← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 109

Sashe 92

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

gefen annah ta zauna a qasa byn tagaisheda annah da dady mua'zzam din,, gyara zama dady mua'zzam yayi sannan yayi yar gyaran muryan sa yace "Alhamdulilla ummu hani dafatan jikin naki dai yayi sauqi ko? dan cikin rawar murya na kamar mai shirin kuka tace "eh dady yayi sauqi,, gyada kai Dady yayi yasake cewa "ina fatan babu wani waje da ke miki ciwo kika boye mun ko ummu? danni a matsayin 'ya nike kallonki bawai inlaw taba dan haka ki saki jikinki kinji? gyad'a kai ummu tayi cikin kararriyar murya tace "banjin komi dady na ciwo allah kuwa, "to shiknn Alhamdulilla abinda dadyn ya sake cewa knn, sannan ya dubeta sosai yace "magana zanyi dake inaso ki dago knki ki dubeni kinji ko 'yata? rassss taji gabanta ya buga da sauri a hankali ta dago knta tana wasa da 'yar teddy baby small dake byn phone dinta wacce ke saman cinyoyinta, tace "to..to dady" tayi maganar a raunane sosai, gyaran muryan sa dady yasakeyi sannan yace "ina son insan cewa shin ummu hani miyasa kika tafo tun daga gariya garara har London batareda izinin mijinki ba??! Shiru tayi zuciyarta nasake doka mata da wani sabon iriyar sauti da dum!! dum!! dum!! dummm!! wato inta fahimci mgnr dady baisan mgnr sakin da dansu mahabeer yai mata ba knn ma? kasa magana tayi danjin wani abu mai kama da mad'aciya yataso ya tsaya mata a maqoshinta, kankace kwabo sai tafara kuka babu qaqqauta cikin mamaki suke kallonta dukknsu dn basuga wani abin kukanba,, momy umaima ta matso tareda rungumota gefen jikinta tana dan rarrashinta tareda cewa "haba kekuwa ummu hani na yadaga tambaya kuma sai kuka ya biyo baya?,, annah tace "ummu ko wani abu yayi miki acen ne dan nasan halin maqetacin jikan nan nawa?,, nanma kasa basu amsa tayi kukanta kawai takeyi tuni idanunta sun kada sunyi ja dasu sai fa daqyar suka samu tayi shiru takoma sakin ajiyar zuciya,, lura datayi sun kasa cigaba da maganar ne saitaji babu dadi kuma ta fahimci basason takura mata ne ita kuwa yau dole ta bayyana musu abinda d'an nasu daya shuka mata yake son boye musu gskiar hakan kuma. dan haka tashi tayi zaune tana goge fuskarta da qasan hijab dinta amman dudda haka wasu sabbin hawayen qara fitowa suke mata a fuskarta , ahaka ta dauki wayarta ta shiga wajen turo message ta shiga inda saqon mahabeer yake tana ganowa ta samu ta miqe tsaye cikin kyarmar jiki ta isa wajen dady mua'zzam ta miqa masa. da sauri kuwa ta dawo jikin momy umaima ta kife kanta a saman cinyarta tana matse qwallan tausayin kanta dan ita batajin komi sai yanda iyayenta zasu fahimci mgnr sakin nata, suce bataiwa miji biyayya ba harya sakota ne koko mi? shine abinda ke qara karyar mata da zuciya kuwa take qara sakin wani kukan wiwi,, dady mua'zzam tunda ya gama karanta saqon kuwa gaba day'a illahirin jikinsa jiqewa yayi sharkaf da gumi zufa har ta cikin hularsa tsattsafo masa takeyi, dole yasa hannu ya zare hular ya ajuyeta samn hannun kujera yahau firfita da wasan rigarsa dudda esikan dake falon kuwa hakan bai hanasa tsiyaya ta lemar jiki ba. allahuma ajirni fi musibati wa khalaqni khairan minha kawai dady mua'zzam yaketa sake maimaita wa daga cikin bakinsa,, annah da momy umaima a razane suke tamvayar miya faru hatta mahabeer ya tsorata sosai shima dudda baisan mike faruwa ba,, cikin sanyin jiki da mutuwarsa dady mua'zzam ya miqawa annah wayar ta cikaro da message din kuwa itama,, tana gama karanta wa a rude ta miqawa momy umaima momy umaima tana fara karantawa tunkan ta ida wasu zafafan qwalla suka dinga sunturi bisa fiskarta tana gamawa kuwa ta miqe tsaye a rude harda ture ummu dake kan cinyarta da qarfi sosai ta jifi mahabeer da wayar sai saman ha6arsa kuwa harta fasa wajen jini ya fito kuwa sosai,, da sauri taqarasa wajen tareda kamo kafadunsa tahau girgizasu da qarfi tana sakin wani mugun kuka tace "haba! haba! haba! miyasa ka yin kalar wannan danyen aikin mahabeer na? miyasa miyasa??! nace ka fadamun man mana bakkada hankali ne koka fara kayi shaye shaye ne kaima gayamun?! tana maganar ne cikin cimamiyo masa gaban rigarsa da jini ya gama bata masa farar t-sheet, sakinsa tayi sannan kuma ta duqe wajen tareda sake fashewa da kuka itama ,, gaba day'a illahirin jikinsa babu inda baiya rawa samshi bai damu da jinin da habarsa ke zubowa ba yafara hawaye shima yace "dan girman Allah momy kiyi haquri ki daina kuka bansan miya faru ba ku.... tasssssss tasssss yaji saukar wasu zazzafan mari akan kuncinansa 2 har kifewa yayi tuni jini ya kwanta masa a gefen idanunsa ya dafe kumatun nasa tareda zubawa dady mua'zzam dake tsaye saman kansa idanunsa cikin wani tsabar mamaki yau shine dadyn sa ya mara? abinda kuwa tun tashinsa ko dungurinsa dady bai taba yiba? gaba day'a nutsuwa tayi qaura daga jikin mahaber kukan ma shi ya kasa sai idanunsa dasuka koma kamar jan gauta,, cijin d'aga murya dady mua'zzam yace "zakace bakasan miya faru ba ko? kada kaga gatan da muke nuna maka yayi yawa ne haka mahabeer fa? a wata razananniyar razanar kuwa sabo mahabeer ya sake duban dadyn nasa yau shine dayn sa ke kiran sunnsa muraran?.. kanya dawo tunanunsa yaji dadyn yasake cewa haihuwa knn haihuwa mai rana share inama ace manal ce ta girma haka kamarka mahabeer ? Share hawayen idanunsa dady mua'zzam yayi yace "kaduba message din wayar da kyau saika samu damar musawa da kanka inda ba number ka bane aka rubuto saqon ko? yaqarashe maganar tareda dakawa mahabeer din wata gigitacciyar qara wacce tasa gaba day'an gidan kuwa amsawa da qarfi. a gigice mahabeer yadauki wayar daga gabansa ya fara bin message din da kallo da jajayen idanunsa yana fmn karantawa yana zubo da wasu dumammun hawaye dasukayi nasarar sauko masa ,, yana gama karanta saqon kuwa gaba day'a dukkan illahirin jijiyoyin jikinsa masu aikin kai saqo suka tsaya cakk kansa yaji tayi masa wani iriyar dummmm d'isssss kamar wanda ya kurmance kuwa, yakai tsawon minti 5 a haka sannan ya dawo Normal Allah sarki gwanin tausayi cikin wani rarrafowa qasa kamar yaro haka mahabeer yatafo yana zubda qwalla ya iso har gaban dady mua'zzam, dady yayi saurin ingejesa yakoma da rarrfe gun annah yana qara sautin kukan sa nanma annah ta janye qafafunta bai haqura ba nnma yasake rarrrafowa zuwaga momy umaima bata jira komi ba ta daukesa da wani sabon marin itama cikin kuka, haba aida mugun gudu ummu hani ta miqe tsaye tana gursasshen kuka tayo kan dady mua'zzam ta zube qasa tareda hada hannunta guda biyu tana cewa "dan Allah kudaina duknsa dady haka wlh banso banso banson ganin hakan nina yafe masa wlhd duka kawai kukaini wajensu baffa na,, !!! a gigice sukaji cikin wani qarajin kuka mahabeer ya kife kansa ga bango yana bubbuga wa tuni goshinsa ya fashe yana zubda jini da gudu ummu hani takuma kwasa tayo kansa da qarshen qarfin ta janyosa gaba day'a suka zube a gabnsu dady cijin mua'zm cikin dakusasshiyar murya mahabeer yace "kuyafen dady billahel azeem banine na sake ummu hani ba,,!! yana gama fadun haka kowa falon ya tsaya cak tareda zubo masa nasu idanun cikin rashin gasgata zancensa wanda sukai masa daukar qanzon kurege da raina musu wayau,, cikin tsabar takaici na ganin mahabeer ya raina musu hnkli dady mua'zzam ya girgiza kansa da qarfi babu shiri ya dafe kansa jin kamar zai ballo daga saman wuyansa ya fad'o qasa tsabar tention d'inda mahabeer ya had'a masa,, cikin sauri da rawar jiki sosai kuwa dady mua'zzam yayi saurinsa hannunsa a aljihu ya d'auko....
Chapter 92 · 0% Book details