← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 130

Sashe 67

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Faseelat hawaye masu zafi sharrrr suka zubo mata tace "seta zageni na kyaleta? Tunda nazo gidannan take fadamin bakaken maganganu na shareta, ta kaini karshe ne har na mata haka meyasa kai baka tsaya Ka tambayi baasi ba adalci ne wannan? Kuma nifa matarka ce ba diyarka ba ba baiwarka ba da zaka dakeni manzon Allah,S.A.W ya hana dukan mata harma yake cewa shin dayanku bayajin kunya? Ya daki matarshi da rana kamar yadda yake dukan bawa, sannan da dare ya sadu daita amma yastahyi? See my body plsss yadda ka fatattaka min skin wlh bakamin adalci ba"

fahad ya dafe kanshi dake sarawa ya rumtse ido yace "kiyi hakuri honey wlh naji kunyar zuwa gareki seda na tattaro duk courage dina sanan, I hate myself saboda haka, duk lokacin da na taba lapiyarki se naji duk duniya tamin zafi I'm sorry "

Yazo ze rungumota ta kauce yayi fuskar tausayi yace "kiyi hakuri hakanan plsss kibari naduba jikin"

faseelat tace"kagama tabamin jikina tunda banda wata daraja a wurinka "

Yace "don't say that inasonki kuma kina da daraja sosai awurina, kuma ai jikinki is mine yanzu haka nafiki jin zafin da kikeji kibari na dubaki"

Ya dauketa cak ya dora saman bed yayi tsaye yana kallon yadda jikinta duk yaji ciwo faseelat ta kauda fuska tana hawaye, ya juya ya fita adakin, yaje dakinshi ya dauko pain killer tablet pcm da ibuprofen da abonike ya dawo dakinta,

Tana nan kwance yadda ya barta ya bude fridge ya ciro cocktail ya hau gadon ya balli maganin ya tada ta zaune yace"kisha magani zaki ji sauki"

Faseelat ta kwaci maganin daga hannunshi ta shanye sannan cikin fada tace "niba wani sauki da zanji, yadda ka wulakanta ni gaban anty "

Yace "nace kiyi hakuri haba honey nine fa hero dinki"

Ta daga ido ta kalleshi ya marairaice fuska "kiyi hakuri plss pardon me "

Jin shiru be fito ba Aisha ta tashi ta haura sama ta duba baya dakinshi tai dakin faseelat ta tsaya bakin kofa ta kasa kunne,

Ya jawota ya bude murfin abonike ya fara shafa mata, tarika fidda numfashi saboda zafi tana fadin "ashhh, uhmmmmm"

Cike da tausayi yake shafa mata yadda take ta mommotsawa tana magana yasa shi jin shaawa ta taso mishi yafara shafarta cikin salo ,

Daga shafawa faseelat taji ya sauya salon,

Faseelat ta daga ido ta ballamai harara,cikin gajiyawa yace "I'm sorry please wai so nawa zan baki hakuri ne amma kinki kiyi nace kiyi hakuri insha Allah hannuna baze kara taba jikinki dasunan duka ba "

Faseelat tace "bazanyi hakurin ba dole ne senayi? katashi kabarmin daki kuma ko nankusa karkai tunanin zankara amincewa da kai"

Fahad ya tsura mata ido haryagaji da bata hakuri se yau yakara ganin hakurin da Aisha takeyi dashi can zuwa yace "faseelat ni kike kora daga dakinki ?saboda slice mistake kuma nabaki hakuri ai yakamata ki hakura, mijinki ne nifa dukda na zalunceki amma ai seki hakura Allah nason fa masu hakuri "

faseelat tamai wani kallo cikin tausayin umma tace "kai kana da hakurin ne ?ummanka tana ta zarya baka hakuri amma kaki hakura abu shekara da shekaru se yaushe ne zaka yafemata wai ko se tabar duniyar sannan ,this is what I want you to understand dole ne amaka laifi kuma dole kaima kayi ma wani seka yafemishi tunda kaima kanason a yafemaka"

Fahad yayi shiru yana tunani faseelat tace "think good,yesterday umma was crying asking for ur forgiveness tana tunanin kaine ka dauki wayar "

Fahad yayi shiru yace "OK I will think about it yanzu de ki yi hakuri kinji? "

Tace "bazanyi ba seka wa umma hakuri itama Ka yafemata just a single slap ne kaketa magana kanshi nifa u slapped me and beat me togather"

Fahad brain dinshi nakara tuno mishi abubuwan da umma ta mishi yace "ba marin ya fimin zafi ba bari na datayi nida mahaifina ta zabi wani shine yafimin ciwo "

Faseelat ta kama hannunshi tana kallonshi cikin kwantar da murya tace "it's ur fate, ko dayaushe musulmi yakamata ya rika daukar kaddara me kyau da Marar kyau kayi hakuri haka Allah ya kaddara ze faru "

"yanzu kayafema ta?"

Yayi shiru yana kallonta tace "idan ka yafemata ba karamar lada zaka samu ba, nima kuma na hakura duk da wannan likimon da kamin "ta Kalli jikinta

Fahad ya yamutsa fuska seda ya hadiye miyau yace "na yafemata amma saboda ke "

Faseelat tai murmushi ta rungumeshi tace "Nagode hero can I ask a favor? Again "

ya daga mata ido tace "please karika sauraranta in ta kira ka, koda na minty biyu ne hakan zemin dadi "

Ya cusa fuska cikin gashinta yace "I didn't promise you about that "
Ya fara mata kisses,

Aisha na bakin kofa labe tanajin su ,jikinta na rawa da tsananin kishi ta shiga dakinta tai dialing number mommy,

Mommy ta dauka tace "lpy kira goman dare? "

Aisha tace "ba lpya ba mommy wai yarinyar can daga zuwanta shekaran jiyar nan har tafara communicating da umman yaya, yanzunnan naji tana rokon ya yafe ma ummar abinda ta mishi "

Cikin jin haushi mommy tace "to yayafematan ne? "

Aisha tace "yace ya yafematan har ma rokonshi tayi wai ya rika daukar wayarta inta kirashi yace beyi alkawari ba"

Mommy tai dariya tace"ko ya yafemata rukayya bazata fini ba agunshi saboda hannuna ya taso reno nane, don haka ki zuba musu ido kawai, ya gidan naku yake dazun ya shigo gaisheni a harmutse"

Aisha tace "hmmmm anty salma ce tazo daga fitar ta naje na amshi amira tarike ta wai itama diyarta ce muka fara cacar baki wlh mommy sede naji mari a fuska ta, ashe yana kallo aikuwa yazo ya dauketa da mari yace tabani hakuri taki shine ya jibgeta ya fita "

Mommy tace "good yayi dede amma Aisha kidena yarda ko cacar baki tana hada ku saboda raina ki zatayi kibar shiga harkarta kuma kinsan inde ta salma zakibi kema jibgar zakitasha kinsanta batada tunani da hakuri ko kadan ki kama kanki kar in kara jin hakan tafaru"

Aisha tace "naji mommy "

Mommy tace "to seda safe ki kula da kanki "ta kashe kiran,

Aisha tai zaune tana tunanin baya, waifa faseelat ce yarinyar da take mata biyayya itace ta mareta, ta dafe kunci tana kara jin zafin marin,

Faseelat ta rike fuskar fahad tace "hero yau ba dare na bane ur heartbeat is there waiting for you, katashi ka tafi tunda dama a kagauce kake "

Yayi murmushi yana tuno dazun dan taji kishi kawai yayi haka don ya rama abinda tayi jiya, besan yadda ze kwatanta mata ba cewar besan tana waya da maza ba kosu dangintan,

Yaja hancin ta yace "korata ma kike ko? "

Ta girgiza kai tace "baniso anty taji badadi yadda kadade nan gwara katafi nasan tana can tana jiranka "

Yace "OK amma plsss kidena biyewa Aisha ki daure kirika bata girmanta ki mata biyayya kuma kiyi hakuri daita , banson tashin hankali a rayuwata "

Faseelat tace "insha Allah hakan baze kara faruwa ba, gobe zanma bata hakuri, a kullum bazan manta alherin da anty tamin ba yau ma bacin raine ya rufemin ido, itada yayarta suncimin mutunci bayannan anty tazo zata amshi amira awurina wai kada nabata mata tarbiyyar diya ni me bin maza da aure na, nafada mata kuskurene hakan da nayi amma me yahada haka da amira se cewa tai wai kila awurin ta gida na koya, naji zafi sosai da takirani mebin maza kuma tahada da mahaifiyata, wlh hero bantaba ko yin saurayi ba ,soyayyarka ce tarufemin ido har na manta auren dake kaina "

Fahad ya lumshe ido yanajin ciwon maganar da Aisha ta mata yace "naji kuma zan mata magana amma kiyi kokari kuhada kanku shine farin ciki na kuma kwanciyar hankali na"

Faseelat tace "insha Allah katashi katafi seda safe ,zanyi kewarka "

ya taba wuyanta "har yanzu da zafi jikinki fa "

Faseelat tace "ai ni na warke tunda ka yafewa umma, fatana de Allah ya dedeta tsakanin ku "

Yace "himmmmm diyar umma kenan "

Faseelat tai dariya ya mata good night kiss sannan yafita,

Dakinshi ya wucewarshi yana shiga yaga Aisha zaune tayi tagumi, bece mata komi ba ya haye gado ya kwanta ,

Aisha ta tashi tsaye kanta kasa taje bakin gadon ta zauna murya sanyaye tace "Dan Allah kayi hakuri yaya akan abinda ya faru baze kara faruwa ba "

Ya tashi zaune ya kalleta yace "meyasa zaki zageta eyeee, saboda neman fitina? inkin lura faseelat tana sonki son da take miki nema harya shafi diyarki ,laifine dan tana koyawa amira karatu? inda batason ki da bazata jata jiki ba ko da muna tare, kisani raini ne kike jawowa kanki kina zubda wa kanki girma awurinta duk biyayyar da take miki tadena"

Cikin ran aisha tace shegiyar fada maka abinda yafaru tai kenan ,ta jinjina tace "kayi hakuri yaya bazan sake ba, kuskure ne nayi "

Yana kallonta yace " Allah yasa amma kinbata min rai sosai"

Ta matsa ta haye saman cinyarshi tarika shafa sumar kanshi tana kashe ido da gantsaro kirji tace "ayya I'm sorry my sweetheart Allah yahuci zuciyarka" tarika lasar lips,

Yaja numfashi saboda yadda joystick dinsa ta motsa ya sa hannu yafara sabule mata riga,

yana fita faseelat ta shiga toilet tayo alwalan bacci tazo ta kwanta da temakon maganin datasha bacci ya dauketa,

ana kiran farko ta tashi jikinta duk yayi tsami sede fever din ta sauka, tana ya mutsa fuska ta shiga toilet ta gasa jikinta tafito ta balli maganin ta tsiyayi warm water a dispensa ta sha tazo ta kabbara sallar rakaatanil fajr,

Shima fahad yanajin kiran sallan ya tashi da yake Sun kwana suna jindadi yasa dole yayi wanka yayi salla ya nufi masjid da counter dinshi a yatsa,

faseelat nagama salla ta tafi dakin amira ta tada ta tai salla suka fara karatu,

kasancewar Monday ce amira zataje school yasa Aisha bayan tayi salla ta shiga kitchen tafara hada breakfast,

Yau dawuri fahad ze fita don basugama tattaunawa da bakinsu ba hakan yasa bayan yadawo masjid ya shiga dakin faseelat ganin suna karatu ya fito, yadanyi aiki a system ya tashi ya shiga wanka,
Chapter 67 · 0% Book details