← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 130

Sashe 34

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru shiru hjya bata kira ummi ba ,don ummi nata tunanin zasu kira amma shiru ganin har anyi 1 month basu neme suba akaje aka kwaso kayan faseelat aka siyar, ummi nata tunanin cewa khalil zargin faseelat yake shiyasa be medata dakintaba sam bata bawa hjya laifi ba,

faseelat se rama take tana ganin rabuwa da fahad abu ne me sauki ashe ba sauki abun, gashi dukda ya shareta abinda yake nuni da bayasonta amma takasa hakura kullum seta kira amma baya dauka ta tura message a what's up yana viewing ammaba reply sosai hankalinta ke tashi, kwata kwata bata maganar khalil ta fahad kawai take,

Hjya da kanta take ansowa khalil ilajis sihir a Islamic chemist ma banbanta ,

Ganin khalil ya samu lpya har yafara zuwa school ,taga be kamata yayi ta zama haka ba dan har yanzu wani lokaci se ya zauna yayi shiru yayi ta tunani, takira shi tai masa maganar aure yace "hjya ki samo duk wacce tai miki ni kuma zan aure ta, amma dan Allah hjya karki nemo wadda zakizo kina kinta, nafison wacce ranki ya kwanta daita farin cikin ki shi nakeso banaso a memeta abunda yafaru"

Hjya tace "Nagode khalil Allah yamaka albarka ya baka abinda kakeso duniya da lahira "

Yace "amin"ya tashi ya fita, kawai ya amince ne don taji dadi ya tabbatar wa kanshi hjyarsu nasan shi saboda yadda ta rude da bashi lpya kadai ze masa bayani,sede bayajin ze kara son wata kamar yadda yaso faseelat, hakanan hjya ke ganin kamar kyan faseelat ne yafiso, batasan cewa faseelat na da wasu abubuwa ba da ba kowace Mace Allah yayi ma wannan bewar ba,

Hjya ta gama shawararta zataje batsari nemomishi auren jamila, diyar kanwar mijin siyama so daya ta taba ganin yarinyar kuma taga tana da kyau don fara ce sal ga ruman cinta tasha,

Lokacin da tajewa maman jamila da maganar ba tai musu ba, tunda tasan ko su waye su,

Tun kafin khalil yaje ganinta aka kai komi na aure akasa rana nanda wata daya duk cikin sati daya akai wannan hidimar,

Seda hjya ta matsawa khalil sannan yaje wurin jamila, yes tanada kyau amma daga ganinta yarinya ce dan shekararta 17 amma tana da girman jiki kana iya cewa takai 19 jss kawai tayi, jamila na da shegen wayon tsiya sannan akwaita da kwadayin balai don duk yadda zatayi taci nama setayi rumawa kenan😜bata iya girki ba tana de koyo ne sannan batai wani ilimin addini ba, hakanan suka gaisa da khalil ya masu sha tara ta arziki ya wuce gida.

Itako jamila khalil ya mata ita bata wani damu da bakinshi ko tsayin shi ba itade ta samu wurin da zata huta, kuma dama burinta tai aure cikin birni gashi ta samu,

Khalil be wani matsawa kanshi ba akan zarya zuwa wurinta ba, hjya ma da kanta ta saiwa jamila waya da tarkace akabawa siyama takai mata, kafin khalil yayi wa jamila kira daya ta yi mishi biyar,

a rana se ta kirashi so ukku, Ahankali yadan fara sakarmata fuska saboda yar ban dariya ce dolenka intai wani abun kayi dariya ganin tana yawan sa kati ta kirashi seya fara tura mata kati a sati 500 kuma yana iya cewa duk akiranshi suke karewa,

bewani rawar kai akan bikin amma hjya yadda takeyi kamar zeyi auren farko, khalil se gashi yafara tsumin kanshi 😂🙈 baya ga Islamic chemist har wani super market ya ke zuwa yana siyo kayan karin kuzari yasha wasu, wasu kuma yana ajiyewa se nangaba, dan seda gabaya da damuwa ta mishi yawa yake bawa amininshi labari shine yake bashi shawara yakara wayarmishi da kai anan yagano musabbabin raina shi da faseelat tayi shiyasa yanzu ya dage neman tsira da mutunci,

Siyama har yau batasan illar da hjya taiwa khalil ba har yau hjya bata kuma kara sa rakiya ido ba,

cikin sati biyu aka hada lefe aka kai akwati 10 reras aka kaiwa jamila, jamila nata murna ganin lefenta ta kira khalil tana mishi godiya "yaya Nagode sosai ni banma san taya zannuna maka jindadi na ba "

Yace "Allah? "

Tace "wlh kuwa se ganin lefe na ake zuwayi ana cewa nayi goshi "

Ya babbake da dariya itama tana dariyar tace "kana sona sosai yaya Nagode "

Yace "to ai dole na so ki jamila tunda kema kina sona "

Tace "yaushe zaka zo inason ganinka "

Yace "a, a gimbiya na kira na ai dole nayi sauri nazo ina nan zuwa gobe "

Tana murna tace "se kazo in zakazo kamin tsarabar kaza me dawafi "

Yana dariya yace "angama gimbiya "

Sukai sallama shi ba shi ya hada lefenba su hjya sukai abinsu itada siyama, ita siyama tanata karason abun don dangin mijinta ne,

Dole khalil ya so jamila yarinya ce kuma tana kula dashi abunda be samuba wurin faseelat ba gata da ban dariya ba ta jiran kauyancin shi yace yana sonta itake cewa tana sonshi, wani abu da yagane daita bata taba boye abinda takeso magana takeyi haka abinda be mata ba,

Biki nata matsowa suleman ne yaketa kara bawa khalil shawarwari da nuna masa abinda mata su keso dan shima yayi aure, da kanshi ya budawa khalil su facebook su what's up insta twee dasauransu yana kara fadamashi amfaninsu saboda kan mutum nakara wayewa inyanayin su kuma zaka rika sanin abinda duniya ke ciki,

Sosai khalil ya gano amfanin sharing problem da masoyi saboda zaka samu mafita da shawarwari har ta kai yanzu ba abunda suke boyewa juna shida Suleiman dama can rashin sakin jikin khalil ne yasa basa irin firar nan ,sosai khalil yagane kurakuran da yayi tayi a cikin zamansu da faseelat kuma baze karayinsu a wannan aurenba, yanzu bema da tym bare yayi tunanin faseelat suna busy hidimar biki,

Ranar biki taro yayi taro murna kowa yake ana abubuwa a wadace cikin kwanciyar hankali ba kamar bikin shi da faseelat ba,

bangaren amarya jamila dadi kawai takeji kokadan taki wani kuka ko ramar da akeyi batayi ba don Batasan miye aurenba ma, anata fahimtar jindadi kawai ne aure ka girka abinda kakeso, kai abinda kakeso a gidanka,

Karfe biyu aka daura auren khalil da jamila, ba laifi ancika kuma khalil ma yanata murna akai reception,

Jamila aka zaunar daita ana mata nasiha da bin miji da masa biyayya da yin duk wani abu da ze masa dadi dason danginshi da girmama mahaifanshi, da bashi hakkinshi akowne lokaci yaso,

se lokacin jamila tafara kuka da akazo daukar amarya dakyar aka bambareta daga jikin mamanta, aka tafi daita dakin mijinta katsina,

Karfe 5 ankaita 6 dede aka medo yan rakiya gida, aka baro amarya jamila dakinta.

Tunda taga gidanta da jeren dakinta tsit tai shiru, suna tafiya akabar yan cikin katsina suma karfe 7 :30 suka tafi bayan angyara mata gidanta ,suna barin gidan tafito tana zagayawa tana jindadi duk gidanta ne ita kadai, tuni ta manta da waazi murna kawai take,

Karfe 8:30 Suleiman ya rako khalil gidan amarya ta sanyo hijab tafito falo, Suleiman yafara musu nasiha da cewa...... "

*first knight a next page 😂maybe ango khalil ya samu zuwa duniyar bakwai🙈*

*Kusani inasonku zanyi iya kokarina don faranta maku, fan's adduar ku kawai nake bukata Allah ya cikamin burina*
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*SHALELEN GOLDEN*💃🏼

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

4⃣0⃣

"Alhamudulillah, anyi komi lpya ,kusani yanzu dukkan ku kunzama daya awaje soyayya kawai ake yanzu ne zaku san juna zaku san halayyar juna dole se kunyi hakuri da juna zaku zauna awuri daya a matsayin maaurata, dukkanku akwai hakkokin juna akanku kuyi duk iyakar ku kusauke hakkin juna, zo mu zauna hausawa sunce zomu saba ce, sannan kurike sirrin junanku, in kunsamu matsala ku sasanta junanku base wani yaji ba, , amarya kiyi bakin kokarin ki wurin farantawa mijinki rai hakanne ze bashi damar natsuwa yakara kyautatamaki, kai ango kaine babba kuma kaine shugaba dole ka rika uzuri ga wasu abubuwa bakomi ne ake magana akanshi ba kuma bakomi akeyin shiru akanshi ba, kayi iyakar yinka wurin kyautata wa iyalinka manzon Allah (S. A. W) yace mafi alherinku shine wanda yafi kyautatawa iyalinshi ni nafi kyautatawa iyalaina inafatan zakai koyi da manzon tsira, muna maku fatan alheri Allah yabaku zaman lpya da zuria dayyiba"

Suka amsa da "amin"

Yace "muyiwa annabi salati (S. A. W) yayi addua suka shafa

Ya tashi tsaye a"amarya Allah yabada zaman lpya "

Khalil yafita masa rakiya jamila ta tashi ta koma ciki tana shiga ta zare abayar jikinta kamshi ne ya bugi hancinta kamshin kazar da khalil ya shigo daita batare da bata lokaci ba ta dauko ledar ta zauna ta bude, tace "wow"tana zaro ido ganin gasassar kaza da vegetable acikinta ba bata lokaci ta fara yaga tanayi tana korawa da ziza don muguwar yunwa takeji,

khalil ya raka Suleiman ya mishi godiya ya dawo ciki seda ya rufe koina sannan ya shigo dakin yayi tsaye yana kallon wurin yanayin da yake ciki yanzu se ya tuna mishi da faseelat yayi murmushi ya kada kai ya shiga cikin dakin tsaye yayi yana kallon ikon Allah kowace amarya se anmata tayi take ci itako wagga bajira harta fara aiki,

Jamila ta dago tana kallonshi tana taunar naman tace "yaya bismillah"

Shi abunma dariya ya bashi itada zaaiwa tayi ita keyi mashi ya girgiza kai yace "kicinye abinki jamila dama ta kice "

Tako ce "tow"ta cigaba da yagar abinta,

Ya danyi dariya ya girgiza kai ya nufi toilet ya watso ruwa tareda yin alwala ya fito har lokacin tana cin namanta ba tsaitsayawa,

Yawuce ta ya nufi kitchen ya kunna gas ya saka tiger man aciki ya fito for some minutes ya rika kurba har ya shanye sannan ya dawo dakin, lokacin har jamila ta cinye kazar ta tass ta shanye zizarta, ta shiga toilet wanka,

Yazo yana tattara plate din yace yarinya gwara da kika ci kazarki,
Chapter 34 · 0% Book details