← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 130

Sashe 44

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin tayi tsaye tana kallonta faseelat ta kutsa kai ciki tana tunanin kila su dedeta, ta zukunna gaban aisha kanta Kasa tace "anty nasan ni me laifi ce agunki dan Allah kiyi hakuri bansan taina zan fara fadamiki bane tuntuni cewar muna soyayya da mijinki....."

Bata bari takara saba cikin tsawa tace "keeee dan uwarki harkin isa kifadamin kina soyayya da mijina, karuwar banza kawai wato tunda kikaganshi kika like masa ko? To ki san dasanin nidake har abada wlh nayi danasanin saninki a cikin rayuwata "

Faseelat tafara hawaye tace "anty kitsaya ki saurareni plsss "

Aisha tace "kimaza kibarmin gida wlh kafin inci ubanki "

Faseelat ta dago zatai magana aisha ta rufeta da bugu ta koina, jikake fas! tab!duf!duf ,

Jin Azaba faseelat tafara ihu, cikin barci yaji ihu, ya farka zaune yakasa kunne inyaji da kyau muryar faseelat ce ,yace "oh my God "ya fita dasauri,

Tunkan bene ya leko yaga yadda aisha tahaye faseelat tana jibga ya kwatsa tsawa "keeeee aisha"

Koji batayi tana ta jibgar faseelat cikin sauri ya sauko daga kan benen ya janye aisha ya dauketa da mari a duka kumatunta, jikake tasss! Tassss,

Aisha ta dafe duka kumatun da hannu biyu tana kallonshi dan saura kirisss ta kife awurin,

Cikin sauri ya tada faseelat tana ta kuka ya rungumota jikinshi yana.........

*inajin dadin comments naku jiya anyi ruwan comments godiya lodi lodi, nima inasonku masoyana*💋💋

Wani sabon salo har team aisha ke da kwai yanzu 😂🤔

Team fahad 💋
Team faseelat 😘
team khalil bodari😂
Team Aisha 😍

Yayin team team ake saura team hajiya da team jamila 😂

luv u always my fans dake koina 🤗
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*

✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽

We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

4⃣9⃣

*dedicated to those lovable group's*👇🏾

*RAGGON MIJI FANS*
*RAGGON MIJI FANS 2*
*RAGGON MIJI FANS 3*
*UMMYN YUSRAH NOVELS GROUP*
*MUKARU DA JUNA BY MOMYN SAUBAN*
*NOVELS ZAFAFA BY DR FATEE*
*MY FORUM GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*
*MOMMY'S NOVELS GROUP BY SHALELE*

*THIS PAGE IS ALL YOURS FRIEND'S ACIGABA DA COMMENTS KAWAI*⛹🏻‍♀

*MANZON ALLAH (S. A. W) YACE :-lalle Allah ya rubuta kishi akan mata, da jihadi akan maza wadda tai hakuri acikinsu tana da lada kwatankwacin wanda yayi shahada.*

Yanajin wani irin ciwo a zuciyarshi, jintana ta kuka ya dagota yafara duba jikinta duk yayi ja abunka da farar fata ga gashinta duk Aisha ta yamutse shi cikin jin tausayi yakara rungumeta yana shafa bayanta,

Kwata kwata kuka yaki zuwa ma aisha tazuba mishi ido tana ta kallonshi ganin yadda ya kwakume faseelat kamar ze medata ciki yasa ta sauke hannuwa daga kumatunta tai hanyar kitchen da gudu ko seconds goma baaiba ta fito da sharbebiyar wuka ahannu tai kukan kura zata sokawa faseelat a baya, fahad yayi sauri ya rike kaifin,

Aisha tafara jujjuya wukar tanaso ta kwace ta sokawa faseelat shi kuma ya rike kuma still yana rungume da faseelat daketa kuka,

Dandanan jini yafara diga Kasa kan farar hijab din faseelat, ganin jininshi yana zuba amma yaki sakin wukar Aisha ta saki wukar ta dora hannuwa biyu akunne ta kwara baki ta saki kuka tai saman bene da gudun tsiya,

Fahad ya Saki wukar tafadi kasa ya bude tafin hannunshi yana kallon yankan da ke jiki,

Faseelat ta zare jikinta tana kallonshi cikin tausayi ta duka ta dauki kallabinta dinta ta kama hannun fahad tana nannada mishi tana kuka, shi ko kallon fuskarta kawai yake yana ganin wautar ta na zuwa gidan a yanzu,

Suna haka aisha tafito tana kuka sabe da amira awuya tafita tabar gidan, duk sukabita da ido,

Seda tafita faseelat ta medo kallonta gareshi tana sheshsheka tace "I'm sorry bansan haka anty take ba nazata zata saurareni ne dana sani banzo ba "

Ya riko fuskarta da hannu biyu yana kallon cikin idanunta yace "aisha zata iyayin fin haka, karki sake irin gangancinnan cutie yanzu da bani nanfa? Wlh aisha har kashe ki tana iyayi saboda gabadaya ta haukace,"

Ya riko jikinta "jibo yadda taimiki da jiki"

Faseelat takara zubo da hawaye dan ta jibgu ba karya ,

Ta riko hannunshi tana fadin "it's hurting ko? "ta kalleshi cikin jin tausayi,

Ya rungumota jikinshi yana kwantar mata da gashin kanta yace "it's not idan nahadashi da zafin dukanki da Aisha tayi "

ta kwantar da kai kan kafadarshi tana hawaye,
Yana ta shafa gashin kanta tai breaking hug din tace "zan tafi gida "

Ya jawo hijab dinta da take dauke da drops na jininshi yasaka mata, sannan ya kalli jikinshi daga shi se boxer ya dago ido yace "bari na dauko key na kaiki "

Ya juya ya haye bene few minutes ya dawo cikin jallabiya da keys a hannu ya kamo hannunta suka fito daga cikin gidan ya bude mata motor ta shiga ya zagaya yaja sukabar gidan ,shide baba tsoho yanata kallon ikon Allah yadda yaketa ganin Aisha na ficewa da kuka yasan akwai matsala,

Suna kan hanya yana tuki da hannu daya hannunshi daya kan cinyar faseelat, tunda suka fito take ta kara zubda hawaye,

Ya kalleta ya meda kai kan titi yace "kiyi hakuri cutie ki dena kuka ,Aisha bata isa ta hanani aurenki ba inasonki sosai fiyeda yadda zaki harsaso, ki kwantar da hankalinki aisha zata sauko insha Allah "

Faseelat zuciyarta zafi kawai take yadda Aisha ta wulakantata ga zafin yankan da taiwa fahad da takeji kamar ita akaiwa,
Ta Kalli hannunshi dake kan cinyarta
Tasa hannu ta rufe fuska jin kukan da ya taho mata tafarayi tana jan numfashi,

Fahad ya dauke hannun daga kanta ya shafi kanshi zuwa sajenshi ya fitar da iska me zafi daga cikin bakinshi gabadaya Sun caza mishi kai yace "cutie ya kikeso nayi ne? Yanzu kina ganin zan bari kitafi gida kina kukannan? Kiyi hakuri plsss"

Ta daga kai ta jawo hijab dinta tafara share hawayen dake zubomata tana sharewa wasu na zubowa,

Ya girgixa kai ,har suka kawo kofar gidansu, Ta bude zata fita yace "kode nakaiki asibity ne ko akwai inda ke miki ciwo? "

ta girgiza kai cikin muryar kuka tace "thank you "ta bude tafita ta shiga gida dasauri,

Yakara murmuxa gashin kanshi kanshi na zafi sannan ya tada motar ya nufi gidan mommy,

Faseelat dasauri ta shiga gida ummi da tundazun ta duba bataga faseelat ba ta ga wulgin faseelat dasauri tafito daga dakin abban tabi bayan faseelat da kallo kayan jikinta a cumumuye ga jini saman kan hijab din zuwa kasan hijab din,

Hankalinta ya tashi tabi bayan faseelat, lokacin faseelat ta yaye hijab din tahaye can karshen gado ta hade kai da gwiwa tana kuka,

Ummi ta shigo dakin tana kallon gashin kanta cumimiye tace "kee daga ina kike "

Faseelat ta dago tana raba ido tafara nazarin me zatacewa ummi,

ummi tace "dan ubanki ba magana nake miki ba? "

Faseelat ta fara yarfa hannuwa tana kuka,

cikin zafin rai ummi ta haye kan gadon ta shakarota cikin tsawa take cewa "bazaki fadamin ba ne dan ubanki daga ina kike? "

Abba yafito daga daki jin kakari da fadan ummi yayi sauri ya shiga dakin ummi ganin ta shakare faseelat yayi sauri ya je ya janye faseelat din yana kallon ummi yace "haba asiya kibari mana aibata haka zaki tambaye ta ina tajeba "

Ummi tace "alhaji yarinyarnan harta san takwasa taje wurin saurayi? Yaga ma tumurmusarta ta dawo tana kuka, jibi hijab dinta "ummi tajawo hijab din tana nunamasa tace "duk jinine jiki wlh faseelat ta iskance tunda har taiya bashi kanta kafin aure "

Faseelat ta dago tana zare ido jin abinda ummi ke cewa,

abba cikin mutuwar jiki yakebin faseelat da kallo duk ta harmutse,

ummi tace "nikam nagaji alhaji dan Allah kasamu yaronnan kace ya turo tunkan ta jawo mana abun kunya"

Abba bece komi ba yabar dakin ummi tazo zata kawowa faseelat bugu faseelat ta kauce tana zare ido tace "wlh ummi banyi komi ba, naje bawa anti hakuri ne, shine ta yankeshi a hannu amma wlh baai komi ba "

Ummi cikin rashin yarda tace "gafara can da Allah ni zakiwa karya, ko ni makauniya ce? ke kikasani dan wlh ko aurenki yayi bazaki wata daraja ba sakarai kawai yo miki so hauka ne da zaki je kibashi kanki, kin kyautawa kanki ai "

Fuuu tabar dakin faseelat ta fashe da kuka ta jawo pillow ta danne kanta dashi ta cigaba dayi,

ummi nafita bataga abba ba har yabar gidan takoma dakinta ta buga tagumi zuciyarta na zafi, tundazu maganar da sukeyi da abba akan faseelat ne don yaji abinda yafaru jiya Sunata neman mafita sega sabuwa ta billo,

Aisha nashiga cikin gida takara sakin kuwwa da mommy dasu ramlat sukayo waje, sadiya tai sauri ta amshi amira daga hannunta,

Aisha ta rungume mommy tana kuka,

Mommy tace "wato Aisha bazaki bi shawarata ba ko? Yanzu mi yakawoki da safennan?"

Aisha na kuka tace "faseelat dince wai tazo bani hakuri shine nahauta da duka ina cikin dukanta shine yazo ya mareni shine na dauko wuka zan soka mata shine yarike da hannunshi duk yaji ciwo ahannun "

Hjy tace "wato de bakijin magana ta kenan ko? yanzu da kin kasheta fa? Kema ba barinki zaaiba, nace kiyi hakuri kibar lura da abubuwansu kinki, inaji miki tsoron ya sake ki dan masu irin wannan haukan da saki suke karewa, kinga shikenan se ita wasila take kowa tasami yadda take so"

Aisha tace "wlh bataisa ta rabani dashi ba "ta cigaba da kuka,

Ramlat dake gefe tace "kinyi dede anty gwara da kika ci ubanta da kyau "

Mommy ta banka mata harara tace "tashi kiban wuri "

Ramlat tatashi tabar wurin dama sadiya bata zauna wurinba tunda ta amshi amira ta wuce daita ciki ta kimtsata,
Chapter 44 · 0% Book details