Sashe 50
Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
samu mu huce hushinmu ta nan,, kwashewa da dariya nabeela tayi tace "yashigeki da yawa gskia mutuniyar, sorry zo muje kawai, haka suka dauko mayafin suka karb'i key wajen Momy sannan suka fice, suna shiga falon gidan suna cin karo da hannat ta d'auki wani shegen dressing kamar ba 'yar musulmai ba, tana ganinsu ta dunga jifansu da kallon banza tana hura musu hanci tareda tabe manyan labbanta tai musu tsoki tai wucewarta tana karkad'a key din motar ta ahaka tai wucewarta. dariya suka kwashe da ita harda tafawa da hannuwa bibiyu sannan da sauri kuma sukasa hannu suka rufe bakinsu suka koma yin ta ciki, basu jima ba hjy aina ta fito bana ganinsu kuwa tace "ah ashe har kunzo ina ciki ban saniba? ynxun muka gama waya da hajiya umaima din tace gashi nan ta turoku, amsan kayan da aka fudda muku, nabeela tace "eh munata sallama munji shiru shine muka zauna jira, "ayya kuyi haquri 'yan matan umaimah bari naje na kawo muku kayan to,, komawa daki tayi ta dauko musu kayan cikin leda ta miqa musu sukai mata sai anjima suka tashi suka tafi tana nan tsaye tabi bayan ummu hani da kallo cikin jin haushi, ta sa yatsa a baki ta ciza tace "gskia bnji dad'in rashin samun wannan dirarriyar yarinyar da bnba dana sameta aidana qara zama multimiloneir ta hnyar ta da wannan kyawun nata, amman gashi can ta zauna inda saidai taci tasha ta tsoma goma tasa biyar basa nemn kudi da ita?? cije lebe tayi tace "kai Allah tsinewa asara da rashin rabo ma wlh basuyi ba arayuwa" tatab'e baki tace "ya zanyi inda rashin rabo ya hauni sai haquri ai. haka tayi juyawarta ta shige daki. da daddare ne bayan mua'zzam saraki yagama kallon sa na N.T.A, ummu hani tana d'aki kwance, sanin datayi amakson din ta na falon shiyasa taqi fitowa ta jawo wayarta tahau chat itada nabeela. annah tana gefe itada mahabeer yasa mata rigiman saiya gyara mata zungurunta daya sassako. saida ya gyara mata sannan yayi komawarsa ya kwanta kusada dady mua'zzam saraki yace "dadyna tun safe nikeson ganinka in maka albishir, momy bata gaya maka bane naji bakace komi ba?, dadymua'zzam yace "albishir nami kuma sojana? duban Momy umaimah mahabeer yayi cikin marairecewa yace "momy kin manta halan baki fad'a masa ba? tace" bn mnta ba mahabeer na inda harna fadawa annah mah, shima dadyn naka dan bainan shiyasa, kuma da yadawo masallaci ya wuce, yana tasowa kuma kaga labarai ya tsaya kallo amman inda gaka gashi saika fad'a masa inda ance waqa a bakin mai ita tafi dad'i, babu b'ata lokaci kuwa mahabeer yace "dady daman maganar school din nan ce ta London wacce kasa natura request nason yin apply akan tsarin school dinsu na harkar sauqaqa kudin petroleum na qasanmu to shine d'azun da safe sukai accepting nawa ta hanyar @mail da suka turomin, sunce cikin wannan month din zasu fara project ga d'alibai, shine nikega a satin nan zan fara shirin shirye shiryen tafiya,r dama munyi da bash zai zauna min a office yana kula da komi kamin na dawo",, cikin fara'a mua'zzam saraki ya miq'a wa d'an nasa hannu suka jinjuna as usual sannan yace "dhat is gud sojana, haka nada kyau kam saika fara shirin tafiya, Allah shi temaka "amunn" cewar momy umaimah. Annah tace "uhumm kun gama?? nace kun gama tsarin naku kaida iyayen naka marasa tunani suma ko dukanku? to naji naku bayanin Saura nima ku saurara kuji nawa bayanin da zan muku yanzun nan basai anjima ba. dukkansu da kallo suka dinga bin annah cikin mamaki suke sake duban annah cikin qarfi hali dady mua'zzam yace ''annah yi haquri dan Allah wani abunne ya faru?? Annah tace "abinda zai farun ne dai ne nike shirin dakatar dashi in kuma kukabi abinda zance to falil lahil hamdu,, shiyasa koda umaimatu ta tunkaroni da maganar tafiyan nasa d'azun shiru nayi da nufin sai naji yanda kai zakace sannan, yanzu kai mua'zzamu da hankalin ka da tunanin ka zaka barsa yatafi har can qasan turawa batareda mata ba? to wlh bazan amince ba in ku kun amince, haba wannan qasashen da suke cike da marassa ta ido dud yanda mutum yakai ga kame kansa sai sunsan yanda akayi suka rinjayesa ya fad'a musu? to wlh bada niba muddin kuwa kunaso yatafi to kuyi masa magana ya fiddo mata cikin satin nan a d'aura masa aure ko da ba ai wani taron biki ba saiya tafi da matarsa in akayi hakan muma hankalin mu zaifi kwanciya, kuma kai ta numa mahabeer tace "karma ka kuskura kace wai wannan kiristan yarinyar zaka kawo mana sam wlh bazan lamunta ba, in kana samo musulman yarinya ka samu in kuma bazaka samoba to wlh babu kai babu wannan tafiyar London wannan umarni ne nabaku kaida iyayen naka dukkanku bawai neman shawara nayi daku ba ehe kujini da kyau kuma". tana gama fad'in haka ta zame zungurunta tanufi bayi da niyyar wankewa. dukkansu da kallo suka bita dan sam anma rasa mai magana ma a cikinsu gaba day'a annah ta kashe musu jiki....