← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 130

Sashe 109

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy tai zaman dirshan kasa sadiya auta na kwance kan cinyarta Tanai mata tsifa Aisha ta shigo tafada jikin mommy tana kuka, sadiya tai wuffff ta tashi zaune,

mommy na raba ido tace "Aisha menene kuma kede matsala bata karewa daga gareki "

Aisha numfashinta na sarkewa take magana "mommy yaya yadena sona yadena kula da rayuwata, faseelat ciki ne daita yaya namin gori yana fadamin ina bakin ciki nake daita "tafashe da kuka tacigaba da kuka tace "mommy yaya yazo yace nabashi kwanaki har seta samu lpy ze dawo gareni gabadaya hankalinshi yana kan cikinta kuma lpyarta lau wlh "

Mommy ranta bace take kallon Aishar,tana dasa aya tace "ubanshi yaci uwatai ita me ciki harwani lokacin lpy ne daita, saboda tana da ciki seya ida kashemin ke, dan ubanki meyasa baki fadamin tuntuni ba seyanzu "?

Aisha tana ta kuka tace "baniso in tayarmiki da hankali ne mommy shiyasa nai shiru"

mommy tace "aiko shegen cikinnan baze zo duniya da rai ba share hawayenki kingama kukan bakin cikin shi daga yau wlh "

"Ke sadiya tashi daukomun waya ta daki",

Tatashi ta tafi sama dasauri, Aisha nata ajiyar zuciya hawaye na kara zubomata mommy tace "shi har yaisa ya miki gorin haihuwa shegen cikin ze bare kuma dole yarabu da shegiyar nan"

sadiya ta dawo da waya hannunta ,mommy ta latso number anty salma takara akunne tace "auta kishirya wurin katon boka nakeso kikaini kowani jibgegen malami wanda dana fadi bukata ta tagama biya "

anty salma tace "tofa anty lpy meyafaru? "

Rai bace tace "kome ma yafaru fahad so yake ya kashemin Aisha kawai wai dan kishiyarta nada ciki shine yake mata gori harda cewa tabarmishi kwanakinta wlh bazan bari ba wannan karan kishirya gamunan zuwa"

anty salma tatabe baki tace "ai dama zuba maku ido nayi tuntuni yakamata ace anwuce wurin base yanzu ba da Aisha tagama wahala, niko keda malaman da zan kaiku gunsu aiki kamar yankan wuka, akwai boka gumurzun duniya ya kware da aikinshi ga lasting, akwai malan halilu megani har hanji kina zuwa ze biya miki bukatunki cikin sauki "

Mommy tace "gamunan tafe nagaji wlh ni kaina abun yana affecting dina some time bana barci idan nakira likita yana fadamin jinina yahau sede munzo "takashe kiran,

Aisha najin abinda tace tai tsit ita gabadaya hankalinta ya gushe mijinta kawai takeso yadawo gareta ta kowane hali,

Sadiya datun dazun take zare ido tace "mommy bade wurin boka zakuba?"

Mommy na harararta tace "can muka nufa ko sadiya "

sadiya tace "mommy kinsan fa Wanda yaje wurin boka yayi shirka kamar hada Allah da wani ne, kuma fa bukatunku bazasu biya ba seya so, meze hana anty takara hakuri kuyita addua in ma wani asiri aka masa seya kare amma karkuje wurin boka plss mommy "

mommy tace"ke sefa munje sena kwato mata yancinta duk wa yaja inba itaba danubanta inata bata shawara taki dauka, tunda nake ko malamin zaure bantaba lekawa ba amma yau dole ne se munje wlh "

sadiya zatai magana mommy ta kai mata bugu, ta janye tana tunzuro baki,

mommy tace "sena ci ubanki da shiga maganar manya tashi kidaukomun gyalena ke Aisha da jikka ta ki duba a closet ki daukomun rapar 1k guda 3 tashi maza "

Aisha ta tashi tana share hawaye ta haye sama jim kadan tafito da kayan tabawa mommy tasaka suka fita,

Suna fita sadiya tafashe da kuka tace "Allah yaganar daku gaskiya"

Basu tsaya koina ba se gidan salma suna shiga ta sabo mayafi suka fito a motar ta suka nufi gidan boka gumurzun duniya suka lula kamar zasu tafi jibiya sannan sukabi hanyar datayi dankama suka cigaba da tafiya,

Sunayi suna labari mommy tace "inta haihu aini nabani bare inta haifi namiji shikenan ita zata cigaba da ruling gida in ita wannan banzar bata kara haifuwa ba shikenan natashi atutar babu nayi renon banza"

Anty salma tace "ki kwantar da hankalinki anty kome yazo karshe"

Sunata tafiya suka tsaya a bakin titi suka sauka sukabi wata yar karamar hanya tundaga kan titin kana hango rufin bukkar bokan, bawata tafiya sosai suka iso wurin yana bakin bukkar wurin ba rufi amma bakikirin yake kamar anyi rufin kwano gawani mugun wari dake tashi gawasu layu da kawunan dabbobi gefenshi, tunda suka tunkari wurin suka rikajin ihunshi da maganganun shi da bakaken aljanu wadanda yake musu hidima su kuma suna biya mishi bukatocinshi,

dukkansu ba wacce ta tsorata har gara mommy danshi kanshi bokan abun tsoro ne shirgegen kato ne baki wulik daga shi se dan bante ya rufe kugunshi,

Anty salma ta bude baki tana fadin "gafara de gafara de,"

Suka zo zasu zauna gabanshi nesa dashi,

Tunkan su zauna ya kwasa masu tsawa dukkansu seda suka tsorata muryarshi na amo yace "Allah ya gaza? Ya gaza ne "?

Dukkansu suka rika gyada kai suna fadin "eh yagaza"

ya kwashe da dariya yayi yan surutanshi da aljanu dawani kalar yare,

Duk suka samu wuri suka zauna,

boka ya kallesu daya bayan daya idanunshi kore kore yellow yellow yanata zaresu, ya nuna Aisha yadaka mata tsawa yace "me kkso a musu?"

Aisha ta girgiza ,jikinta na rawa tace "so nake a zubar da cikinta asa mishi tsanarta amma karya saketa yanzu harse ta kamu da ciwon zuciya"

boka ya babbake da dariya "hahahahahahahahaha bukatarki zata biya yarinya amma dan dukununu nason ganin tsiraicinki aljani betau yanason shan maniyinki,aljani mugu yanason ya sadu dake daganan kuma bukatarki tagama biya har'abada hahahaha "

mommy ta zaro ido waje jikinta yana rawa ta kalli salma ta banka mata harara,

Aisha zatai magana mommy tai karaf tace "muna zuwa boka zamuyi shawara"

Yayi ta dumumuwanshi kamar beji taba yanata juya hannuwa,

ta wurga musu harara duk suka mike suka bar wurin seda suka kai gaf titi, mommy ta kalli salma tace "amma wlh salma bakida hankali kirasa wurin wanda zaki kawomu se wannan bakin arnen wanda in ance rabonshi da wanka yafi shekara baa gardama ,ahakan ze kwanta da diyata wlh batayiwu wa dan nasan duk cutukan duniya babu wacce bazaa samu a jikinshi ba "

Salma tace "aa anty bawani ciwo kuma seme dan ya kwanta daita inde bukata zata biya Allah anty aikinshi na lasting wani lokaci mutu karaba"

Mommy tace "keni inason diyata ban shirya ganin gawarta ba bazan bada ita shida aljanunshi suyi wartambe da jikinta ba wancan katon idan yahaye ta na tabbata seta ji kamar bata taba sanin namiji a rayuwarta ba "

taja hannun Aisha tace "mutafi wurin dayan mugani"

Aisha ta riko gyalen mommy tace "mommy kibari plssss "

Mommy ta balla mata harara tace "inbari wancan laanannen Allan ya tumurmusheki? Lalle bakida hankali Aisha nida sauran hankali na"

Taja ta da tsiya suka shiga mota suka bi ta ring road sunata tafiya seda suka bullo cikin batagarawa suka kutsa kai can ciki can wata unguwa daba mutane sosai se daidaya suka faka bakin wani gidan bulo,

suka firfito salma nagaba tanajin haushin mommy ta bude labulen dake wani daki awajen gidan suka shiga,

wani dattijon mutum ne zaune da katon tray da kasa cike dashi ga casbaha yanaja zut zut kai kace ba abinda yake fada casbahar kadai yake ja,

suna shiga yadago yabisu da kallo da daidaya,

suka samu wuri suka russuna,

Sukai tsitttt, ya dukar dakai yayita jan carbi sannan ya dago ya kalli aisha yakura mata ido yace "mijinki yafi son amaryarki, yanzu tanada ciki yakara fifitata akanki?"

Aisha ta girgiza kai kamar kadangaruwa,

yasa yatsa yafara zane jikin kasar yace "ba'ita ce ta kashemiki diya ba dodon matsafa ya bukaci jininta suka bashi, bataiwa mijinki komi ba sonta kawai yake, me kkso a mata? "

tace "so nake yaji ya tsaneta sannan azubda cikin jikinta kuma data kamu da ciwon zuciya ya saketa"

ya cigaba da rubutu yana jijjiga kai,

mommy de shiru tayi wato Aisha seta dau fansa takeso ya saketa lalle Aisha ta azabtu sosai,

bayan lokaci ya dago yace "ze tsaneta bazeso ko hada ido daita ba, sede cikin jikinta baze zubdu ba saboda tana adduoi kuma cikin na yan baiwa ne dole se sunzo duniya sede akwai mafita idan cikin ya tsufa yakai watan haihuwa zakizo nabaki wani magani data fara nakuda ki mata turarenshi cikin kwana ukku yaran zasuyita ciwo su mutu su duka "

Aisha ta daga kai alamun ta yadda,

ya bude wata kwarya dake gefenshi ya dauko magani daya tallin tall kulle a leda ya mika mata jiki na bari ta amsa,

Yace "da kinkoma Gida kiyi turarensa akoina acikin gidan ki tabbatar ya shaki hayakin kafin awa biyu dayinsa daganan kuma aikinki zefara "

Mommy tace "mungode sosai tome zaa bada? "

Yace "zakubada 100k idan wata takwas sukayi zata dawo ta amshi cikon maganinta"

abun yawa mommy sauki da yawa, ta zuge zip na jaka ta fiddo 200k ta ajiye agabanshi tace "ga wadannan idan aiki yayi kyau yaran suka mutu zan kawo maka wasu 200k din "

malam yace "da kyau se kundawo"

Suka tashi suka fita sunata godiya,

Suna fita mommy ta kalli salma tace "keda kinsan wannan yafi sauki kika kaimu can? "

Salma tace "Ai kuma waccan aikinshi yafi lasting kuma dashine har cikin seya zube amma wannan ma semujira lokacin da yace "

Aisha na murmushi tace "nagode anty "

anty salma ta harareta tace "shasha seki meda hankali kiyi yadda yace, kuma kita abubuwan da shegiyar zuciyar ta zata buga karshen ciwo ma"

Aisha tai dariya suka hau mota sunata labari suka koma gidan anty salma daga nan suka dau motarsu suka wuce gidan mommy,

Lokacin marece yayi sosai acan gida faseelat suna zaune da hero a main falo tana jikinshi da shagwaba tace"hero ice cream vanilla essence plss "

yace "akwai fa acikin fridge bari na dauko miki"

Tace "nide bashi ba vanilla nakeso"

Ya dafa cikinta yace "baby kacika shan sanyi ka rage kar mura takama minkai"

faseelat tai dariya tace "yaji plsss yanzu nakeso sena sha nakejin dadi"

Yace "bari nafita na siyo miki bayanshi seme? "

Ta langwabe kai tace "mutafi tare mana kaga senaga wani abun danikeso din "

yace"bafa ki lpy honey kiyi zamanki"

tace "nide senaje "tai kamar zatayi kuka,

yace "no don't cry bari na daukomiki hijab "
Chapter 109 · 0% Book details