka sa masu me sanyaya zuciya ,

Faseelat tai tsaye taki rawa, fahad ya matsa ya ruko bayanta suna dan jujjuyawa yana ta kallonta, aka dau tafi, se kara matseta yake , kamar ze medata ciki, kunya duk ta dabaibaye faseelat sanin tarin mutanen dake wurin kuma video recording ake,

su anty kulsum itada kannenshi kamar suyi hauka ,

Suka koma suka zauna akafara kiran mutane suna takawa akan stage ko da aka kira su anty kulsum har sunbar wurin haushi be barsu Sun tsaya ba, ganin yadda yaketa nan nan da amaryarshi kamar ze medata ciki,

Karfe 10pm aka gama dinner din sunyi kusan more than 3hrs,

bayan ansaka faseelat a moto kowa ya shiga tashi suka nufi gidan amarya,

Ahankali fahad ya ke yawo da hannunshi saman hannun faseelat yana dan wasa da yan hannunta ,

Faseelat tai shiru tanajin feeling na taso mata,

Asannu ya bude fuskarta ya kai baki kan nata yafara kissing dinta,

Faseelat da takejin feeling tuni tafara meda mishi martani abu yayi kamari jin tana medo mishi ya tallabo kanta gabadaya suka cigaba da kissing juna, cikin motar bakajin komi se sautin kisses dinsu,

Sabeer dake driving hankalinshi na can yana tunanin fatouma don ta mishi kusan suna yanayi da faseelat sede faseelat tafita diri me kyau batare da yasan abinda ke faruwa ba sede yaji sautin kisses ta madubi ya kallesu ya dafe kai dukda de shi ba irinsu bane seda joystick dinshi ta harba ,

akagare yake su isa yasamu ya tafi wurin radiyar shi shima,

Fahad Sun manta a ina suke har suka zo gidan sabeer yayi parking ya fita daga motar yayi jingina jikin motar,

Yanmatan amarya sukayo wurin motar domin shiga da amarya ciki,

Sabeer ya tsaida su yace "kujira sugama testing tukunna "

Sukai dariya zainab tai knocking motar, nocking dinta ya dawo dasu duniyar mu faseelat ta fara mayafinta tana dedeta kanta,

Fahad kau jikin seat yakoma ya jingina yanajin wani iri,

Akunya ce faseelat ta bude motar tafita,

Friends suka shiga ciki daita,

Sabeer ya koma cikin motar yajuya yana kallon fahad da yayi likimo yace "inafatan de bawani abu kasawa yarinyarnan a cikin drinks din dazu ba? "
Ganin yadda take bashi cooperation,

Cikin sanyin murya yace "angayama ni mugu ne kamar ka bansa mata komi ba amma ka tunamin zansa mata a drink da zan kaimata anjima,saboda I want to enjoy her all the night"

Sabeer yayi dariya yace "kar kai haka naga itama a hannu take maybe kasamu irinka "

Fahad yace "ka kuma kawo shawara, "

Sabeer yace "karka sassauta tunda yar hannu ce,muje na ajiye ka natafi wurin matata ta dumamani"

tuno fa she's sauran wani yasa yaja dogon tsaki,

Sabeer yace "what? "

Fahad yayi banza dashi sabeer yace "fitarmin a mota malam "

fahad yayi dariya yace "da Allah yi hakuri niba zanma iya driving ba yanzu, mukoma hotel din akwai bakina da zan sallama gobe zasu bi flight din safe daganan mu wuce na dan siyo musu abun ci kamedoni se kawuce gida "

Sabeer yace "Allah kaci saar yau ranar murna ce da ba inda zanje gida zanyi tafiya ta "

Fahad yace "sorry please mutafi "

Sabeer yaja motar suka tafi,

Friends na faseelat suka dan gyaramata dakinta yanata kamshi, suka kara mata nasiha da hakuri da tunatar daita dagewa da yin ibada, addua don samun kwanciyar hankali,

Karfe 11saura aka medasu gida bayan Sun mata bankwana,

Koda aka medasu gidan su yan balai duk suntafi gida,

Aisha kuma tana dakinta, bayan tafiyarsu gidan yayi tsit kamar ba mutane acikinsa,

Seda fahad yayi bankwana da bakinshi wadanda zasu koma gida sannan suka wuce yahuza suya,

Kaji biyu ya siyi leda daban daban, sannan suka biya wani supermarket suka siyi drinks dukda de akwaishi agidannasu,

suna zuwa kofar gida fahad yace "Nagode abokina Allah yabarmu tare hakika ka cancanci yabo don kayi iyakar yinka a bikinnan banda abinda zance maka sede ince Allah ya barka da radiyar ka "

Sabeer yayi murmushi yace "karkaji komi abokina kafi haka aguna, kuma bagashi ba nima nasamu irin taka "

Fahad yace "wacece?"

Sabeer yace "wata yarinya ce inajin sunada tight relation da faseelat don suna ma kama "

Fahad yace "I didn't see her saboda yau gani kawai kuke amma hankalina sam baya jikina "

sabeer yace "ai ni ne zanbada wannan labarin nima ai sauran kiris na zauce kamar ka, yanzu de seda safe agaida amarya "

Sukai musabaha fahad ya bude motar ya fita ya shige gida sabeer kuma ya tafi gidanshi.

Tunda yashiga gidan yaji shi shiru, saman benen ya haye direct dakin aisha ya nufa ya bude ya shiga da sallama bakinsa,

Aisha dake kwance looking pale ta tashi zaune tana kirkiro murmushi,

Yana murmushi ya zauna gefen bed ya kalli amira dake bacci yace "uwargida ya gajiya?"

Aisha tace "bawata gajiya, kune da gajiya ai "

Fahad yace "meyasa baki kai amira dakinta ba? "

Tace "yau so nike takwana anan ta debe min kewarka "

Fahad yamata kallon tausayi yace "I'm sorry my heartbeat ,kwana ukku ne kacal fa "

Ta bata fuska zatai kuka jin yace kacal,

Ya jawota jikinshi yace "it's okay, nima dolene tasaka amma zanyi missing naki "

Tai shiru ya jawo leda daya ya mika mata dayar kuma na gefen gado,

Aisha ta yamutsa fuska,

ya tashi tsaye yace "zanshiga wurin amarya "

Cikin bin shawarar antin ta tace "muje na raka ka nabawa amarya amanarka "

hannunshi cikin nata suka fito suka shiga dakin faseelat atare,

Wani kamshi me rikita kwakwalwa ne duk ya ziyarcesu.

Faseelat Na zaune jikin bed har lokacin,
Chapter 53 · 0% Book details