← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 130

Sashe 3

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

yajuya yafita daga zauren takara bin bayanshi da kallo kuttt se yanzu ta lura rigarshi ta wuce gwiwa tsabar tsawo

Ta kai minty 5 zaune sannn ta tashi tai cikin gida,

Shiko Karon farko da yafara fira da mace dadi kawai yakeji yanda ya sameta ya tada babur dinshi yayi gida.

Faseelat nashiga cikin gida da sallama ummi ta amsa, zuwa tai zata wuce ummi tashiga daki ta kwanta ko ta samu ta dawo dede,

ummi tana kallonta tace "zo nan faseelat"

Tana daga kafa daya kan daya kamar wadda kafar taiwa dayi tazo gun ummi ta zauna,

Ummi tace "ya kukayi"

Faseelat ta sosa kai tare da cewa "naam"

ummi ta harareta tace "eh "

Sosa kai faseelat ta fara labbanta na kyarma tace "ummi beyi kama da mijin da nikeson aure ba "

ummi tarika jifanta da mugun kallo can tace "dan ubanki har wani kalar mijin da kikeso kika tsara? wallahi faseelat ki shiga hankalinki tom,"

Faseelat ta zumburo baki gaba "wlh ummi bani sanshi baki ganshiba beda kyau ko kadan "

ummi ta rike haba "faseelat? Dan kina ganinki fara shine zaki ce haka, ke kekikayi kanki haka hala? To kamar yadda kike haka fara shima haka Allah yayishi baki kuma haka yakeson ganinshi "

faseelat ta matso hawaye "Allah ummi ni banisonshi "

ummi tace "rufemin baki kar in mazgeki, dan kinsamu ze temakamiki ma wa yataba cewa yanasonki? Dankawai ze rufa miki asiri? To barikiji wlh inkinga baayi aurennan ba to abbanku ya binciko wani mummunan hali atare dashi ne ko in Allah ya kaddara
Ke ba matarshi bace amma ina tabbatarmiki se anyi bikinnan "

Faseelat ta dora hannu akai "nashiga ukkuna ummi dan Allah ki temakamin "

Ummi tace "temakon da zanmiki knan in aurar dake "

Faseelat tafasa kara tana kuka sosai ummi ko tatashi tabata wuri tace "ai seki tayi "

"wayyo Allah na ni wlh bansonshi "
Hardasu majina saboda kuka sallamar abbansu ne yasa ta gudu wurinshi ta rungume "abba dan Allah banisonshi karku auraminshi "

cikin mamaki yace "share hawayenki diyata "

Tasa hannu ta goge still wasu na biyowa yace "bawanda ze miki auren dole kinaji ki wuce kije ki kwanta "

Faseelat ta wuce sundum sundum ummi tafito daga kitchen "amma de alhaji kasan bazanji kunya nai magana biyu ba nariga na amsa musu yanzu mi kakeso nacema uwarsa ince bata sonshi? "

Abba cikin sanyin murya yace "haba asiya kibi komi sannu mana, wai ma duka Nawa faseelat din take ne? Duka fa yanzu shaekararta biyu da graduate, kibari komi asannu akebinshi ai yau suka fara haduwa may be su dedeta zuwa gaba"

Faseelat dake labe tace "wlh aa banisonshi bazan so sa ba harabada "sede bawanda yajita dayake ta Shiga daki

Ummi tace "hmmmm"

Tashige kitchen

Shiko abba ya shige daki yana girgiza kai, yarasa daliin ummi da ta kagara ta aurar da faseelat.

faseelat kan gado ta mike tanata sharar kwalla har bacci ya kwasheta.

shi ko malan mudi da farin ciki ya isa gida,

Bayan ya shigar da babur dinshi yawuce dasauri dakin Hjyarsu Hjyar na tsefe gashinta da rabi yafara zama furfura ya shiga, Hjy saratu ta dago tana kallon fuskar shi tagane yana cikin farin ciki,

Ya zauna tare da cewa "Hjy kiniya zabe wlh tayi komi yayi dede, gata da kyau ga iya wanka "
Hjyar tai dariya" marar kunya kawai, aibaka isa aure ba "

Yayi shiru yana dariya "toya ita faseelat yanayinta ta amince? "

yace "eh Hjy "

"to yaushe Zaka koma? Kukara ganawa, kafin atura su kawu "

yace "gobennan Hjy "

Hjy tace "hmmmm Allah ya kaimu, sede dan Allah ka natsu kuma ka rika yimata kyautuka saboda takara sonka sannan kuma ka san maganar da zakurika yi "

Yace "to "

Yakagara gobe tayi

*nace da akwai matsala kufa? 🤣*
[7/12, 10:58 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

Writing by *MAMAN MAMY*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

5⃣

*Dedicated to SIS ZULAIHAT RANO*

Ya kagara gobe tayi ko yakara ganin kyakkyawar fuskarta.

Wasa -wasa har dare faseelat taki tafito waje, ummi de ta share ta su abulkhair suna ta tambayarta sede ummi tace bacci take ,

Har abba ya dawo gida bayan ishai ummi da abba suna daki suna fira while ishak abul da Mubarak na tasu firar, dan auta ya kasa hakura da rashin ganin ta ya leka dakinta tayi rubda ciki amma ba bacci take ba, abin duniya ne kawai ya sha mata kai, ganin idonta rufe yasa yaja mata kofar,

Dakin abba ya shiga ya samu ummi ya zauna gefenta "ummi kode ya faseelat bata lpy? Naga tundazu da rana bata fito ba yanzu naje dakinta na ganta kwance har yanzu "

Ummi tace "to bana ce maka bacci take ba? Ka tashi kaba mutane wuri "

Yace "to ummi kode a tado ta ni wlh gidan ba dadi da babu ita "

Ummi tace "kai kasani ai "

Abba yace "wai tun dazu bata fito ba? Kuma kika kyaleta haba Hjy kinsan fa ulcer na iya kamata "

"to ya kake so na mata? Ko so Kake naje na rarraso ta tunda na mata laifi "

Abba yace "yaro dan rarrashi ne in kika lallabata se ki shawo kanta amma bata haka ba, kinsan faseelat na da saukin kai ai "

"Alhaji kabarta kawai in yunwa ta kusa kasheta zata fito, nifa duk abinda nakeyi saboda ita ne yarinyar nanfa da kake gani kusan kullum se tayi mafarki, taya kake tunanin hankalina ze kwanta tana zaune gidannan gwara ai mata auren tun kan ai abun kunya "

Abba yayi shiru yana nazari,yace"eh ki de bita a sannu, wa ma ta gado inbake ba da jarabar tsiya in baayi miki 3 rounds ba baki koshi "ya ida yana dariya

Tace "eh naji din ai kai ma shine da har kake iya yin ukkun "

Suka sa dariya Mubarak fa yadade da barin wurin tunda aka korashi.

Ummi nata zuba ido faseelat zata fito cin abinci amma bata fito ba, se kuma tafara shiga damuwa.

Itako faseelat muguwar yunwa takeji ga, zazzabi da ya rufeta kwance kawai take tanata tunanin yadda zatayi rayuwa da khalil.

Can 12am samarin duk sunyi bacci ummi tafito daga dakin abba har zata wuce se kuma ta shiga dakin faseelat,

Tana kwance rubda ciki still ummi ta matsa "ke bana hanaki kwanciya haka ba?"

faseelat ta birkita ba tare da ta dago ba

Ummi tace "wai dani faseelat zaki fushi ?dan kawai ina fadamiki gaskiya? Ya kikeso nayi ne? So kike nabarki na zuba miki ido? Bayan ga hanya Allah ya kawo, haba faseelat wlh kinbani mamaki da har zaki bijirewa magana ta shi dake namiji ya amince da umarnin mahaifiyarsa, amma ke kinkasa ".

faseelat ta fashe da kuka tana sheshsheka ummi tace "aa kidena kuka faseelat bazan takura miki ba tunda bazaki iya aurenshiba shikenan gobennan zankira uwarshi in fadamata bakisonshi tunda burinki ki kunyatar dani, ni wlh daace kinada wanda kikeso da baabinda zesa na matsa miki amma keda bakida kowa ihhhhm? Dama ace ke lafiyayya ce amma kinada larura ki duba fa yanayinki faseelat, shikenan anfasa auren ki tashi kije kici abinci "

Ummi ta juya zata fita faseelat na kuka ta kira sunanta "ummi "!

Ummi ta waiwayo ta cigaba da cewa "Dan Allah ki hakuri baniso ranki ya baci karki fushi dani "

"bazanyi fushi da keba faseelat sede ki sani zaki sani cikin zullumi da tunani dan wlh inde ban aurar dake ba banida kwanciyar hankali "

Faseelat daga kwancen de take magana cikin rashin tunani tace "na yadda ummi zan aure shi inde zakiji dadi "

Ummi tace "dako kinfaranta min rai dan inada tabbacin bazaki kuka ba in Allah yaso"

faseelat tace "na amince ummi kuma kiyi hakuri da bata miki rai da nayi "

ummi tace "bakomi Allah ya miki albarka ki tashi kici abinci karkijawa kanki ciwo"

Faseelat tace "bazan iyaba ummi masassara nake tun dazu "

ummi tace "subhanallahi "tana hawa kan gadon ta fara tattabata gabadaya jikinta rau yake har kafafunta, ummi tace "sannu kinji bari na kawo miki magani "
Ta tashi ta fita wani kuka ne yazowa faseelat ita kanta tasan ta amsa ne kawai amma tasan haka zatai ta rayuwar hakuri harabada, tasa hannu ta share hawayenta yanzu de koba komi ta farantawa mahaifiyarta rai da tun tasowarta tana ganin yadda take fifita ta akan yanuwanta.

Motsin da taji yasa ta kara goge fuskarta ummi tashigo dauke da tray ta ajiye ta bude flask ta debo taliyar hausar da ta dafa da daddare ta dora kan bed ta debi ruwa ta ajiye sannan ta zauna bakin gadon tace "tashi ga abincin diyata "

Faseelat na ciza baki ta yunkura ummi taida tadata zaunen jikinta har kyarma yake saboda yunwa,

Ummi tafara bata abincin a baki da yake tana jin yunwa taci abincin sosai sannan ta bata magani ta koma ta kwanta se sannu ummi ke mata sede ta daga kai, tashi ummi tayi taja mata kofa tana mata seda safe.

ko bayan fitar ummi faseelat kuka ta rikayi ga bacci ya kaura cewa idanunta,
Ba abinda take tunani se fuskarshi da jikinshi tana tunanin yadda zasuyi rayuwa tare wuri daya gida daya daki daya gado daya.

Se asuba bacci ya dauketa, ummi na Gama azkhar taje ta gaida abba yake tambayarta jikin faseelat da yake wurinshi ta amso maganin tace dasauki ta fita dubota, tana shiga ta tada ta faseelat bude ido kawai tayi ummi tace "ya jikin "tana tabata faseelat tace "dasauki "

Ummi tace "naji haryanzu da fever din kitashi ki salla inje in hado miki tea kisha kisha magani "

Faseelat tace "I'm off"

Ummi tace "kinada pads ne? "

Faseelat tace "eh amma beda yawa "

"OK anjima zanba Mubarak yasiyo miki wata tashi kije ki kimtsa ko kinji dadin jikin "

faseelat tace "to "ta mike ummi taga har tangadi take ummi tace "zakiiya wankan kuwa "
Chapter 3 · 0% Book details