← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 130

Sashe 122

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta dan juya kai ta kalli faseelat dake tsaye tana ta kuka tana share hawaye da gyale,tace"faseelat nagode da soyayyar da kika nunamin nida amira ,inafatan zaki mana takwara don nima mutuwa zanyi"

Faseelat takara volume na kuka ta rufe fuska tanayi ,Aisha tai murmushin ciwo ta meda kallonta akan fahad ,tana ta kallonshi,

Yanata hawaye hannun ta still anashi yace"I love you Aisha u r part of my life"

Kallonshi take tayi bako kyaftawa,yanata hawaye ,

Lura yayi numfashinta ya dauke idanun basa motsi jikinta ya saki,

Nan take jijiyoyin kanshi suka firfito yakara damke hannunta ya duke jikinshi na kyarma agabanshi daddy ya rasu now Aisha bayan amira,kuka kezo mishi yasamu ya hadeshi,

Ya dago fuska ya juya yana kallon uwar yaya, tanata kuka da alamu batasan ta mutu ba,

Ya tashi jikin na rawa ya tsayar da jinin dake shiga jikinta ya juyar daita sannan ya rufe mata ido ya nufi wurin faseelat daketa kuka ya kamo hannunta batare da yace komi ba ,

Ta kalleshi ta kalli Aisha da aka meda kanta yana kallon bango ,takara kallonshi tashin hankali karara fuskarta ,

Dakyar yasamu Yace "mutafi in medaki gida"

Tace" ta mutu ko ?anty ta mutu"

Tai luuuu zata fadi ya tarbeta sede har ta suma ya ida zauniya kasa yasaki kukan dayake dannewa faseelat na jikinshi a sume ,

Jin kukan yayi yawa mommy ta shigo dakin ta ganshi rikeda faseelat yanata kuka,

Ta kalli gadon Aisha ta kuramai ido gabanta na faduwa taisa tana juyota taga babu rai jikinta ,hawaye masu zafi suka kara wanke mata fuska ,acikin ranta tace "ka kashemun diya son"

Ta zauna ta Dora Aisha jikinta tana kuka shikenan tayi bankwana daita shikenan ta tafi bazata kara dawowa ba,

Kukan Su momy yasa Su ramlat shigowa itada Su anty salma suka samu Aisha ta mutu dakin yakacame da kuka ,

Asibitin dake very silent takacame da sautin kuka nurses biyu suka shigo suka ga abinda ke faruwa sune suka kawo gado suka dora faseelat dake lifeless suka tafi ceto rayuwarta fahad ko nanan zaune yakasa tashi se kukan dayake kamar mace,

Mommy kam zuciyarta ciwo take sosai ,

Anty salma ce ta dauki Aisha datakoma sakwaf bayan sun rufeta suka fita daita ,dukkansu suka Mara mata baya basujira likitoci ba suka tafi abinsu ,

Faseelat kam suma tayi bayan sun samu ta farfado tanata kuka jinin ta ya hau sosai sukasa mata drip da allurai ciki dandanan bacci ya kwasheta ,

Fahad seda yakara shan kuka sannan yatashi yanjin jiri beko leka faseelat ba ya tafi gidan mommy akan hanya yakira wani yaronshi akawo likkafani ,sannan yakira sabeer ,

Sabeer na kitchen gimbiya fatouma tasashi aiki kiran fahad yashigo ya dauka yanata goge zufa yace"dude what's going on?".

Sheshshekan kukan fahad ta katseshi ,hankalinshi ya tashi yace"meya sameka aboki?"

Fahad na hawaye yace"I loss my Aisha ,Aisha ta tamutu "

Sabeer yace "innalillahi wainna ilaihi rajiun!!!!" Akidime saboda yaji mutuwar,

Murya sanyaye yace "kayi hakuri fahad Allah na jarabtar imanin ka yaga yadda zakayi kayi hakuri Allah yajikanta yakara maka hakuri na tausaya maka"

Fahad yace"thanks agidan mommy zaai janaiza "

Sabeer yace"I'm on my way yanzu"yakashe wayar yafita dasauri,

Fahad naisa dangin mommy sun cika gida angama hada ruwan wankanta yaje wurin mommy yace "mommy kubarni nai mata wanka kubari nai mata sutura plssss"yanata hawaye

Mommy tace"to kai zaka mata ,but plss kadena kukannan"

Yadaga kai ,yashiga dakinda Aisha take shiya mata wanka yanata hawaye aka kawo likkafani yasa mata yayi zaune wurin yanata kallon gawar,

Dandanan labarin mutuwar Aisha yabazu acikin garin dangin babanta dangin mommy Su Umma D's,bayan mutane suntaru aka kaita makwancinta ,

Kamar na amira kowa yatafi seshi da sabeer da yake taya amininshi hawaye ,

Yana zukunne yanata mata addua ganin de baze bar wurin ba yasa sabeer yadago shi suka nufi mota yanata waigen kabarin nata,

Jiri keta dibarshi dakaganshi kasan yana bukatar temako hakan yasa sabeer wucewa dashi asibity ,suna isa sabeer yace"plsss friend kayi hakuri kadauki kaddara karka bari wannan abun yayi affecting lpyarka ,I know kaga jarabawar mutuwa ,rashin daddy ,rashin amira and now Aisha amma duk da haka kayi hakuri yanzu zamushiga doctor ya dubaka "

Fahad dake dafe da zuciya yace"before that inason ganin faseelat bata lpy ta suma kuma she's alone"

Sabeer ya zaro ido jin wata kuma ya meda damuwar yace"don't worry zata samu lpy "

Fahad ya daga kai suka fita sabeer rike dashi suka shiga,

Office din okato sukafara zuwa yadubashi jinin shi yahau sosai kuma ga zuciyarshi dake ciwo to shima yana bukatar bedrest ,

Fahad yace"where is my wife?"

Doctor yace"don't worry shock data samu yasa tai loosing breath dinta sede itama she have similar problem da naka domin jininta yahau amma she will be okay"

doctor yasa aka kaisu dakinta tanata bacci tana sauke numfashi ahankali,

Hawaye suka cikawa fahad ido suka gangaro ,

Ya karasa bakin gadon shiko sabeer na bakin kofa yana kallonta,

Fahad ya duke jikin gadon yafashe da kuka,

Yana kuka yake cewa"they all gone suntafi sun barmu"

Hannunta yafara motsi da alamu tanason tashi ,

Sabeer yayi sauri ya rikeshi yace "plsss stop this crying karka tadata she need to rest mutafi they're waiting for you"

Yajashi suka fita dakyar suka samu ya kwanta akasa mishi ruwan amma idonshi ko rufewa beba,

Se lokacin yayi wa sabeer magana yakira Abba yafada mishi faseelat na asibity suka kamo hanya ,

Ummi na zuwa ta zauna gefen gadon faseelat arude tanata dubata ,

Ya omer da Abba na gefe ,

Faseelat din duk tafita hayyacinta,

Kukan Ummi ya tada faseelat ta farko tanata hawaye tana kallon ummi tace"Ummi anty ta mutu tatafi kamar amira"

Ummi tace "kiyi hakuri Allah yajikanta,ki daure karki sawa kanki ciwo"

Taita rarrashinta ,

Fahad na kwance drip nashiga sabeer na gefe yanata kara masa waaxi,

A can gidan mommy Umma nacan tuntuni sede mommy takara hawa da akace mata fahad bayagun karbar gaisuwa ,cikin ranta tace"yana wurin matarshi itada yakeso ta rayu son bemin adalci ba bemin koda rabin abinda na masa na alheri ba ,"itama seda jinin ta ya hau seda aka kira mata doctor,

Se marece aka cirewa fahad drip yatashi yayi salloli sannan suka nufi dakin da faseelat take,

Ummi na zaune beko kula daita ba yaje ya zukuna gefen gadon ya kamo hannun faseelat da har lokacin take kwance ,dukkansu suna hawaye faseelat tace"hero bata mutu ba ko?Dan Allah kace bata mutu ba"Se kuka ,

Yana kuka yace"she's died Aisha tana makwancinta "

Tana ta kuka tace"nata baka hakuri nata fada maka bata lpy kamata hakuri mutuwa zatai inbabu kai amma bakaji ba"

Yana kuka yace"I'm sorry nakasa manta abinda tamin ne ,kuma I don't know halinda take ciki wlh danasani da na medata tuntuni"sunata kuka,

Ummi da sabeer sunata kallonsu basu fahimci komi ba ,

Ganin kukan bana karewa bane yasa sabeer janshi suka fita gidan Umma yawuce dashi time din ta dawo ,shi kuma ya wuce gida yanata tunanin abunda yafaru,

Fahad nata ma Umma kuka tanata hawaye itama tana bashi hakuri dakyar ta samu kanshi ta debo abinci tafara bashi spoon daya kawai yayi ya dauke kai,

Yananan wurinta se Maghreb ya fita yaje masallaci yayi salla yawuce gidan mommy,

Dakin mommy yawuce direct ya samu anty salma nata mata fifit dukda AC dake dakin zufa take tayi,

Yaje ya zukunna gabanta yana kuka yace"mommy Dan Allah kiyafemin ,wlh bansan halinda Aisha take ciki ba what I only know is halinda nake ciki kiyi hakuri wlh name data dakinta kafin ta mutu"

Mommy dataci kuka tai hamdala idonta lumshe tace"son bakai ka kashe Aisha ba ciwo ne ya kasheta katashi kabar bani hakuri "

Yace"mommy inajin nine silar mutuwarta Dan Allah kuyi hakuri"

Mommy tace"to nayi hakurin amma dama bakai komi ba ,katashi katafi masjid ga kiran salla can"

Yace"thanks mommy " yatashi ya fita ,

Anty salma tabishi da harara tace"wai anty kinsan me kk cewa?"

Mommy tace "nasani mana kibar maganar yanzu Allah de yabani lpy"

Anty salma tace"to amin"

Saudat tazo daga abuja koda taga wucewar fahad da harara tabishi don duk gani suke shiya kasheta,

Acan Egypt Su lady duk gobe zasu sauka Nigeria suda mazansu,

Haka Su khadija dake sudan ,

Bayan isha'i yakoma asibiti ya samu anata daru da faseelat takicin komi yaje kusa daita ya zauna yace"meyasa bazaki ci abinci ba?kinaso babies Su samu matsal? Dan Allah ki tausayamun faseelat yanzu idan wani Abu ya sameku bansan yadda zanyi da rayuwata ba"

Ta share hawayen da suka gangaro mata tace "I will eat"

Ya amshi abincin yafara bata tanaci tana ajiyar zuciya,

Ummi de fita tai tabasu wuri, aranta tana da niyyar da an sallamesu suwuce gida da ita se ta haihu sannan ,don kullum kara zubewa takeyi ,

My condolences to Aisha fans Allah yasa maku hakurin rashinta,
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰

By

*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

9⃣0⃣

*Manzon Allah (S.A.W)yace bawata musiba da zata samu musulmi face Allah ya gafarta masa zunubansa koda kayace daya taka*

*Naji dadi ga masoya da sukamin fatan alheri ,adua da jinjina nagode sosai Allah yabar kauna .*

Bataci sosai ba yazo ze bata ta rike mai hannu so daya ya kalleta ya dauke kai takura mai ido duk yayi wani kala ta kyafkyafta ido tameda hawayen da suka zo mata murya dishe tace "kaci abinci kuwa?"

Yayi shiru be kalleta ba kanshi kasa ,

Tanajin matukar tausayinshi tace"plsss kaci abinci banaso wani abu ya sameka"

Dakyar yace"bazan iyaba I gone through a lot of pain ,faseelat kode naiwa Allah wani laifi yake jarabta ta?"

Hawaye suka gangaro mata tace "kodaya Allah yakan jarabci mutum idan yanason sa don ya kankare masa zunubansa "

yafashe da kuka ,

Ta rike kanshi tana sharemai hawaye tace"kayi hakuri nasan akwai ciwo amma kadena kuka kadena sa wani abu aranka,kasawa ranka dangana Allah zebaka ladar"

Ta cigaba da share mai hawaye ,yayi shiru zuciyarshi na zafi ,ya kalli katon cikinta yadora hannu akai yaji yana motsi ahankali
Chapter 122 · 0% Book details