← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 130

Sashe 18

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tai banza dashi ta cigaba da kukanta ya yi zaune yana kallonta, tana ta kuka kamar ranta ze fita shima se yafara hawaye, ita batasan ma yanayi ba can zuwa setaji sheshshekar kuka, tai sauri ta dago tana kallonshi ya dafe kai da hannu yanata kuka, wani malulu ya tokare mata makoshi ta tashi dasauri tai cikin daki tafada kan bed ta cigaba da rusa kuka Allah kadai yasan yadda takeji tagaji, tagaji kullum ta kwanta da miji a gado daya amma baya katabus kanshi kawai yasani be damu daita ba ,

Tana cikin kuka ya shigo dakin da ka kalleshi kasan yana cikin tashin hankali, kuma har lokacin yana kuka, ya samu ya hau kan gadon ya jawota jikinshi, yasa bayan hannu ya goge hawayen fuskarshi sannan ya fara gogemata nata, bata bar kuka ba shi kuma be dena goge mata ba,

Ya samu dakyar yana ajiyar zuciya yace "faseelat ki dubi girman Allah kifadamin mike damunki, lpy lau muka kwanta dake amma kintashi kina kuka, "

Tai banza dashi tana cigaba da kukanta ai halin da take ciki sede akirata marar lpya gabadaya duniya ta rasa me ke mata dadi tana kuka ta bakanta shawarar gwara taje taga likita don inta cigaba da zama haka zata iya jefa kanta cikin halaka,

ya cigaba da cewa "bazakimin magana ba faseelat? Ko Kinfiso kiga nima ina zubar da hawaye ,wlh faseelat jin kukanki nake kamar ana yankan naman jikina ki temaka kifadamin damuwanki "

Ta dago tana kallonshi duk yayi koje koje dashi idonshi jawur murya a shake ko kadan be bata tausayi ba sema wani tsanarshi da taji cikin ranta, tana sheshsheka tace "ban lpya cikina ne ke ciwo sosai da baya na "ta mishi karya .

Hannu na rawa ya dora a kan cikinta cikin nuna tausayi yace "sannu kiyi hakuri kinji zaki samu lpya "ya fada dasauri

Ya kwantar daita dasauri ya tashi ya fita ya debo ruwa, ya zauna ya fara tofi a cikin Cup din ta dan dago ta kslleshi ta cigaba da kukanta ,ya tofa fatiha 7,da Allahumma rabban nasa, azhabal baasa antashshafi la shifa'u illa shifa'uka shifa'un lah yugadiru Sakman,da a'uzu bi izzatillahi wa kudratihi min sharri ma'ajidu wa uhadiru7,(insha Allah in mutum be lpya ya dage da wadannan insha Allah zesamu lpy) dasauri ya tada ta zaune ya dora mata Cup a baki cike da kyankyami ta shanye tana meda numfashi yace "insha Allah yanzu ze lafa gobe da safe se muje asibity sannu kinji"to wai dama tofi na maganin shaawa ne? 😂toga de ustaz ash sheik khalil yayi se kujira kuga if its work kurikayi😜.

ya kwantar da kanta kan cinya yana shashshafawa dayan kuma yana kan cikinta yana cigaba da tofa mata A, uzu bi izzatillahi....

Tai shiru tana ajiyar heart, shima ajiyar zuciyar yake dan yasha kuka Ahankali ahankali bacci ya dauketa badan ta dena jin feelings ba, har tayi bacci yana mata addua jin tayi bacci ya ajiye kanta ya gyaramata kwanciya ya kwanta gefenta ya na kallon yadda fuskarta ta kumbura da tausayinta taff a zuciyarshi barawon barci ya daukeshi.

tunda asuba ya tashi ya Jona masu electric, yayi wanka ya tafi masallaci, har ya dawo tana bacci, kamar kar ya tada ta amma dole ya tadata saboda zuwa asibitin,

Kiran sunanta yafara yi ta bude ido tana kallonshi yace "ya jikin idan zaki iya ki tashi ki wanka mu tafi asibitin ko baza ki iya ba? "

ta rumtse ido tana magana aranta, "to in ban iyawa kai zakamin wankan?kajimin mutum"

Ta mike zaune tana cije baki ta dafe kai, sosai kanta ke ciwo saboda kukan da tasha ta saukar da kafafunta ta tashi tsaye se sannu yake jera mata ta shige toilet ta yo wanka tana fitowa tai salla ta saka kayanta, sega shi ya shigo da tea ya Mika mata ta sha, shi already har yayi breakfast suka hau mashin suka tafi asibitin lokacin wajen karfe 7da20 suna shiga asibitin ya ajiyeta ya fiddo kudi ya mika mata yace "ki shiga kiga likitan zanwuce school don ban dauki excuse ba in kingama ki kirani zanzo mutafi " ta anshi kudin kawai tajuya tana yatsina fuska ,ya dauki school kamar rayuwarshi har haushi takeji dan kullum 7 yabar gida.

Be tafi ba yana ta kallonta har tashige cikin reception don siyan kati sannan ya juya ya tafi.

Tana Shiga ta siyi card ta zauna jiran likita, fuskarta a duke abun duniya duk ya isheta tunani kawai take tayaya zata fadawa likita damuwanta, zuciyarta ce taita karfafa mata gwiwa ana haka taji ankira faseelat maaruf ta mike jiki ba kwari ta shiga office na likita,

Tunda tashiga likitan ya kafeta da ido he has never seen a cute and beautiful lady like her before har taja kujera ta zauna yana kallonta ta cikin medical glass dinshi,

Ta zauna tai shiru kanta kasa saboda kunyar abinda zata fada, likitan ya dawo tunaninshi ya gyara zaman glass dinshi ya meda kallonshi kan file nata yana memeta sunanta can zuwa yace "yanmata mi ke damunki "?

Tai shiru tana jinjina maganar yace "ehenn me ke damunki? "

Ta daure can kasa kasa tace "desire ne yamin yawa shine nakeso abani wani magani da zandena ji" takarasa maganar muryarta na rawa,

Tunda tafara magana yake kallonta cike da mamaki ,lokaci daya yaji yana sonta kuma he's willing to married her saboda be taba haduwa da such beauty ba da kuma irin tarin baiwa ta dadi ba, yes dadi mana duk macen da feelings yama yawa aidole tai dadi,

Jin shiru ta dago ta kalleshi he's black beauty kuma dagani beda shekaru, ta sadda kai tanajin nauyi ganin yayi kasake yana kallonta.

dakyar ya jawo tunaninshi yace "ammm zanbaki shawara mana dukda de u r young amma kifadawa iyayenki kina son aure, don duk maganin da zan baki yana da side effects kingane aure shine kawai solution and medicine to ur problem "

Tai sauri ta dago batare da tasan lokacin da tai maganar ba tace "I'm married woman fa plss likita ka temakamin zan shiga wani hali inna cigaba da zama haka "Idonta na kawo kwalla.

Duk dade likitan ba dan iska bane amma he has felt for her, jin tanada aure be mishi dadi ba, cikin mamakin tana da aure take neman maganin shaawa yace "mijinki baysnan ne? Ko baki samun satisfaction dashi?"

Ta dago tana mamakin tambayoyin ta girgiza kai,

yana basarwa yace "ki bani number dinki ni zan temaka miki da maganin matsalarki.......
[7/12, 11 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

*PAGE* 2⃣4⃣

*MESSAGE TO ALL MALE AROUND THE WORLD* *maza kutashi ku nemi maganin maza 😜majority maxan yanzu bakwa iya gamsar da matanku sukuwa kullum tunaninsu ya kare ne ta yin abinda zakuji dadi shawarata gareku ku tashi tsaye kuma kurika bawa matanku duk hakkinsu dan tseratar dasu daga fadawa halaka a yanzu lokacinan akwai matan aure da yawa masu neman maza don kawai basa samun a gidajensu, ku tashi ku nemi maganin basir😂da na sanyi ku tsira da mutuncinku a wurin matanku, mata mu munason harka sosai 🙈inde Kana badawa dede yadda zaaji dadi to zakaga kana samun wata good care awajen matarka, yes akwai mazanda suna da karfin da zasu gamsar da matansu ko ba magani amma kadanne ,kutashi ku nemi maganin saurin releasing kai ma kanka ai zakaso ka dade kana jin nice ,amma inde u r poor matarka zata rika tsanarka ne, 🙈I'm sorry fa amin uzuri gaskiya ce, Dan Allah muhada karfi mugyara rayuwar aurenmu ta hanyar kashe kishirwan Juna,inafatan maza na bibiyar novel dina dan sakon ba na mata kadai ne ba*

*🔊🔊🔊Maza a tashi asha tsumi aja girma🙈arika bawa mata kulawa a gado*

*dedicated this page to all married woman amma masu hakuri da yadda mazajensu suke*

Tana mishi kallon banganeba yace "ni ba dan'iska bane bantaba having sex da kowace mace ba, amma naji inasonki ki yadda in temakamiki zan baki duk kulawa, kuma zaki sameni jarumi saboda nasan kaina,"

Tunda yafara magana idanunta suka fara kawo ruwa takara fiddosu waje that make her extra beauty,hannunta na rawa ta dora shi saman bakinta tana cigaba da zaro ido, yana kallon yadda ta firgice lokaci daya ya janye glass din idonshi yace "come down, come down my friend, idan bazaki amince dani ba ki kashe aurenki ni wlh inasonki zan aureki nabaki duk wata kulawa da kikeso"

Tai sauri ta mike tsaye shima ya tashi "ki tsaya faseelat mu fuskanci juna plss"gani tayi yana niyyar kawo hannu ya tabata ta kwasa aguje tana kuka, yabi bayanta da sauri, yana fitowa nurse ta tareshi tana cewa "doctor patient dinnan gata can tana bleeding "

Cikin jin haushi yace "kije ki kula daita gani nan zuwa "ya diba aguje, ko da yafita harabar asibitin ba faseelat ba alamunta don tana fitowa tai saa wani me agwagwa da buje ya ajiye wata tai sauri ta shige,

Cikin jin haushi ya kaiwa iska bugu sannan ya tallabo keya dayan hannun kuma ya rike kugu, yana jin ya tafka babbar asara da yabar faseelat ta kufce daga hannunshi, ya sauke hannunshi yana kara jan tsoki sannan ya juya ya tafi duba patient dinshi,.

Faseelat ko a cikin adedeta se kuka take me napep din lokaci to lokaci yana kallonta ta mirror yana tunanin me kyakykyawa kamar ta takewa kuka har haka ,bata sanma yanayi ba dan gabadaya ta hargitse ,

Yana ajiyeta bakin kofar gida ta bude jikka ta zaro dubu daya ta mika mishi ta shige gida , yayi sakaf da dubu ahannu sanan ya girgiza kai tare da fadin "Allah ya kyauta"

Tana shiga ta samu ta bude kofar falon ta burma ciki da shigarta ta wullar da jakar hannunta ta zare hijab din jikinta ta wurgar tai jifa da dankwalin kanta ta duke ta dora kanta akan hannun kujera tana kara volume din kukanta,
Chapter 18 · 0% Book details