← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 109

Sashe 45

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

qawata ummu na nunawa momyna ita,, momy umaimah tace "babu damuwa nabeela kuje sai kun dawo to, haka nabeela taja hannun ummu suka fice cikin farin ciki. ita kanta ummu hani lokaci day'a taji nabeela ta kwanta mata arai sosai sosai kamar 2 mi. Momyn nabeela hjy asma'u da taga ummu itama ta yaba da ita,, sun jima tare sannan nabeela ta rako ummu gida itama ta koma nasu gidan, haka ta kasance kullum sai nabeela taje wajen ummu sunyi fira, lokaci guda sabo yashiga tsakanin ummu hani da nabeela sosai kamar irinma wad'anda suka jima da sanin junansu daman can, takai ta kawo harsu baffa da momy ni'ima sunsan da qawancen su ummu hani da nabeela, kuma nabeela ta fahimci wacece ummu hani a gidan, dudda Momy umaimah bata fito filii ta nuna cewa 'yar aikinta bane a farkon had'uwansu saidai ita data fahimta daga baya. zuwa yanzu barci kadai ke rabasu dan sun shaq'u sosan gaske. 6angaren mahabrer kuwa tunda ya koma office ya rage zaman gidan sosai inba weekend ba shima inya shige daki ya dauki laptop dinsa yahau bazai sake fitowa wajeba saita kama mafarin knn ma suka daina haduwa da ummu inda itama yanzun data gama aiki suke shigewa shashin Momy umaimah itada nabeela suyita fira abinsu,, satin bikin mukhtar ya kama wato yau takama alhamis da Misalin qarfe 8 na dare yagama shirinsa cikin hadadden shigarsa ta farin boyel sai sheqi yake, ya kawo hulansa q'ube read colour ya d'ora ta a kansa ta zauna sosai gwanin kyau, wnda hakan yaqara qawata kyakkyawar fuskarsa, sajen nan nasa kwantacce yasha gyara yayi wani luf -luf yas -yas saman fuskarsa zuwa qasan ha6arsa, bash dake zaune gefen bed dinsa yace "huhh!! kai gifted billaheel Azeem za'ayi zaton kaine angon ay,,, kaganka kuwa? yanda ka had'e tsaf kanata faman tashin qamshi kamar wanda yashiga cikin perfumes yayi wanka?,, mahabeer farin watch dinsa ya dauka ya daura bisa lallausar farar fatar hannunsa wacce ke cikeda gargasa sannan ya dago ya dubi bash yace "pleass is ko bash, mutafi ko? dan kasan bansan african time tunkan ango yafara danno mana Kira kagane ai? Miqewa tsaye bash yayi yace "hakane mutumina muje kawai tom" saukowa sukayi falon gidan nan suka iske momy umaimah tana karanta littafin addu'oen ta yayin da ummu hani da nabeela suke zaune qasan carpet suna buga game daga zaunen da suke, cikin computer d'in nabeelan da tazo da ita, har wajen Momy umaimah mahabeer ya qarasa ya runguneta ta baya ya bata sumba a goshinta yace "cheap momy na zamu wuce mu sai mun dawo,, "to mahabeer na sai kun dawo bashir ka gaisheda ango mukhtar, "to momyn mu zaiji sosai, wani ihu su ummu hani sukayi na q'ara saboda game over din da zuma game din nasu ya basu wanda sai lokacin nema mahabeer ya lura dasu awajen ma , tsoki yaja mai qarfin gaske wanda hakan yasa ummu hani saurin ankarewa dashi a wajen ta d'ago kai tareda zuba masa fararen idanunta shima kuwa ya sauke mata nasa idanun gamida cika mata idanuwa da harara da kalar kallon sa gareta na wulaqanci, Murmushi kawai tayi abinta cikin halin ko in kula irin nata data tayi masan, a hakan ma koda tazo janye fuskarta garesa saida ta d'an wani murgud'a masa baki itama sannan tabisa da hararar itama tareda sake maida kanta wajen game d'insu sukaci gaba da buga abinsu,, nabeela kuwa daman sanin kota gaidashi ba amsawa zai yiba shiyasa ta shafawa kanta lpia bata sake tankawa ba tun byn gaisheda bash datayi kuwa. Koda sukazo fita tanan wajensu inda suke zaune mahabeer suka biyo, da gayya yasa cover shoes d'insa ya takewa ummu hani babban d'an yatsa na qafanta yabi ta kansa ya wuce, bash kuwa ya gansa ashe tym din. wata uwar q'ara ummu hani ta q'wallara kuwa ba shiri.....shi kuwa ida ficewarsa sukayi ko kallonta ma baiba bare yanuna ko yasan shine yayi mata aika aikar. "Subhanalla ummu hani lpia???!, cewar momy umaimah, nabeela kuwa baiwar Allah dutta rud'e ta riq'e ummu tana fad'in ''sister na minene ya faru haka? share hawayen fuskarta ummu hani tayi da bayan hannu tace sannan "takamun qafana yayi"!!, har had'a baki suke momy da nabeela wajen cewa wanene ya takakin? cikin takaicin furtama sunansa daga bakinta tace "amakson ne ya takamun qafa na mah"!!, dafe kai momy umaima tayi tace ''ya ilahee!,, kai wai mike damun yaron nan ni umaima? "Kiyi haquri kinji ko ummu barshi zai dawo gidan ai yasameni kinji ko? gyada kai tayi tace "a'a Momy ni na yafe masa nasan bai sani bane, tayi haka ne danta fidda damuwan dataga momy umaimh din tashiga gameda hkn, Murmushi momy umaimah tayi tace "to qiln hakanne amnan komi nada kula ay, kamata yayi ace yakulan ai, Nabeela tace "myn masa afuwa ai Momy babu komi, "to shiknn Allah shi muku albalbarka yarana, duknsu suka amsa da "Amunn mah, haka sukaci gaba da buga game dinsu yatsan qafan Ummu nata mata zunga dan takawar ba qaramin shigarta tayi ba daurewa kawai takeyi. A mota kuwa bash yana gefe yayinda mahabeer shine yake driving nasu juyowa bash yayi ya dubesa yace "gaskia gifted kana takurawa yarinyar mutanen da yawa wlh, sam kabi ka hayyaci yarinyar nan ina lura dakai tuni batun yau bafa, mahabeer yana jinsa yayi masa shiru driving dinsa kawai yakeyi hankali kwance. cikin annushuwa yake jujjuya kan styarin motan hannun nasa a haka har suka isa qaton hotel din da ake partyn, yana gama parking ya sa remote yarufe dukkan glass tintac din motan sannan ya juyo wajen bash ya sakar masa wata harara yace ''waitttt mlm to inkai bakaga abunda taimun ba toni nagani dan haka kadaina samun ido haka ok? Ko sauraron amsar bash din bai tsaya yi bama yayi wani ficewarsa daga motan ya rufo murfin motan da qarfi,!!!!! tabe bakinsa shima bash yayi gamida wara hannuwansa yace "wannan kuma matsalar kuce kaida itan ba tawa ba, dan haka kuje kuyi tayi ina ruwa na, wanda baiji bari ba ai zaiji hoho ne". tare suka shiga cikin hall d'in wanda yake cike tatil da isassun mata 'yan mata da samari gogaggon 'yan boko gayyar ango mukhtar wanda yayo hayarsu daga manya manyan h- instution, elder sister na ango da amarya ma sun hallara wajen ba'a barsu a baya ba. kujerun gefen ango guda 2 wnda an tanadesu ne daman sabida mnyn abokan ango har kan kujerar wata budurwa taiwa su mahabeer jagora tanayi tana wani lanlanqwashewa ita ala dole saita burgesa musamma dataga dud yan matan wajen hankalinsu yatafi ga yalla6ai mahabeer mua'zzam saraki yaro da fire2..,, wata budurwa dake gefen yan uwan Amarya ta tab'o qawarta tace"wow ihsan wannan ai wannan guy dinne mahabeer mua'zzam saraki ko? wanda ake posting nasu a gidajen television shida dadynsa?,, huhh cewar ihsan din tace "eh wlh laurat a fili ma yafi qara mun kyau da had'ewa ma,,,,,dudda fuskarsa a d'aure yake Wlh ba qaramin masifan kyau Allah yabasa ba, ya had'a komi fa wlh, nan sukayita santin mahabeer wanda shi babu daya daga cikinsu dayai mata kallo ko d'aya, tunda ya maka dark brown eye glss nasa yanata muzurai nashan qamshi sai kowace yarinya datake shirin rab'arsa a wajen sai tasha jinin jikinta saidai naisa naisa kallon kura dasuke binsa dashi. firarsa kawai yake da ango cikin qus qus bamaijin miyake cewa hatta Bash kuwa dake kusa dashi. Haka akaci aka sha sai 1 saura sannan aka tashi, a gajiye mahabeer ya ajiye Bash gida shima ya wuce ya isa gidan, koda ya shiga falo bai iske kowa ba kai tsaye dakinsa ya wuce yabi lafiyan gado ya kwanta babu jimawa barci ya suresa, saida asuba sukaje masallaci shida dady mua'zzam basu dawo ba sai da gari yayi haske sannan, qarfe 10 na safe suka fice daurun aure shida bash zuwa 11 har an daura auren mukhatar da amaryar sa. daganan aka zarce da shagulgula babu kama hannun yaro, kwana 2 da gama biki ya ja bash sukaje katsina suka d'auko annah, sai wajen biyar na yamma sannan motarsu ta dira a farfajiyan gidan dukansu suka fito daga motan suka shiga cikin gidan inka dauke bash daya juya da motar ya fita. Momy umaimah na kichen itada ummu hani da nabeela sun gama shirya abincin tarar annan wajen kala 5,,suna gyaran wajen ne suka jiyo sallamar annah daga can falon, ai da gudu ummu hani ta fice daga kichen din ko towel din hannun ta nagoge wajen bata ajiye ba ta ruqunqume annah da qarfi tana fad'in "oyoyo annah ta i missing you alot annah sosai, annah dariya kawai takeyi tana fad'in "nima kina raina ummu hani na kullum Amman dai sakeni in sarara haka ki kayar dani, sakin annah din tayi cikin siririyar dariyar tace cikin shagwaba da turo dan mitsitsitsin bakinta tace "kai annah uhm ehm tayaya zan iya kadaki nikuwa??, kan annah tai magana mahabeer dayake riqe da jikar kayan annah ya buga wani dogon tsoki,,, da sauri ummu hani takai dubnta garesa dan ita bata tsammaci yana wajen bama, "dalla malama niki matsamin hnya in wuce, binsa tayi da fararen idanunta qar suke kamar madara da digon baqin daya qara fiddo mata da kyawunsu afili, jitayi yasake daka wata tsawan yace kin warke makanta ne koko? Useless girl isay move me from here, annah tace ''o'o o'o,, kai dai ka cika fitina Wlh mijin nan nawa,, jawo hannun ummu hani tayi suka zauna bisa kujerar tace "rabu dashi kinji ko ummu na, Murmushi ummu hani kawai tayi sannan tasake d'agowa ta dubesa shima ita din yake kallo lokacin da yake qoqarin wucewa kaiwa annah jikkar ta cikin dakinta, sakar masa harara tayi tareda saurin dauke idanunta a kansa lokacin da momy umaiah tashigo falon hannunta daukeda juns da cup tace "annah oyoyo muna miki sannu da hnya,, "yawwa umaimatu 'yan katsina suna ta gaishe daku ay, "muna amsawa sosai annah, "annah sannu da zuwa" cewar nabeela data zauna kusa da ummu hani. annah tace "yawwa naveela, quta mahabeer yayi yabar wajen, ta gaban annah yazo zai gifta anna tace "kagani bani jikkata nan kaji, ina zaka kaimun ita kuma ban bawa kowa da tsaraban saba,kasan ance da zafi zafi yafi ai" ajiye jikkar yayi zai wuce samansa
Chapter 45 · 0% Book details