← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 130

Sashe 84

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hjya tabi ta rude tayi sambatu har muryarta ta shake dole tai shiru tana ta kuka batsayawa, matan dake wurinta sunata bata hakuri, hjy rabi tafara mata nata waazi "haba hjy kinaso kinuna Allah be kyauta ba komi? kituna fa Allah ne yabaki shi kuma ya amshi kayansa meyasa bazaki hakuri ba? Kiyi hakuri kita innalillahi wainna ilaihi rajiun ki kuma cigaba da mishi addua ita yake bukata a yanzu ,insha Allah yanzu khalil ba abinda yakeso fiyeda akaishi makwancinsa inamishi kyakkyawan zato kiyi hakuri Allah seyabaki ladar hakurinki, ko kuma kita kuka da surutan har Allah yayi fushi dake, hjy bayau akafara miki mutuwa ba ina iyayenki ina mijinki? duk kin hakura donmi yanzu bazaki hakuri ba? kuka dole ne amma ba irin yadda kike ba kiyi hakuri Allah yamishi rahma "

hjya ta cigaba da kukanta danbata jin wani waazi yanzu,

kawu manu sunje matuary mutane da yawa wadanda abun ya rutsa da yanuwansu ,har akazo kan su kawu manu aka tambayi sunan khalil suka fadi acikin list na fasinja harda khalil a motar su shidda ne ,

dandanan aka shiga dasu ciki akafara zaro maza daga lokokinsu ba kyangani abun, basuga khalil ba, abun yabasu mamaki ga sunanshi amma babushi dan sandan da kenan yace "to gaskiya kila babushi a motar don motocin duk sunyi ragaraga kaida ka gansu kasan ba ran daze fita daga ciki kuma ba gawar da tazama toka donba kasusuwa kuma wurin ba wasu gawarwaki awaje munyi screening sosai kuje kukara bincikawa ko kafin accident sun saukeshi wani gari "

su kawu manu suka fita suka nufi gidan hjya,

hjya na zaune tayi lakwas ko mutuwar alhaji bata girgizata haka ba, suka shigo suka zauna,

ta dago tace "manu ina gawar khalil? Ko gawar tashi ma bazan samu gani ba? "

manu yace "se hakuri hjy, Allah kadai yasan komi munje acikin gawarwakin ba khalil kuma dasunanshi acikin list na passengers ,kila babu shi cikin motar"

Hjya tafashe da kuka da shakakkar muryarta tace "khalil ya zama toka ya zaai aganshi,ashe kallon bankwana nayi mishi ayau, naso ya mutu yanajin dadi ba cikin kunci ba "

baban farida yayi sallama yashiga ciki,

kawu manu yace "ance ba gawar da ta kone, kode har yaisa batsarin shi?"

baban farida yace "a, a beje ba saboda yanzu mukayi waya da zulai tace beje ba "

hjya tace "khalil fa ya rasu shikenan banda kowa yanzu se siyama ba alhaji ba khalil "

Sukace "hakuri zakiyi hjya Allah yajikansu ya musu rahma "

Hjy ta kalli baban farida tace "ina siyamar? "

baban farida yace "suna asibity da jamila taji mutuwar se labour tataso mata "

hawaye suka zuboma hjy jin wadda ma yatafi biko tana cikin garin, se tausayin jamilar yakamata tanason khalil sosai, se hjyar taji yanzu ba abunda takeson gani se dan ko yar khalil ,

Tana share hawaye tacewa baban farida "mutafi asibitin "

Ta tashi ta dauko abayarta, ta fita su kawu manu da baban farida suka biyo bayanta, su hjya rabi ko suna zaune jingum jingum,

Baban farida ya budemata mota tashiga suka nufi asibity,

Suna zuwa siyama ta rungume hjy tana ta kuka se yazama hjyarce ke rarrashin siyamar, suna tsaye ba abinda sukeji se kukan jamila dake fitowa daga cikin labour room,

Fahad na isa gidan mommy yashiga jiki sabule ,ya fada kan kujera yayi zaune yanata tunani yanzu wane hali faseelat take ciki? zuciyarshi zafi kawai take for minutes sannan mommy tafito taganshi yanayinshi wani iri tace "lpy son naganka haka? "

yace "mommy amira bata lpy suna asibity tundazu "

mommy tace "subhanallahi tun yaushe? "

yace "tunda safe "

tace "shine se yanzu zakafadamin? "

Yayi shiru taja tsoki ta haye sama segata tafito da gyale da car key da jaka tazo zata wuceshi tafita,

Yace "mommy kitafin musu da abinci don haryanzu Aisha bataci komi ba "

mommy ta harareshi tace "tunda safe ace haryanzu bataci komi ba kai miye amfaninka ne dabazaka zo kafadamin ba in ita hankalinta ya dauku wurin jinya? Mtsswww "taja tsoki tafara kwadawa jummai kira, jummai tazo dagudu mommy tace "kingama dinner? "

Jummai tace "a, a amma akwai abincin rana kuma cikin warmer yake "

Mommy tace "daukomunshi dasauri"

jummai takoma tadawo da kula mommy ta amsa ta fita tashiga mota tai asibity,

Fahad nanan zaune dafe da kai yarasa yazayayi neman mafita yaketayi daga karshe yatashi yakoma kofar gidansu faseelat har lokacin kulle gidan yake yaja tsoki yanajin kamar yayi kuka ya bar unguwar,

mommy nashiga wurinsu Aisha amira ta rungumeta tana hawaye tace "mommy kitafi dani gidanki banison gidan daddy "

mommy tace "yi hakuri princess dake zan tafi kinji ko? Ki kwantar da hankalinki "ta kwantar da amira jikinta,

ta kalli Aisha dake koje koje tace "meya sameta?"

Aisha ta girgiza kai tace "zamuyi maganar after"

Mommy tace "okay kidaure kici abinci ko kadanne fahad yace bakici komi ba "

Aisha tace "banajin yunwa ruwa kawai nakeso "

Mommy tace "kibude jug gashinan ki zuba tea kisha amira nasa aka hadomashi itama ki zubamata "

Aisha tace "baride na zuba mata kibata ni zanfita nasamo mana drinks a reception "

Ta zuba tamikawa mommy ta dauki kudi ajakar mommy tafita,

Mommy tayi tayi amira tasha amira taki sema tafara rigimar ita anty "mommy ni anty nakeson gani ki kaini wurin anty"mommy tai shiru tana tunani dan tagano akwai abinda ke faruwa,

Su hjy na zaune sukaji kukan jariri yanata inyarrrr inyarrrr, hawaye suka zubowa hjya, dukda jamila ta haihu bata bar kuka ba nurses sukace ko ciwo takeji wani wuri batace musu komi ba tacigaba da kuka sunata fada itako bata fasa kukanta ba, suka shirya baby nurse tafito wurin su hjya dauke dashi,

duk suka tashi tsaye hjya hannunta har rawa yake wurin son ta amshi yaron, ta amsheshi ta bude fuskarshi yaron sakkkkk khalil lokacin da yana jariri, hjy se kuka ita kuka siyama kuka, Allah assamad khalil yatafi khalil yadawo, nurse tai tsaye tana kallonsu ganin suduka suna kuka ta juya takoma ciki,

Baban farida na tsaye ya rike hannu,

bayan mintoci aka fito da jamila aka medata rest room, su hjya sukabi zuwa dakin,

Jamila na kwance tana ta kuka suka shigo hjya ta mikawa baban farida jaririn ta matsa tariko hannun jamila tace "kiyi hakuri jamila, Allah yafimu san khalil shiyasa yadauki abunsa, "

fuska jage jage da majina da hawaye jamila ta kalli hjya tace "hjy kema kin yarda ya mutu? Wlh be mutu ba yana raye yananan zuwa baze tafi yabarni ba "

Hjya ta share hawaye tace "kiyi hakuri jamila kowa seya tafi can"

jamila takara fashewa da kuka, ko sanin me ta haifa ma batayi ba, hjy tasa hannu tana share mata hawaye tana rarrashinta,

Baban farida besan lokacin da hawaye suka zubomishita gefen ido ba, duniya kenan gashide wanda suke fada kanshi ya rasu dukansu suna kukan rashi yasa hannu ya share,

ana haka mamanta suka iso ,jamila takara wage baki tana kuka, duk dauriyar zulai seda tayi kuka,

gaf Maghreb faseelat ta farfado tana nishi ,idonta arufe ta tuno abinda yafaru tabude ido dasauri hawaye na zubarmata ta dafa cikinta dake ciwo, hawaye masu zafi suka kara zubomata,

ummi ta dafata tace "sannu faseelat ya kikeji?"

Se sannan faseelat tasan su ummi na wurin ta juyar dakai ga ummi abba,omer abul ishak da Mubarak harda baaba matar baba babba,

hawaye na cigaba da zubomata murya dishe tace "ummi cikin ya zube ko? "

ummi tace "kiyi hakuri haka Allah yakaddara"

Faseelat ta juyar da kai tana hawaye ,tana tuno yadda fahad ya rikice yarika dukanta kamar ba mutum ba, yanzu shikenan cikin ya tafi,

Ummi takatse mata tunani tace "bari na temaka miki kisha tea kokadanne "

faseelat ta girgiza kai tace "nakoshi ummi bazan iya cin komi ba"

Ummi tace"kidaure ko kinsamu karfi "

faseelat ta girgiza kai, dukkansu suka matso suna mata sannu ta rumtse ido bata amsa suba,

she wonder yaakai takenan ina fahad yaakai baya nan se su ummi kawai mike faruwa ne? Karde........zuciyarta tabuga da karfi, ta bude ido tace "ummi ina fahad? "

ya omer dake gefe zuciyarshi nacigaba da tafasa saboda halin da take ciki jin tana nemenshi yasa yaja dogon tsoki ya fita daga dakin,

Ummi rai bace tace"wane fahad kuma ke yanzu dan kina dakikiya ya nakada maki shegen duka daga farkowarki kifara tambayarshi wlh sunan fahad yafita daga bakinki ko natashi nai tafiya ta "

faseelat na hawaye tace "ummi waya kawoni nan?dan Allah kufadamin yana ina "

Ummi taja tsoki zatai magana abba yace "Dan Allah kibarta zafin ciwo ne bawani abu ba, kibari tadawo hankalinta sannan "

ummi ta tabe baki, faseelat ta cigaba da hawaye zuciyarta na harbawa tarasa gane meke faruwa,

Maghreb tayi musa da yazo duba gonarshi daga babbar riga, besamu yaje gonar bama seda aka kusa Maghreb don ya samu hadarin da yafaru, yagama abunda yake ya na cikin tafiya zuwa wurin da yayi parking motarshi yaga mutum sheme sanbal straight akwance acikin ciyayi,

Ya matsa wurin khalil ba alamun ko rauni jikinshi ya zukunna ya fara duba shi,

kamar wanda yayi bacci khalil ya tashi zaune, yana salati ya jujjuya kai gabas da yamma kudu da arewa ,sannan yadafe goshi yana jin kuwwar mutane da salati da mutane sukai tayi lokacin accident din,

musa ya dafashi yace "bawan Allah mekake anan yanzu da daddare? "

khalil idanunshi jawur zuciyarshi sanyaye yace "bansan yaakai nazo nan ba, nide nasan muna cikin mota, wata mota tahawo tamu daganan bazan iya tuna komi ba"

Musa yaja kabbara "Allahu akbar ,Allah me yadda yaso dama akwai ran da yafita a motocin can abun alajabi, bawan Allah lalle Allah nasonka daya barka da rai har zuwa yanzu domin acikin motocin bawanda ya fita duk sun kone "

khalil ya dago arazane, mutumen yace "eh duk sun mutu kaima ina mamakin ganin ka anan tunda yayi nisa da inda hadarin yafaru "

khalil yace "jinake kamar nayi bacci na farka amma nasan bakomi ne yasa Allah yatsareni ba se don yawan ambatonshi da nake kuma nakasance me kiyaye dokokinshi "
Chapter 84 · 0% Book details