Sashe 34
Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
🌊🌊🌊🌊🌊 🅿3⃣1⃣ 🌊🌊🌊 *A* nan ta sameta kwance bayan sallamar da tayi yayin shigarta room din. mamaki ya kama momy umaimah na ganin yanda ummu hani ta kwanta ta duqun qune jikinta waje day'a kamar mai jin barci, gefe daya kuma wasu busassun hawaye ne kwance a kan kumatunta. zama tayi grfenta Tana dan bubbuga hannunta tareda fad'in "ke?,,, ke ummu hani tashi mike damunki haka? da dan sauri ummu ta farka sannan ta miqe zaune daga kwanciyar da take tana fad'in "mah ina kwana,,, maganar take amman gaba day'a hankalin ta yanaga agogon dakin ganin ynda lokaci ya qure mata bata farka ba,, cikin rashin jin dad'in hakan ta sake duban momy umaimah tace "mah kiyi haquri dan Allah ban farka da wuri bane shiyasa bnje na had'a breakfast din ba, kuma,,,, kuma,,,,, tayi mgnr cikin sanyi sanyin murya tareda sartsewar hareshe. kasa ida maganar tayi tayi shiru kanta naqasa. cigaba da nazartarta momy umaimah kawai takeyi,,, ta fahimci kamar akwai damuwa tattare da ita ummu din,,, girgiza kai tayi tace"mikikeson cewa "ummu?,,,kibar d'ari d'arin nan fa dan Allah kinji? kisaki jiki kimin mgn normal dan Allah ummu hani na,,,, gyad'a kai ummu hani tayi alamar to sannan tace "momy ina gama sallah ne baccin ya daukeni kuma ina tashi ynzu naji jikina masassara ne" inaga ciwon da qafana kemum ne ya saukar mun d masassarar,,, cikin tausayawa momy umaimah take fad'in "assha Allah sarki mimakom ki fad'a mun ummu sai insa mahabeer ya kaiki kiga doctor ay hospital,,mike damunki ne? ummu hani kasa magana tayi sai fiddo mata qafafun da tayi taga ynda kumburin nan na jikinsu still Yana nan kmr ynda yake bai sa6e ba. "subhanalla ummu miya samu qafan ki haka kokin fad'i ne? Cewar momy umaimah din cikin tsananin tausayin ummu din da take,, tayaya zata fara cewan d'ansu wanda sukeso matuqa gaya kamar tsoka day'a a miya shine yayi mata wannan ta'adin a qafa? girgiza kai tayi wata zuciyar tace mata "Kaiii ina bazai yiwuba,,, samun kanta da d'agowa tayi ta dubi momy umaimah tace "mah sulbe ne jia da tayils da dare shiyasa qafan nasan suka kumbura dan na bugu sosai a qafan,,, "sannu ummu Allah sawaqa to bari naje na kawo miki abin karyawanki anan to tunda ga alama ma qafafun bazasu iya takuwa ba kozaki iya ne, a hankali ta girgiza kai tace "mah inajin kamar suna mun zugar ruwa ne bazan iya takawa ba, tausayinta ne ya qara sshigar momy umaimah tace "sannu bakomi kiyi breakfast din zanwa doctor lurwan waya sai yazo ya duba miki qafafun kinji ko ummu na, cikin muryar son yin kuka tace "ngd mah Alkah qara girma,,,amimm ummu karkisa komi a ranki ke a matsayin diya na daukeki,,ina zuwa bari na kawo miki kiyi breakfast din,,, daga haka ta fita daga dakin ummu hani tabi bayanta da kallo sannan ta sauke ajiyar zuciya ta dubi qafafunta cikin takaicin hakan a fili tace "wlh amakson bazan taba yafe maba,,, sai hawaye sharrr suka sake zybo mata a kumatunta. cijewa tayi ta daure ta miqe tsaye Tana mai sake bin bangon dakin taje toilet tayo burosh sannan ta dawo a hankali ta zauna a qasa dafe da qugunta da taji ya amsa mata kokaci day'a shima. Hade kai tayi da gwiwa kawai tasaki sabon kukanta. baa jimaba tayi saurin shanye kukan nata jin ana turo qofar dakin zaa shigo,,, momy umaima ce ta dawo wannan karan hadda annah da momy ni'ima ma a lokacin. ajiye mata kayan kalacin tayi tace "ngd mah,,, momy umaima tace "bakomi ummu na kedai Allah baki lpia, amin injisu annah. Anna tace assha assha ummu hani ashe kin fad'i a qafa ne? naji umaimah tana fadawa ni'imatu ne anan falo shine nace Bari nazo na ga yar gidan nawa,, Momy ni'ima tace eh annah nima yanzu na shigo gidan wajen qawata da kuma qara duba qafan d'ana sai kuma naji wannan abu shima daga ummu hani,, kai Allah baki lpia ummu ya tsare gaba kinji ko?, "Aminnn suka amsa da. saida ta dan tsakuri breakfast din badon dan jin dadin da bakinta ke mata ma kawai a'a tasan cewa in momy umaimah taga bata ciba zatayi fad'a ne kawai shiyasa. shiru tayi da cin wainar qwan da sotayyen dankalin jin momy ni'ima na cewa, gskia iyayen ummu suna da matuqar kirki qawata, yanzu kullum in akace miki safia yayi mamanta zata shigo ta gyara dud wani bangaren falon cikin gidan nan harta tayani wasu ayyukan? Kai gskia basuda ganda ta aiki sosai nikejin dadin zaman mu tare hakan ne yasa dud in na tuna kirkin nan nata in ana zaune da baban late boy na (mahabeer ) na kan ce baban boy har yanzu inna indo shiru babu labarinta? daga zuwa ganin gida da tace mana zatayi bayan sunan 6acewar yaronmu mahabeer amman tsawon shekarun nan shuru bata?,,, dud inna fad'a masa hakan nakan zubda hawaye domin matace mai amana a rayuwarta mutunci da karramawa wlh bazan 6oye miki ba inna indo na dauketa tamfar mama nace mun shaqu mun shaqu musamman ma lokacin da nikeda cikin mahabeer dud wani nau'in abincin gargajiya dataji inaso wlh komin wuyarsa za tanai mum shi, abin saiya qaru lokacin dana haihu kullum mahabeer yana hannunta tana matuqar sonsa, hakama ranar suna tana kusa dani taredashi sam ko motsawa batason yi takance wannan kyakkyawan mijin nawa masha Allah sai dai muje can garin su mamanka (mecca) ka samo min kishiyata a can vadai anan ba, dan inka samu kalan ka zakuyi matching kuyita haifamun kyawawan 'ya'ya ni kuma a lokacin kaga na qara tsufa angona sai naita maka renon yan dugwi dugwin yaran namu,, dud inta fadi haka dariya mukeyi nida baban boy a lokacin,, wlh daran ranar ne da mahabeer aka sa cesa ban mantawa ta shigo dakin nawa lokacin ina feeding din mahabeer yana cikin jikina tace "dan Allah d'iyata kiyi qoqarin ganin kinyi kaffa kaffa da mahaberu jikina kwata kwata bai yadda da lamarin abokiyan zaman nan taki ba hajiya Lariya saboda nasan matar can bata kirki wlh sam,, dudda nasan cewa maganar ta gskia ne dan koni haquri kawai nikeyi na zaman mu tare mutumin daya fito qiri qiri yace baya sona da qaunata aikasan kowaye wannan mutum din abin yakai intiha na tsanin qiyayyar dayake makan,, amman dan dai kawai in bawa inna indo qarfin gwiwa akan maganar yasa nace "komi zatayi inna indo nina fawwala Allah komi Allah natareda bayinsa kada kidamu insha Allah ba abinda zai faru zata dawo dai dai ne itama addu'ar danake mata knn" inna indo din tace "kayya wadda bata cikin yabo injii 'yan magana,, ni dai 'yata banga alamun wata rusuna daga matar cen ba, amman Bakomi inda kince Allah ai shiknn magana taqare kam," Wlh qawata in taqaice miki labari haka muka wuni a ranar tare da ita tana riqe da mahabeer takasa ajiyesa (mai karatu in ka tuna a ranar ne inna indo taji hajia larai tana mgnr da aminnanta ta yanda za'a dakin ni'ima a fako idonta a sato mata jinjiri mahabeer danta cika burinta na ganin bayansa, to mafarin knn inna indo din taiwa ni'ima wannan jirwayen maganar amman taga bata dauki maganar ynda ya dace ba, mafarin knn take manne da mahabeer a ranar sam ta kasa rabuwa dashi, sai lokacin da ta koma dakinta ta ajiye mahabeer din anan bed net dinsa ganin maman nasa na shirin kwabe kayan jikinta ta shiga wanka da daddare knn. da sauri inna indo ta koma dakinta a lokacin ta dauko qaton hijab dinta tareda wata takarda ta linketa ta sanya cikin wani ambulant wanda tun sa'ilin data dawo bngaren hajia larai ta rubuta rubutun sakamakon daukar shawarar da zuciyarta ta bata a gameda mahabeer muddin taga mamansa bata dauki mataki ba, ta gama hadasu waje day'a ta boye jikin zaninta sannan ta lallaba ta koma side din ni'ima din taga har lokacin bata fito daga wankan ba, ai da sauri ta zari mahabeer wnda keta barcinsa ta goyasa da farin showel dinsa ta fice daga gidan,,,.....) shiru momy ni'ima tayi tace na shiga tashin hankali lokacin dana fito bnga yarona ba wlh ban qara samun lpia ba daga lokacin,, baban boy kuwa sanarwa babu wacce bai bada bs tsawon wata da watanni amman shiru kkji,, ga kadaicin inna indo data tafiyarta garinsu a washe garin ranar a cewarta bazata iya zaman rashin mahabeer ba,, daqyar muka shawo knta hatta yarda ta amince da cewan zata zauna, amman dan Allah muyi mata uzuri akan cewa zataje can Qauyen nasu gano babanta dabashi da cikakkiyar lpia dayake mmnta ta rasu saidai kishiyan Mmnta din ce, kama ba kulawar ta yake samuba,, anan muka yardar ta tafin bayan baban boy ya bata isassun kud'aden ta.... wannan tafiyarce da tayi tasa na qara shiga matsananciyar kewa dudda baban boy kullum yana taredani yana rarrashi na da cewa insha allahu zaa gano mahabeer. amman duddu haka wlh ni kadai nasan ynda nikejin a raina dan 6acewar yaro ba qaramin fitina bane gar gara ace yau gashi Allah ne daya haliccesa ya karbi abinsa wannan kasan cewa eh bazai dawoba kuma kasan inda ya tafin nan kaima sai kaje,.kuma abin mamaki dudda muna gida day'a da hajia larai wlh dai dai da rana day'a bata taba shigowa ta jajanta mana ba akan 6atan yaron namu ba, ahaka har tsawon wasu watannin 3 babu labarin ganin mahabeer babu na dawowar inna indo kuma gashi bamu san qauyen nasu ba bare muje muji komi nene ya riqetan bata dawoba,, har wasu watannin hudu suka shud'e amman shuru kkji dole tasa na fidda rai da samun mutanen nan anan nadasawa baban boy rigiman maidani can gida mecca amman ya dinga rarrashina,, nikuwa bn taba iya yi masa musu ba tun rayuwar mu ta zaman aure,, shida kansa daga baya ya daukeni muka tafi mecca din wajen iyayena ganin ynda ciwo yasa bn iya moruwan komi ko abinci bn iyacinsa tsawon cokali 4. Shiru momy umaimah tayi gaba day'a wajen jikinsu yayi la'asar sunji sun qara tausayawa momy ni'ima akan rashin danta ba qaramin wahala tasha ba Ashe dai, tuni ummu hani taji tama daina tausayin dan ciwon jikinta dan tasan ciwon dake cikin zuciyar momy ni'ima ya zarce nata sau