← Book details Ragon Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 130

Sashe 48

Ragon Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sabeeer yace "OK see you later "yakashe kiran, fahad ya fidda iska daga baki ya cigaba da aikinshi,

Wajen 5pm faseelat tafito daga dakinta looking very happy tashiga dakin ummi, ummi na waya da sister nata dije faseelat taja tatsaya, ummi na kallonta tace "yawwa eh kibada alhaji babba yazomin dasu inze dawo, ki hada komi plsss masu kyau nakeso kinsan saura 3wks bikin kuma tanada kishiya, ba matsalar kudi zanturo miki dasu, abinda nakeso kafin ranar ma yakasa ganeta "

Faseelat na tsaye najinsu ummi ta kashe kiran ta kalli faseelat tace "amarya ya akayi ne?"tana murmushi

Faseelat ta sunkuyar da kai tana wasa da hannunta tace "ummi cewa nai me zaa dafa maku da daddare? "

Ummi tai dariya tana kallon faseelat tana jinjina kai tace "kin warke kenan? "

Faseelat ta daga kai tana murmushi,

Ummi tace "ai dole ki warke kinji zaki auri muradin zuciyarki ko bahaka ba? "

Ta kalli faseelat tana dariya, faseelat tace "lahh ummi ni wlh aa kawai naji sauki ne "

Ummi tace "isee any way daga yau bazaki kara shiga kitchen ba banmaso kina yawan fitowa tsakar gida saboda zafin rana, aikinki kawai kirika amfani da magungunan da zan baki, nayi magana da dije zata aikomin da wasu kafin lokacin zanbaki nawa kirika amfani dasu kuma kishirya nida kaina zan dilke ki kullum so biyu gobe zan shiga kasuwa zankara siyo wasu kayan, kede ki kwanciyarki kawai ga ango yakawo miki engine kita shan fanka "taida tana dariya

Faseelat tabata fuska itafa bata yadda ta kwanta tsohuwarta na aiki ba ta bude baki zatai magana ummi ta dakatar daita "karkicemin komi marar wayau kawai daga zaamiki abun arziki, duk abunnan dan inkara samar miki daraja nakeyinshi , ba don komi ba, haka wancan karan kika nace seda kika rika yin aiki, to wannan karan ko kinki ko kinso baxaki yi aikinba, gidan kishiya fa zaakaiki dole ki dage itama tana can tana nata shirin don bazama zatai hakananba Sonike kiyi dumdum ki kibarki koina ya ciko daga jikinki ,kiyi hakuri kinji ni nayafe tayani aikin Allah yamiki albarka ya baki kema wadanda zasu miki fiyeda yadda kikemin "

Faseelat tai tsit jin adduoin da ummi keta mata amma bahaka taso ba, har faseelat ta juya ummi tace "yawwa karki ci abincin dare nayi magana da hjy hajara anjima zata kawomiki kaza me hadi, mun mayi late tun saura 1month ake cinta amma dukdahaka de zaamiki ita, zakisha dadinki amarya so nake amiki harda dahuwar nama me nonon akuya, ciccibi,da sauransu kede ki daure da dadi ko babu kitaci "

faseelat tai murmushi tace "Nagode ummi "
Ta juya tabar dakin dasauri,

Ummi tai murmushi ta girgixa kai ta tashi Tawuce kitchen don yin aikinta,

Faseelat nakomawa daki ta bude data messages nagama shigowa taga anyi removing nata a mijina aljannata group ta shiga group din tanabin messages nasu tafara kwasar dariya tana dafe ciki ganin firarsu, tai deleting group din gabadaya ta wuce tafara bin messages nata, tagama karantawa tsaf ta fito ta shiga contact din fahad ta tura mishi "my love ya hannu hope dasauki murna ta hanani tambaya dazun"

Tafita ta shiga charting dinta da maman amira tana binsu 1 by 1 tana girgiza kai, kamar basune good friends dinnanba,
tana tunani tai mata text kamar haka "anty bazan gaji da baki hakuri ba, ki yafemin haka Allah yatsara ki kwantar da hankalinki plsss wlh inasonki bana da mugun nufi akanki ,ina rokon Allah ya sanyaya miki zuciyarki "tana gama rubutawa takashe data ta kwanta,

Karfe 7pm abul yashigo zeyi alwala ummi tace "kai tadawa amarya inji taga haske "

Yayi dariya "kai ummi abari har duhu yayi mana "

Ummi tace "katada mata inji nace tirka nakeyi "

abul yana dariya yatada injin din ya wuce masallaci,

Da isha fahad yakira faseelat gabadaya ta cire kayan jikinta daga ita se vest ba ko dankwali gashinta har saman kafada ta dauka tana murna tace "hi"

Fahad ya kureta da kallo wato vest din ta kamata sosai this make her look sexy

Yanata kallonta ganin yayi shiru tace mishi "why are you looking at me like this?kamin magana "

Ya sa hannu ya rumtse idonshi ya murzashi ya bude ganin nipples dinta a tsaye yakira sunanta "cutie "

Tace "naam my husband "

Ya nakara kallon breast din yace "plsss kidena receiving calls dina inkina sanye da vest, saboda I'm loosing my control duk lokacin da naganki ahaka ,kirika yafa gyale kar wata rana inyi something bad "

Ta Kalli breast din ta dago tace "okay I'm sorry bari na saka hijab dina murna ce tasakani dauka ahaka "

Yace "no no ba hijab nace kirika sakawa ba, banaso ne inrika ganin twins dinnan suna min Tayi saying plss suck us we need you "

Ta bata fuska tana mishi wani kallo, ya fara dariya ya hade hannu biyu yace "I'm sorry amma abinda suke fadane kallesu da kanki kiga "

Batare data kalla dinba ta mike tsaye ta jawo hijab dinta tasaka ta na hade fuska saboda ba tasan bad talk din da yakemata saboda yana sata wani hali ,
Ta kalleshi tace "banason haka fa "

Yace "naji, wannan hijab dinda kikasa ta banza ce nanda 3wks kome ze zama nawa inyi yadda naso"

ta kalleshi kasakasa ta sauya magana tace "ya hannunka? "

Yayi dariya jin ta waske ya dago mata hannun tana kallo tace "sorry "

Yayi shiru yana kallonta,

Suka cigaba da fira zuwa 15mnt sukai sallama, tana kashewa ta kwanta ta rungume pillows tanajin kamar ta jawo ranar bikin takoma gobe,

shima zaune yayi a garden din ya rumtse ido yana jin kamar ya jawo days din baya,

Bayan 10 mnt ummi takawo wa faseelat daHuwar kazar ta zauna tafara ci mugun daci keda kwai amma ta daure tana ci tana ya mutsa fuska,

Bangaren khalil ko tundaga ranar jamila tafara ganin sauyi awurinshi se yadena yi mata girki da wasu abubuwa da yakemata Seta fara dafawa da kanta, bayaci sede yaje gidan hjya yaci hakan nawa hjya dadi kuwa,

Jamila tafara rama saboda abinda yakemata take bawa makwabciyarta da suke zuwa islamiya tare labari,

Matar tace "gaskiya kinada bukatar gyara baki iya abinci ba jamila, kinga dama dole yarika zuwa yanaci wani wuri, gabadaya ma yakamata ki gyara rayuwarki ace miji shi ze hadawa kanshi break fast kafin yafita ai akwai matsala, kuma kidena maganar mahaifiyarshi uwa uwace fa jamila be kamata kina maganarta bama, inde kinshirya zan rika koyamiki girkin ke kuma ki dage dasauran "

Jamila tai mata godiya da yake tanada zuciya dandanan tafara koyon girki inta tashi kuma abinda yafiso wake duk girkin da zatai setayi dabarar sakashi da siyasa da kissa tasamu yadawo yana cin abincinta, batun bacci ko tuni ta ajiye shi tana tashi tanai musu girki, amma ta tsani hjy duk ranar jumaa yana kaita gidanta,seta kirkiro yin rashin lpy aranar, da khalil ya ganeta seya dena mata maganar zuwan yasa mata ido, dukda hjya bata damu da zuwan jamila ba dan ba abinda yake kara mata se haushi amma seda ta tambayi khalil meke hanata zuwa yace batajin dadi ne tundaga lokacin yasa masu ido su duka saboda hjy mafa ba sauyawa tai ba,

Bayan sati fahad ya tura kawunshi ya kaiwa abba makullin gida ya masu albishir da umara da fahad ya biya musu, abba yaji dadi sosai amma yaki amsar key din yace yafi son zama anan gidanshi ,yayi godiya da umarar da zasu bayan biki,

Koda alhaji yafadawa fahad yanda sukai ya shirya yaje da kanshi gidan bayan abba yafito Sun gaisa yace "abba kayi hakuri ka amshi key din nan nariga na mallaka maka shi, kuma gidannan zansa agyara shi kafin bikin, atemaka a amsa "

Abba yayi murmushi ya ansa yayi godiya, ya riga yagano fahad mutum ne me kyauta sosai,

Faseelat kau gyara taketa sha ciki da waje fatar ta tanata kara kyau kullum da hijab suke fira da fahad ko yazo ma da hijab take fita wani lokaci ya kan tambayeta miye sirrin tanata haske da kiba sede tai dariya tace sirrine,

Mommy awurin alhaji takejin labarin gida da umara da fahad yabiyawa su ummi, yau ya shigo gaidata ta amsa tana mishi wani kallo fuska ahade tace "wai kai haka akeyi ne ? kaita kashin kudi kamar wannan ne aurenka na fari, bazaka ko nemi shawara ba sede naji labari awaje"

fahad ya dukar dakai cikin sanyin murya yace "kiyi hakuri mommy daban fadamiki ba, kuma bawani kashin kudine ba nai musu "

Mommy tana hararanshi tace "duk ga gidaje nan plat kabasu mana amma seka basu me ginin sama "

Ya dago yana kallonta yace "mommy gani nayi duk abinda zanmusu ban biyasuba akan alherin da sukamin "

Mommy tace "eh naji sunmaka alheri kam sunbaka jawarar diyarsu "

Ya dukar da kai yace "kiyi hakuri mommy "
Yana mamakinta ya manta when last ta mishi magana gatsai kamar haka, kuma ita bata ko ganin hidimar da yake musu gabadaya shine abincin gidan suturarsu kudin kashewarsu, kudin makarantar su ramlat dukkansu sunayin prvt school ne university ,duk abinda sukeso shine amma mommy bata gani,

Ta dan saki rai kadan tace "shikenan , ni haryanzu banji kana maganar lefe ba yaake ciki ga biki yakusa ? "

Ya dago kai yace "nayi order daga dubai next 2days zamu tafi can da Aisha zamuyi 8 day's acan innaje zanga yadda kayan suke "

Mommy ta jijjiga kai jin lefen zawara ne har seda akabar kasa tace "toyayi Allah yakaimu "

yace "amin mommy nace nawa zasu isheki hidimane ?"

Ta danyi nazari tace "5million ta isa "

Yace "alright ya fiddo cek daga aljihun wando ya rubuta 5milion ya bata "

Mommy ta amsa tace "I'm grateful "

Yamike tsaye yace "inbasu isa ba amin magana "
Mommy ta daga Kai kurum ta rasa wadanne irin kudi ya tara haka dukda ba cikin kudin gadonsu bane don andade da bawa kowa nashi tun kafin nadiya mebi mishi tayi aure, tuntana Bin diddikin sanin dukiyar da daddy yabar mishi har tagaji tabari, saboda ta kasa iyakancesu kuma ba yadda zaai ta mishi maganar,
Chapter 48 · 0% Book details