← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 130

Sashe 6

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

"bakasan laifin da kayi ba kenan? Jiya ban hana ka zuwa gidannan ba da daddare amma seda kaje, tunda kaje kaga yarinyar nan shikenan ba saura ba kingi duk ka zauce, aka gaya maka haka akeyi ? ko dama can kana santa bansaniba?"

Maganganun hjy sun matukar bashi mamaki yace "haba Hjy kefa kikayi wannan hadin ni ina zan santa ma bare na so ta, kuma ni wlh hjy banga wani abinda nikeyi ba dede ba, jiya kuma Banyi tunanin tafiya ta zata bata miki rai ba, kiyi hakuri "

Tace "to naji why kake ta kashe kudi har haka danna ce kai mata kyauta aiba cewa nai kaita kashe kudi ba .

Shiru yayi kanshi duke tambayar kanshi yake mi yasamu Hjyarsu.

can zuwa yace " bawani kudi bane fa sosai waya kawai na siyo mata se cosmetics that's all "

Ta Harare shi "eh ba kudi bane masu yawa tashi kaban wuri, ai gwara ayi ai auren ko kasamu kanka, ni wlh dama kauye naje nasamo maka yar yarinya"

ya tashi tsaye ya shafi sumar kanshi can zuwa yace "Allah yabaki hakuri "ya fita

Tace "amin"

Khalil kusan Karo sukayi da alhaji yayi saurin zukunnawa gaida shi alhaji ya amsa ya wuce ciki.
Khalil ya tashi ya tafi saboda shirin makaranta .

Alhaji yana shiga yafara wa hjy fada "wato de sararu bazaki bar halinki na banza ba ko? saboda nasan halinki fa shiyasa ban kara aure ba danna san duk wacce na aura kashe ta kadai ke bakiyi, yanzu kuma ga matar danki zaki koma, to kibi Ahankali wlh tun kafin yaronnan ya fahimci manufarki "

komi batace ba ta tabe baki a ranta tace "aini ma bansan haka yake ba nazata ze cigaba da halinsa na rashin son auren.

7:30 khalil ya fito da shirin shi yau kam yayi kyau wani yadi ne ash color yasa mishi bakar hula da bakin takalmi rigarde tazarce ce da alamu duk haka dinkunansa suke hular ma tayi gaban goshi sosai shima da alama haka yake saka hular shi, ya leka kitchen hjy se diminiya take dan kawai karyayi kalacin danwake ne zatayi amma tai nan tai nan batare da ya damu da rashin hada kalacin ba yace "Hjy natafi "

Tace "Allah ya bada saa "fuskarta ba yabo ba fallasa.

Ko damuwa beba ya bar gidan se sannan hjy tagama danwaken,

karfe 9 siyama ta shigo gidan tareda yaranta biyu "Fatima da farida "

hjy saratu tace "oyoyo oyoyo yan albarka "

siyama tana fara'a tace "hjy ina kwananku "

"lpy lau ya jikin kwana biyu da kikai ba lpy kamar kin kwana goma wajen sunan ramla se tambayarki suke "

Tace "eh wlh hjy amma jiya na aika mata da sako kuma Bayan kwana biyu zanje gidan na gano takwara, ai wlh naji jiki hjy danbana iya komi, abdulkadir ke komi har girki "

hjy tace "Allah yasa kaffara ne,"

siyama tace "amin su yaya ana makaranta "

hjy tace "uhm antafi ai yayanki ya kusa zama ango "

siyama na murna tace "dan Allah Hjy wacece yarinyar "

Hjy saratu tace "eh ba wata bace se faseelat "

Siyama tana murna tace "faseelat de wadda nasani Hjy? "

"itafa "

siyama tace "gaskiya naji dadi hjy Allah yasa alheri ai faseelat full option ce komi yaji, tana dariya tace "finally yaya zaayi aure "

Hjy tai dariya siyama ta mike tsaye "Hjy mi zaa dafa muku yau ?"

Hjy tace "komi kikayi yau de jumaa komiye de da miya zaki "

"ayi taliya da miya NE? "

Hjy tace "a, a kide yi shinkafa kinsan khalil beson taliya gwarama in anyita da safe shima se anci saa kawai kiyi shinkafar se ki dafa masa wake, dan kinsan shinkafar ma baya sonta ita kadai "

Tace "to "tai hanyar kitchen.

Khalil ko school ya wuce ,jss classes yake koyarwa duk jiki mace yake komi maganganun hjy nata mashi yawo yanata kara nazarin su,, ga rashin lpyar faseelat data dameshi.

12:30 aka tashi saboda sallan jumaa direct supervision store yawuce ya siyi su peak milk , bournvita,cornflakes,block sugar, golden moon da tea bag, da different sweet , kusa da wurin akwai oasis bakery ya saye big bottle ice cream da snacks ya nufi gidansu faseelat .

yana isa yayi dede da dawowar Mubarak daga school , Mubarak se kallonshi yake, khalil ya jawo shi "abokina zo mugaisa "

Mubarak de yayi tsaye yana kallonshi khalil hannunshi ya kamo yasaka a nashi yace "ummi na gida?"

Mubarak ya daga kai

Yace "yayar ku fa ya jikinta "

Mubarak yace "dasauki dan dazun naganta tafito zatai shara ummi ta hanata "

Yace "good kaje kafadawa ummi cewa khalil yazo yana so ze shigo ya gaidata "

Mubarak yace "to"
ya shige gida seda yafara shiga dakinsu ya ajiye jikkarsa sannan yaje ya fadawa ummi, ummi tarike baki "Allah sarki yaron kirki ,jeka ce ya shigo "har ya tafi tace "Mubarak dawo jirani "

tashige dakin faseelat, faseelat taji sauki sosai dan wayar da yabata tasaka wa tsohon sim dinta, tai checking balance babu kudi ciki tanayin Wanda ya kawo taga 1000 ta tabe baki ta siye data tayi download what's up tai installing messages sunata shigowa ummi tashigo ,"ke ki tashi ki kimtsa ga khalil nan shigowa "

faseelat tace "khalil ?"tana zaro ido

Ummi tace "eh ki tashi gashinan shigowa "ta juya Tabar dakin faseelat tace "mtssww shikenan fa khalil khalil maganar kenan ta kalli riga da wandon dake jikinta fakistan tace "ni shirye nake danban kara irin gayunnan saboda shi "

Ummi nafita tace yashigo tashige daki ta sako hijab.

Tare da Mubarak suka shigo yana dauke da katuwar bakko,
Har bakin dakin ummi yayi sallama ummi ta amsa tace "maraba ka shigo "

ya dan sunkuya dukda tsayin kofar ya shiga memakon ya zauna kan kujera ya xube kasa, a sannu ummi ta saci kallonshi tace "kambuu da wannan ne faseelat ke kushewa ina laifinsa yanda mazannan sukayi tsada,

Ummi tace "a, a katashi kazauna saman kujera "tana sunkuyar da kai na surukai,

Yace "ina yini, "batare da yakoma ma waccan maganar ba.

Ummi ta amsa akunyace yace "ya me jiki? "

Ummi tace "dasauki "

yace "Allah shi bata lpy dama zuwa nai nagaisheku"kanshi a kasa shima kunyar yakeji

Ummi tace " amin angode kwarai "

Dama da shigowar shi ya jingina bakkon jikin cushion hannunshi ya cusa cikin aljihu ya zaro kudi a kalla sunkai 10 ya ajiye sannan yace"ni zanwuce "

Ummi tace "to angode bari na kira maka faseelat din "
Bece komi ba ummi tafita Mubarak de na zaune ummi nashiga tacewa faseelat "ki tashi ki shiga ku gaisa "

faseelat da tunda taji sallamar shi taji zazzabi ya fara rufeta ta tashi tafita kamar me koyon tafiya,

Ummi tace "yar rainin hankali har ciwon ya dawo ko "

Faseelat ta shiga da sallama bakinta, wani sanyi ya mamaye zuciyar khalil ya dago kananun idanunsa ya zuba mata, kallo daya ta masa ta samu kujera ta zauna.

Yace "inawuni malama faseelat,"faseelat ta kalli zungure riyar hijab din dake jikinta tai shiru,
yanata kallonta yace "ya jiki?"

ta lumshe ido ta bude tace "naji sauki ai "

Yace "da sauki zaki ce de, tunda baki warware ba "

Tai shiru

Yace "to Allah yasa kaffarane "

Tace "amin "kasa-kasa

Ta dago ta saci kallonshi Sukai 4 eyes seda gabanta ya fadi ta rasa wane irin kallo yake mata, shiko kallon luv ne yakeyi, to da yake de sabon shiga ne se kallon yayi kama da kallon ruruwa🤦🏻‍♀Inajin harda kallon luv se kun koya mishi 🤣

Faseelat ta kauda kai sannan ta dago ta kara kallonshi lokacin ya dauke ido yana magana da Mubarak harda kudi ya bashi, wannan ya bata damar kallon dressing nashi a zuciyarta tace not bad,

Ya mike tsaye yana jifanta da wannan kallon yace "ni zanwuce "

tafara wasa da hannunta,

yace "ba bankwana?"

Tai shiru yace "to natafi amma plss ki rika daukar kira na i have called you several times but you don't pick my calls why? "

Faseelat seda murmushi ya kufce mata saboda jindadi atleast de yana iya kwantar da murya wajen pleading kuma ya iya turanci daya daga cikin abunda take so wajen mijinta.

akan idonsa tai murmushin wani farinciki ya mamaye shi ganin smile a fuskar ta,

Yace "I'm pleading I hope you will accept my request "

kawai ta girgiza kai dariya tazo kufcemata ta jawo hijabinta ta rufe fuskarta.
yayi dariya yafita ummi bata waje danhaka yawuce har kofar gida Mubarak ya rakashi khalil nata masa labarai,.

Yana wucewa Mubarak ya shigo gidan dede fitowar faseelat daga dakin taci dariyarta se kuma daga karshe ta dinga buga tsoki,

sukayi kicibus da ummi.

Mubarak yace "gaskiya ummi yana da kirki sosai jibi kudinda ya bani "ya fiddo yan 200 guda biyar da yabashi sabbi fill

Ummi batabi kan maganar shi ba hankalin ta na kan faseelat daketa murmushi ummi tace "wai lpya kike ta dariya ke daya "

Faseelat ta daure fuska "bakomi "tashige daki da sauri

Ummi tace "hmmm Allah ya shirya ki "

Ta Shiga dakinta, tana zare hijabin jikinta ta jawo bakkon ta bude kaya niki -niki, ta fiddo Ice cream da snacks din ta ajiye gefe guda,

Kudin da ya ajiye ta kirga nera dubu goma ciff ummi tai murmushi ta jawo wayarta tace "bari na kira hjy saratu nai mata godiya "

Batare da tunanin komi ba ta dannawa lambarta kira.....
[7/12, 10:58 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

🔟

Ringing biyu Hjy saratu ta daga bayan gaishe gaishe ummi tace "yanzu khalil ya fita yashigo har gida mungaisa, mun gode da abun arziki "

Hjy saratu tana ta faraa kamar duka knan tace "ah bakomi wlh ai anzama miye aciki "
Chapter 6 · 0% Book details