← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 130

Sashe 7

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sukai bankwana ummi Nata godiya sede bata fada mata yakawo wani abu ba Hjy saratu tace "hmmm yanzu haka wani abun ya kai musu, kowa na haramar tafiya masallaci shi yanata surukai," taja dogon numfashi "nasan abinda zanyi komi zezo karshe "

Shi ko khalil masallaci ya wuce daga gidansu faseelat, hankali kwance, gabadaya jiyake kamar bashi ba, soyayya ta fara sauya masa rayuwa.

Faseelat kau seda ta shiga daki ta kara jan tsaki "komiye na mishi dariya ma? Nan fa se yayi tunanin tafara sonshi ne "ta kara jan tsoki,

Ta jawo wayarta messages sungama shigowa abinda ta lura groups dinta Sun ragu dama inka dade baka online groups fita suke, bin groups din tafara yi taga wadanda suka fitar daita,

Taga kusan group bakwai ta fita, se tafara bin numbers dinta tayi wa friend dinta magana a medata wasu ,akwai wani group sirrin mu mata, shi ta fara shiga saboda tanajin dadin group din, messages din wasu Sun bude wasu basu bude ba, tatura sallama ,suka amsa tace "plss masu group suyi adding dina ko abada number ta asani nadade bani online ne "

Se akafara mata reply da welcome masu turo sticker na turowa, wata me suna maman amira tace akwai wani group amma se kinbiya 500 ake adding naki ana karuwa sosai ciki,

faseelat tace "anayin share and self? "

Maman amira ta turo mata "eh anayi, Ko kati ko BTU ko transfer "

Faseelat tace "kiban no din admin zantura mishi through share and self saboda banda kudi "

maman amira tace "ayya zan biyamiki asaki ki dan jira "

Faseelat tace "amma de Nagode aunty Allah yaraya amira "

maman amira ta turo mata smile face.

daganan faseelat tai taganin new groups na matan aure wasu na novels ana sakata,

Seta bi maman amira PC tana mata godiya maman amira tace karkidamu sister sunanki kawai ya burgeni ,faseelat tace zan'iya adding number dinki?

maman amira tace"yes zakiiya nima zanyi adding taki "

Faseelat ta tura mata thanks you" (the Fateful relationship just begun)

Ko minti 10 baaiba akayi adding nata ta tura" slm "

Maman amira taturo "you are highly welcome friend "

Faseelat tace "I'm grateful "

Fitowa tai a group din tafara bin status daya bayan daya sannan ta sauka online,

fitsari ne ya matseta ta tashi tafita waje dasauri,

Ummi tagani tafito daga kitchen hiyaki ya korota, tai sauri tashige toilet ta biya bukata ta dawo, ta tafi gun ummi "ummi for god sake miyasa kikeson wahalar da kanki nace naji sauki kibari nayi "

ummi tace "ai gwara narinka shiga ciki ko na saba tunda tafiya zaki kibarni ni daya "

Faseelat tace "eh naji amma bari nashiga inbani nan kyayi din "
Ta kutsa kai kitchen din duk da hiyakinsa inda sabo ta saba .

Hjy saratu kau alhaji ta dannawa kira, bayan ya amsa yace "lpy de ko kira gab Shiga salla "

Tace "eh dama so nike ince maka inason zamuyi magana inka dawo "

yace "To saurin mi akeyi da antaso masallaci zanshigo gidan "
Ko to batace ba ta yanke kiran,

Siyama ta fito daga kitchen tana kai abinci daki har ta gama sannan ta zauna tana "wash Allah na "

Hjy ta kure ta da ido tace "wannan dan aikin? To ko de ciki gareki "
Siyama tai murmushi batare da tace komi ba,

Hjy tai dariya "to Allah ya raba lpy "

Siyama tai tsit can tace "bari naje nai salla "

Hjy tace "har lokaci yayi ne "

Tace "eh karfe 1:40pm"

Hjy tace "bari mutashi muma "

Ana saukowa masallaci alhaji ya taho gida yana shiga da sallama bakinsa yaran siyama suka gudu suka tarboshi ya tallabo kawunansu sukayi ciki, yanata jindadi,

Dakinshi ya wuce kai tsaye ya rage kayan jikinshi ya dan kishingida sega siyama takawo masa abincinsa suka gaisa ya mata ya jiki ta fita tareda yaran.

Yana tsakiyar cin abinci Hjy tashigo ta zauna sannan tace "sannu da zuwa "

yace "yawwa yana Kai loma bakinsa "

yace "wai maganar mi cece da baajira na dawo "

Tace "dama bawata magana bace seta khalil da faseelat "

Ya ajiye cokalin hannunsa yace "inajinki"

Tace "nace mi zaihana akai kudin neman aurensu tunda de akwai su, bayan ansa rana se su cigaba da fahimtar juna kafin auren, nasan shima khalil din zeso hakan."

yadanyi nazari for some minutes sannan yace "yanzu de kifara yiwa mamanta maganar duk yadda kukai se inji saboda kamar abun yayi wuri "

Tace "haba bawani matsala amma bari na kirata "

ta kwalawa siyama kira tace mata ta miko mata wayarta, takawo mata ta juya.

hjy tayi dialing number ummi

Tadanyi ringing sannan ummi ta dauka da sallama,

Hjy tace "kinga na sake kira ko,dama maganar yarannan ce to munyi magana da alhaji kiyi magana da abbansu in anbada izini zaaturo "

Ummi tace "to ba matsala nasan yanakan hanyar dawowa Inya dawo zamuyi maganar duk yadda mukayi zakiji "

Hjy tace "to Nagode kwarai se na jiki "
Ta yanke kiran

Alhaji bece komi ba ya cigaba da cin abincinsa.

Khalil siyama nafita ya shigo tafara zaulayar shi, yana dariya yace "siyama bakiji ni kuma ake zolaya? Ni yayan. "

Tace "hmm yaya kenan ,yanzu de kabar number anty ta mufara gaisawa "

yace "zanbaki amma ba yanzu ba, kije ki daukomun abinci na tukun inna gama se muyi maganar "

Ta kawo masa abincin yafara ci dan mutuminnaku be wasa da k'oto.

Seda ummi tabari abba yagama cika cikinsa da daddadan abincin da faseelat ta dafa sannan tafada mishi yadda akai yace "kunde nace ga hadin nan auren hadi matsala ne dashi in aka samu sabani, "

Ummi tace "insha Allah bawata matsala"

Yace "to yanzu de su bamu lokaci kamar nanda sati daya, dan inaso nayi bincike, bama wannan ba ita faseelat din ta amince ne? "

Ummi tace "eh mana ko akirata ka tambayeta? "

Yace "eh kiramin ita "

Ummi tatashi ta fita kiranta daga can bata dawo dakinba,

Faseelat ta zauna "gani abba"

ya kalleta sannan yace "kinji iyayen khalil zasu aiko me kikace? "

Faseelat gabanta ba karamin faduwa yayi ba tai shiru ta sadda kai kasa,

Abba yace "kin amince? Yanzu kina sonshin? "

Kuka ne yazowa faseelat tai saurin rufe fuskarta da hijabin jikinta,

Abba yayi tunanin ko kunya ce yace "to tashi kije? "

Ta tashi da gudu tashiga dakinta ta fara kuka me cin rai.
[7/12, 10:58 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

*dedicated to rano sister*

1⃣1⃣

Kukan nata bame sauti bane ,zeyi wuya kaji shi inba dakin kake ba,

Tadau tsayin minti 15 tanayi, se tafara magana da zuciyar ta,

"ba kince bazaki kara kuka ba to me kikeyi yanzu"

Dayar zuciyar tace "i have to ko don na rage zafin da ke tsatstsafowa a raina"

Dayar zuciyar ta tace " you're only wasting your tear, ba abinda zaafasa, so you better stop it"

"you are right fa "ta sa hannu ta share hawayen nata.

Tambayar zuciyarta take "to me yakamata nayi? "

Dayar tace "don't ever take decision in haste, kibari ayi auren mana "

Shiru tayi tana tunani

Can zuwa ta Saki murmushi ita kadai tasan abinda ta kulla, se ta mike zaune, ta jawo wayarta ta fara chart.

Bangaren khalil ko seda cikin shi ya cika tabbb sannan yasha ruwa sukafara labari da kanwar shi, har yabata number faseelat din kamar yadda ta bukata, shiru shiru Hjyrsu bata fito ba seya fita zuwa wurin best friend nashi wanda suke tun suna yara amma saboda irin yanayin khalil basa sharing problems nasu ma juna, ana taren ne kawai.

Ummi na komawa abba yace "ba matsala tunda ta yarda ki kira ita hjyar ki fadamata yadda mukayi "

Ummi tace "to "
Ta kira hjy tafada mata duk da de hjy ba haka tasoba amma se tace "ai bakomi sati ai kamar gobe ne "

Alhaji najin yadda Sukai yace "to Allah yakaimu satin zanyiwa su yakubu magana dan su shirya da sunbamu rana se suje "

hjy saratu tai murmushin jindadi.

Faseelat na tsaka da charting kiran siyama ya shigo ta dauka tai sallama, daga can bangaren aka amsa,

Akace "antinmu inawuni "

Faseelat tace Anti kuma? Ai batada kanwa mace sannan bama haka ake kiran taba ta daure tace "wa ke magana? "

Siyama tace "kanwar mijinki ce siyama"

sora kirisss faseelat tai ta bargaza dan harta hade baki da niyyar yin tsoki tai saurin fasawa, tace "ina yini "

Siyama tace "lpy lau anty dama cema yaya nayi yaban number ki mugaisa "

Faseelat tace "ihhhhn Nagode "

Siyama tace "bakomi se anjima agaida su ummi "

Faseelat tace "ihhhhm "takatse kiran ta turo baki gaba tare da cewa "Se kuyi tayi ai nide nawa ido"

Kiran wata number yashigo wayarta da alamu number Niger ce saboda digit din farkon number din, tadesan baze wuce danginsu ba ko ya umar, yaushe rabon ma suyi waya ankwana biyu

Ta daga kiran ta kara wayar a kunne "assalamu alaikum"
Ta fada ,murmushi ya doki kunnenta akace "waalaikumussalam"

Tunda taji murmushin ta gane me magana, yanayin yanda ya amsa mata sallama da zolaya ya sata tafara dariya,

Tana dariya tace "yaya na, kaine kamanta dani kwana biyu ko? "

shima yayi dariyan yace "ina ni ina mantawa dake duk in mukayi waya da ummi ina cewa ta gaidaki bata fadamiki ne? "

"Allah ni bata fadamin"ta zumburo baki kamar yana ganinta.

Yace "to laifin ummi ne ba nawa ba tunda kinsan bakida waya yanzu ma hakanan nace bari nakira layinki se gashi tafara ringing, kice baba babba har ya siyi wata, dan nasan ummi de bazata se miki waya ba tunda kudinta kaff suna karewa ne wurin se miki cosmetics, kuma nasan abba baze siyamiki waya ba ya fiso ki karatu besan shiririta "

Tace "a, a ba shi yasiyamin ba fa "

Daga can yace "to waye? "
Chapter 7 · 0% Book details