← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 109

Sashe 84

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

wani iriyar mugun duhu ne ya mamaye idanunta,
nan ta zube saman gadon ta saki wani mugun kuka mai qarar gaske tana fadin "miyasa zakai mun haka amakson?! saida kabari na saba dakai sannan zakaimun wannan mummunan sakayyar? shin wai wane iriyar mugun qiyayyar ne kake mun haka?? miyasa?! miyasa?! miyasa?!!!, wani Murmushi takaici tasaki cikin kukan tace "dama wannan saqon shine kake cewa zaka turomin mai gigita qwalwa?? jitayi ranta yasake yin wani tsananin b'aci tareda wata iriyar muguwar tsanarsa data durar mata a rai nan take, ta miqe tsaye daga gadon nasa dan batajin ko minti daya zata iya qarawa a gidan da ba'asan darajar mace ba, tana hada kayanta tana kuka wiwi hadda majina tana share hawayen da hijab din jikinta, da qyar ta gano passport dinta cikin jikkarsa, sannan ta debi kud'adenta ta sauko qasa tana jan troleey dinta tana fita waje sukaci karo da sera ganin tana kuka yasata cewa "ahhh sister tamu miya faru kina kuka?? Ko kallonta ummu hani bataiba dan qagare take tabar gidan,, tana fita kuwa tayi sa'ar samun drop nanta ce masa airport xai kaita, tashiga yaja suka tafi har zuwa airport din,,, rashin sani ashe motarsu mahabeer na fitowa daga airport din bayan sunga tashin jirgin su mukhtar su kuma taxi din da ummu hani suke ciki ta shiga filin airport din,, dayake abin na kudi ne nan danan aka shirya mata biza ta shiga sahun fasengeer ko minti biyar bataiba jirgi ya daga bnda kuka babu abinda ta shige cikin qaton hijab dinta tanayi, tana nuno kamar jia ne sukazo garin cikin jirgi ita dashi,, amman gashi yau qaddara ta fiddota,, tun tana kuka mai hawaye har saida taji kukanma kansa ba dadi dole ta haqura takoma yinna zuci, sune basu sauka nigeria ba sai Misalin tara na dare, taxi tasamu ta kwantata masa anguwar nan kuwa nan da nan sai gasu cikin anguwar 'yan majalissu ta bashi kud'insa ta shiga falon gidan tana jaye da trolley tana kukanta marar hawaye sai gunji,
annah ce da momy umaimah ke zaune a falo suna yin hira aiko kamar daga sama suka ga ummu hani ta shigo ta kife kanta anan bakun qofar tana kuka, har bangaje juna annah da momy umaimah suke har suka isa wajenta suna hada baki wajen cewa"ummu??! ke ummu hani lpia miya sameki?? daga dawowarku sai kuka? Inashi mahsbeer din yake kuma neto??!!
gani kawai sukayi ta sulale qasan wajen idanunta a kakkafe ko baqin ba'a gani sai farin,,, bakinta kuwa banda fitar da wani farin kumfa babu abinda yakeyi, zuwa can suka ga ma ta daina yin motsi kwata kwata, jikinta ya saki gaba day'a babu inda ke motsawa tartare da ita sak matatta.....!

*Xexen Fasaha*
f. o. w.
[10/11, 2:49 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb 💤💤

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.
Chapter 84 · 0% Book details