← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 109

Sashe 59

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tareda janye hannayen da tayi tagumi dasu, da sauri ta juya ganin dady Muhammad ne yasata sakin ajiyar zuciya tace "baban boy da yaushe ka shigo ban jika bama?, cikin murmushi yace "kinyi zurfi da tunani daman bazaki san nashigo ba, maganar yake amman can qasan zuciyar sa tabashi cewa qilan babu shakka tunanin danta mahabeer ne abin ya dawo mata shiyasa take wannan tunanin, dan murnushin qarfin hali ta saki tace "afuwan habibina hankalin yayi balaguro ne shiyasa banji shigowar kaba, muje dining na shirya maka lunch ko, fitowa sukayi falon nanta hau shirya masa abuncin a dining table, saida yaci sosai yayi hamdala nan ya fara jan ta da fira cikin son boye gaskiar abunda ya faru momy ni'ima ta dube shi tace "habibina amman yau dai gidan hjy laria zaka inda daman jian abunda ya hanaka zuwan kamar yanda kasa ba sabida watom masassaran data saukoma lokacin, dady Muhammad yace "hakane amarya ta zanje yau insha allah dudda bn son rabuwa dake dai dai da minti 1 amman dole na haqura na kwatanta adalci a gareku a matsayinku na mata na ku duknku, murmushi momy ni'ima ta dan sakeyi batace komi ba, sai zuwa can tace "hjy laria dinma bata jima da fita ba ay, lokacin datayi wannan maganar dady Muhammad yana qoqarin kiran layin wani abokinsa, nan da nan kuwa ya yanke kiran ya maida hankalin sa kacokam zuwa gareta yace "whatt ni'ima ta? Hjy laria tazo gidan nan fa kikace?! tomi ya kawo ta inda nai mata kashedin zuwan nata nan tuni ba tun yauba, inda nasan zuwanta din ba haifuwar d'a mai ido zai yiba yanda take jarababbar nan,? cikin sauri momy ni'ima tace "a'a kwantar da hankalin ka zuwa tayi kawai muka gaisa kuma ta tafi babu wani tashin hankalin da tayi mun, abunda yasa ta boye gaskiar abunda ke nan kuwa tasan muddin yasan gskiar sai yaci mutuncin hjy laria sosai fiye da yanda ita din tai mata, ita kuma gashi sam bata son taga tana zama sanadiyyar dazai dinga jin zafin uwar gidansa hjy laria din. Kallon ta kawai yake amman yasan tadai boye ne kawai amman yasan cewa wlh ko wuqa da varandami aka kawo gabnsa zai iya fadin hjy laria bata shigo gidan nan ta ficesa salin alin ba batareda ta zubar wada ni'ima samfur din nata ba na kalar cin mutun cin nata ba kamar yanda ta saba. Sharewa kawai yy sukaci gaba da fira dan baison yawan maido magana baya. anan ne yake shaida mata tafiyarsu Niger din gobe tace "to shiknn AllAh kaiku lpia asamo abinda ake nema kuma" da amin ya amsa yana fad'in "amma samu ai insha Allah. nabeela da ummu hani ne zaune bisa gadon nabeela a gidansu, duban agogon hannunta ummu hani tayi tace "sister lokaci na tafiya inason tafia gida kada mah taga shirun yayi yawa kuma gashi sai jana da fira kike tun dazun suprise dinma da kike magana akai ya gagara ki gwadamun" tayi maganar tana hararar nabeela din. qyalqyacewa da dariya nabeela tayi tace "kai amaryar yaya amakson kin cika gajen gaquri kam,, hararta ummu hani tasakeyi tace ''mtsss wai dan Allah sister saunawa zan gaya miki kidaina hada ni da wannan azababben mutumen? nabeela tace "taya kuwa zan daina had'aki dashi bayan kun kusan qara jonewa a babban tsibirin ma'aurata taqarashe maganar cikin tsokanarta, fuuuuu ummu hani tayi fushi ta miqe tsaye zata bar dakin da gudu nabeela takamo hannunta 1 tace "afuwan sister inda bakison maganar na daina, qin yadda ummu hani tayi data qara zaman saida nabeela ta shawo kanta da qyar2 sannan ta haqura suka zauna a gefen gadon hannunta nabeela ta daura gefen kuncin ummu hani tace "sister miye yasami fararen kumatun kin nan naki naga yayi ja haka?, tana maganar cikin mamaki tabe baki ummu hani tayi tace "hmm! kad'an daga cikin aikin amakson knn!!, zaro idanuwa nabeela tayi tace "kaddai kice mun shine sila sister? girgiza kai ummu hani tayi tace uhmm to inba shi ba waye kike ganin zaimun haka ne? bama ki kalli lips dina ba knn kikaga yanda yaqara mayar mun dasu ja sosai ba? da sauri nabeela takai hannunta ga lips din nata tace "aikuwa wlh gashi nan har wani pink pink colour yamayar miki dasu kalar nasa kai wannan amarcin nakufa so matching,hararta ummu hani tayi tace "wlh inkika saki na tashi bazan qara zama ba, rufe bakinta nabeela tayi tace sorry sister na, harararta ummu hani tasa keyi tareda jan wani d'an siririn tsoki, wardruf nabeela ta bude ta fiddo wasu manya manyan baqaqen ledoji ta dawo saman gadon ta zazzage su dukknsu nan, tace "ga gudummuwata nan sister dan nasan kina son inglesh wears sosai shiyasa na karb'i kud'i wajen dady na isassu tun jiya da dare naje boutique na siyo miki su shine nike cewa zan miki surprise dasu ay". cikin mamaki dajin dad'i ummu hani tace "kai sister thanks so much wlh amman wannan dud ni day'a basumin yawa ba? cikin murmushi nabeela tace "kinfi qarfin irin haka sau dubun dubbata a wajena sister, kuma basu miki yawa ba kamar yanda kika fad'a , murmushi ummu hani kawai takeyi tana d'aga kayan tace "kai sister kayan nan akwai a tsokani shari'a sosai a cikinsu fa? dan na gama kusan ma dud su sukafi yawa saikace wata wacce zatayi auren soyayya bare in rinqa yiwa hubbyn nawa kwalliya dasu? ,sai nikega irinsu dake yadace saiki dinga yiwa amrinin dinki gayu dasu, girgiza kai nabeela tayi tace "a'a wlh sister bazan dauka ba dan nikena sawowa snn kuma inada tabbacin cewa zakiji dad'insu kuma zakiga amfaninsu nan gaba, dan aunty sadiya qanwar momyna tace mu'amala da wad'an nan kayan suna qara jawo hankalin miji akan matarsa inda da sune matan waje har suke nasarar iya cin galaba akan mazanmu,sai nikuma nikega why to muda mike matansu mizai hana muyi fiyeda yanda su nawajen ke musu,? yamutsa fuskarta ummu hani tayi tace "hmm sister na kenan inda ake soyayyar knn kiketa fad'a ai badai gani ba da wancen farin mugun,, bnda dariya kuwa babu abinda nabeela keyi tace "kai sister yanzu yah mahabeer d'in ne ya koma miki farin mugun knn, cikin tab'e lips tace "yess shifa da knsa sister bawani ba,tayi maganar tana mai mi miqewa tsaye. murmushi kawai nabeela tayi tana yar dariya tace "hmm Allah kawo muku mafita mudai muna nan nijeria zamu sha labari daga gareku 'yan qasan turai,, tana maganar ne tana mayarda kayan cikin ledarsu. banza ummu hani tayi mata harta gama suka fito ummu hani taiwa maman nabeela hjy asm'u sai anjima suka fito tareda nabeela saida sukazo bakin gate tabawa ummu hani kayan sannan tace "by sister zan shigo anjima" a haka ta juya ta koma gida, ita kuma ta ida shiga cikin harabar gate d'in gidan, da sauri ta b'oye jikin wata bishiya maiyawa daga qasanta koriya ce shar, dan hango sa datayi shida bash zaune can wajen swimming pool inda suka saba zama, tarasa ta inda zatabi dole tadinga bin ta bayan bishiyan nan harta isa ga qofar shiga gidan dud abin nan kuwa datake bash na lura da ita tun shigowarta gate din gidan yaganta. murmushi kawai yayi a boye ya raya kuma a zuciyarsa da cewa dud yanda akai ta had'ota ne da mutumin nasa shiyasa take faman bo'yo batta son ya ganta. ita kuwa tazo shiga falon gidan kenan ta jiyo shassheqan tashin kuka a falon gidan, gabanta ya fadi sosai kuwa, d'an dakatawa tayi jin magana tayi ance "haba hjy umaimah dole hannat tayi kuka ai wlh, kinkuwa san irin son datakewa yaronki mahabeer a cikin zuciyarta? amman shine har kika iya amincewa aka basa wata banzar yarinyar buzuwa can dangin asiri?!" murmushi na mamaki momy umaimah tayi tace "dole na yarda kuwa hjy aina inda bani na had'a ba iyaye ne suka had'a kuma nima da yardata dan ummu hani yarinya ce tagari wacce kowace uwar miji tagari zatayi kwadayin ta zamo mallakin ta, hjy aina tace "aho wato mu mune surukn banza kenan kk nufi ko hjy umaimah? cewar hjy aina, momy umaimah tace "badai kiji hakan daga bakina ba kam sai dai inke kika dorawa kanki,, muryar annah taji ta fito tana cewa "waimi ke faruwa ne tun d'azun haka nikejin hayaniya da kuma koke koke, Nan momy umaimah tayi mata bayanin komi nagameda kukan da hannat takeyi wa uwar tata tun a gida hatta sa uwar tata tafowa nan babu shiri. jiyowa annah tayi tace "toke hjy aina antab'a sha'anin tursasawa haka? basai kibawa 'yar taki na annabawa ba(haquri) inda hukuncin an riga an zartar gameda kyakkyawan zab'in da a kaiwa yaro? du AllAh hayaniyar nan ta isheni kudaina haka musamman muryankin nan da kukan yarki wlh sun hanani saqat a daki ina hailala,, tana gama fadin haka tajiyo takun tafiyar annah ta koma dakinta. jiyowa hjy aina tace "shiknn hjy umaimah ngd da abinda yafaru, tana fadin hakan kuwa ta jawo hannun hannat din da qarfi sukayo waje, rab'ewa tayi awajen tabasu waje harara hannat keta sakarwa ummu hani kamar idanunta zasu fado qasa tace "banza shegiya dangin ma'asurta. da sauri ummu hani tace "kul wlh niba shegiya bace da ubana kan wani can adaina zagarmun iyaye, tayi maganar cikin gatsine fuskarta. cikin masifa Hannat tace anzagi iyayen naki ko wata tsiya ce daku baccin ta asiri ne eye? cikin gatsine fuskarta ummu hani tasake cewa "oho dai naji kuma wannan, ngd Allah inda dai har banzo nayi kuka akan ba'asoni ba na zubda q'imata ta mace kamar yanda wata tayi ynzu, hjy aina ta jawo hannun yartata tace "nace kirabuda ita kizo mutafi ko? inda kin jawo mana abin fad'i ba shikenan ba hankalin ya kwanta ba 'yar banzar yarinya sai nacin tsiya uwa matar shugaban mayu na dudduniya haba har abin ma ya isheni wlh bagaira ba sabar kinsa na gayawa aminiyata magana "!!! Hannat kuwa sai turo baki take ta yiwa uwar har suka shige motarsu suka bar gidan. da harara ummu hani tabi bayansu harta shige falon itama taga momy umaimah ce kawai, anan ta gwada mata kayan da nabeela ta siya mata momy umaimah ta yaba itama sosai nan sukaita fira abinsu sai daga bisani suka shiga kichen dan d'aura girki
Chapter 59 · 0% Book details