← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 109

Sashe 4

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🌊🌊🌊🌊🌊
🅿3⃣
🌊🌊🌊
*Q* ara ware idanunta umaimah tayi kan hoton tana kallon mamar shi mahabeer d'in, wnda kowa ya gnta kuwa yasan tabbas itace dai mamarsa sbd kamarsu d'aya sak,
Sannan ga kuma ita wannan dattijuwar matar da akace ita ta kawosa a gefen mamar MAHABEER d'in suna dariya aka d'auki photon. Maganar da taji mu'azzam sarakin na cewa ne yasa hankalinta dawowa wajen kacokam!
"To shiknn mlm mukhtar bakomi, Allah shi kaimu lokacin da rai da lpia kuma,
ay kasan shi cika alq'awali abune muhimmin gaske a dukkan rayuwar d'an Adam."
Nan mu'azzam sarakin dai ya cike file d'in da shi mlm mukhtar d'in ya basa ya ciken,
da kuma dai sauran abubuwan daya kamata yayin duk yayi su lokacin gaba d'aya,
Sannan da zasu tafi kuma ya cikasu da kyaututtuka suda kingin marayun gidan,
A lokacin kuma suka kamo hnya suka dawo gida.
Suna shiga falon gidan kuwa umaimah tayi saurin kar6ar yaron daga hannun Annah tana murmushin murna ta shige d'aki dashi ta goyeshi ram a bayanta ta fito falo tana zagayawa dashi,
shi kuwa sai mutsu mutsu yake yana q'oqarin tura hannunsa a baki ga alama mamansa yake son sha bai ishesa ba.
Annah kuwa sai binta da murmushi kawai take yi,
Sannan Annah d'in ta d'auko wayanta tafara gayawa 'yan uwa da abokan arziq'i haihuwar,
nan da nan kuwa akaita kiran iyayen jaririn ana musu murna sukuma suna amshewa cikin farin ciki.
Ranar kamar umaimah ta zuba ruwa a q'asa tasha Dan murna,
nan mu'azzam ya kirawo family doctor d'in su yace yana so ya siyo masa madarar da yasan ana bawa jinjirai in ruwan nono yaq'i biyawa.
Ba'a d'au tsawon lokaci ba sai gashi kuwa doctor d'in ya kawo madarar katan katan.
shima yai mamakin ganin jinjirin nasu.
Amman kuma da suka fad'a masa abinda suke fad'awa sauran sai ya yarda shima, duba da shi kansa ma yajima rabon sa da garin sai kwanan nan ya dawo sakamakon canjin wajen aiki daya samu.
Nan aka had'awa baby milk d'insa,
ita ya wuni sha abinsa.
Washe Gari kuwa abokanan umaimah sukaita zuwa ganin jinjirin kowa ya gnsa sai yayi santin yaron matuq'a.
'Yan katsina suma tun ranar suka fara durowa gidan haihuwar har zuwa ranar suna inda akasha shagali na kece raini kusan sati ana shagalin kuwa bai q'are ba,
Hatta abokanan mu'azzam saraki sukan zo takanas dan ganin jinjirin tareda ajiye masa kyaututtuka masu nauyin gaske.
Gskia kam baby yasamu dukiya ta ban mamaki, shiyasa babansa mu'azzam saraki ya bud'e masa account kawai yana zuba masa kyautarsa daya samu.
Kullum Annah tana tare da MAHABEER itama bacci kawai ke maidata d'akinta dan tana matuq'ar son sa itama sosai.
Haka suke rainon d'an nasu cikin farin ciki har yau gashi yayi wata 6 zuwa lokacin harya karya qafarsa wato ya fara rarrafawa knn abinsa gwanin sha'awa.
A lokacin ne Annah ta koma katsina cike da kewar MAHABEER.
Amman tun zuwan MAHABEER gidan Annah bata d'aukar tsawon lokaci bata zoba gidan d'an nata ba kamar da ba da zasuyi ta fama da ita ma akan tazo sai ta q'iya wai a cewarta jikin tsufa ciwo baison tafiye tafiye...
Shima MAHABEER ya fara sanin Annah shiyasa daya ganta tazo gidan har wani murna yake da zullon son ta d'aukesa Dan ya tantanceta a yanzun shima sosai.
Kullum kyansa q'ara fitowa yake na sak jinin larabawa....
'Yan magana sunce shekara bata gadon shekara yau har MAHABEER ya cika shekara 5,
A lokacin har an sanyasa nusry one a school.
Akwana a tashi har gashi ya gama nusry t primary har ya shiga secondary lokacin.
Allah yai masa brain shiyasa yai suna a school d'in su kowa a frnds d'insa zakaji suna fad'in
Gifted MAHABEER.
Tun su umaimah na zullumin yau ko gobe za'a zo d'aukar MAHABEER har suka daina dn ganin an Shari wad'annan shekarun haka Amman kuma shiru kukeji .
Kulawa kuwa ta fannin iyayensa kullum sai abinda yaci gaba kuwa takai yanzun in dai ya samu Hutu shida kansa yake matsawa dadynsa yakaisa katsina wajen Annah Hutu.
Haka zasu tafi kuwa su kaisa shida momynsa umaimah....

Haka lokaci yaketa tafiya kwanaki na zama shekara har gashi yau MAHABEER yayi degree d'insa da masters degree yagama duka.
A lokacin kuma ne
Ya zama wani irin murd'adden mutum q'arfaffa, wato irin giant d'innan ne,
ya ida riked'ewa ya zama hands some guy wani muskilin mutum naq'in q'arin kansa, d'an shekara 29.
A cikin satinne kuma mu'azzam saraki ya tursasa masa fara zuwa office d'insa dashi yayi murabus a kan kujerarsa ya d'ora MAHABEER akai a cewarsa yanzu ba kamar daba, ayyukan zasuyi masa yawa, q'wamma ya tsaya kan fita q'asashen wajen sa yana fiddo da kayan business d'insa abun zai zamo masa da sauq'i hatta al'amurran gidajen man sa da motocinsa na company dinsa ya damqa ragamar komi ga MAHABEER d'in,
Giant man knn,
nera kamar tai masa kuka ga kyaun usuli,...
'Yan mata kuwa komin nacensu garesa jin kansa da isarsa bazai ta6a iya bari ya d'aga kai ya dubesu ba, muddin bashine yaso ba dan Karin kansa ba.
**
Yau dai a matuq'ar gajiye MAHABEER ya dawo gida,
Parking motarsa yayi sannan ya sa6o labcote d'insa da brife case d'insa, fuskar nan a had'e ya tura q'ofar falon nasu ya shiga.
Ganin saman q'ofar dak'in ammi d'insa a rufe ya tabbatar masa da tana hospital d'in datace masa zataje ganin diyar q'awarta nahnah.
D'akin sa ya wuce ya tulla kayan hannun nasa kan gado sannan ya cire kayan jikinsa ya d'aura towel iya q'ugunsa ya shige toilet.
Yana fitowa kuwa yaji phone d'insa ta fara ringing a d'an duban harara ya kallo wayar dan baison wani Abu ya gitto ynxu ya damesa a ynda yakejin ya gajinnan over,
Wayar ya d'auko ya duba ganin sunan bash ne yasa shi d'an sakin fuskarsa kad'an shima, sannan ya d'aga yace
"yadai bash kun dawo ne?
Daga can bangaren bash yace
"kai gifted wlh mukhtar d'an iska ne,
yau rabon iv d'in nan na bikinsa da mu kaje nida mas'ud ba q'aramar wahalar damu yayi ba harda imran,
tun safe fa sai ynxun ana magrib muka dawo gida ,
Kai kai kai huhhh,!
Rabon iv ko masifa,
Shiyasa Nace masa
wlh gobe weekend dole ka fito dan a ida rabon nan dakai kaima kaji ynda abun yake inda gobe shine last day na rabon iv d'in.
Ta6e lips yayi yace
"ba inda zanje guys dan kuma sani,
Ni gobe ma KT zanje na dauko Annah ta,
Da sauri bash yace
"kai Dan Allah gifted?
You seriously?
Indai haka ne nima zanje kuwa ka jirani zan zo to muje dan nayi missing Annah wlh a lot nima, Amman Allah sadai ba jirgi zamu hauba?
Dan na sanka kamar tsuntsu kake wajen yawo a Sama."
ta6e lips ya sakeyi yi dan gajiya da yayi d mgnr sannan yace "don't mind bash,
a motor zamu indai zaka, but kuma wlh karkamun iskan cinka na lates African time, dan by ten i think zamu wuce ma ok?."
"OK babu ji ay gifted"
Cewar bash d'in.
Ajiye wayar yayi ya ida goge sauran leman ruwan jikinsa da towel d'in kansa, sannan ya murza sansanyen cream lotions d'insa ya fiddo wata baq'ar Riga irin ta shan iska mai gajeran hannu,
inda ta bayyana masa kwantaccen gashin jikinsa lu6 lu6 gwanin sha'awa. sannan ya zura tree quater d'insa blue shi kuma, fita yayi izuwa kan dining table nan ya iske fried rice wacce Tasha kayan q'amshi, baje baje take da kifi sosai, dama haka yake son ganin fried rice, shiyasa abinda Momy d'insa tafi girka masa knn dan tasan shine choice cook nashi a rayuwa.
Sam baya wasa da cikinsa shiyasa daya zauna sosai yaci abincin sannan yaje yai brush ya nufi wajen games d'insa inda yake motsa jiki nan wajen harabar gidan,
qaton d'aki ne babu abinda ke cikinsa sai kayan exercise a ciki manya da q'ananu an zube su a cikinsa.
Yakai one hour yana exercise a wajaje daban daban na wurin, yayi gudu ya d'aga q'arfe q'aton gaske da hannayen mabanbanta, yayi ta rubda ciki, yayi ta duq'e,
shiyasa lokaci d'aya wani irin mugun gumi ya jiq'esa sharkaf kamar Wanda ya fito cikin ruwa dudda esin dake wajen Sama da guda 5 kuma.
Saida yaji ya gamsu yaji dud wata sauran gajiyar daya kwaso ta ware sannan ya fito yana share zufa a saman fuskarsa da jikinsa da farin towel d'insa,
Nan ya fito ya koma cikin swimming pool yayi iyo nan ma sosai son ransa sannan ya koma d'akin sa ya canzo wasu q'ananun kayan farin jeans da farar Riga mai gajeran hannu Wanda ta bayyana Masa shatin murd'a murd'an qarfin arms d'insa na maji qarfin qarfaffen namijin gsk, yazari keys d'in motar sa ya fito yana shirin shiga motarsa knn yaga shigowr motar mamynsa a gidan.
Da sauri ya nufi wajen cikin takunsa a sassarfa na son ganin momyn tasa.
Amman lokaci d'aya ya tsaya cak dan ganin wacce suke tare da ita a gefenta.
Tuni ya q'ara d'aure d'aurarriyar fuskarsa katamau.
ita kuwa Hannat sai wani fari take masa da idanunta tana karye karye,
Wani dogon tsoki yaja yayi kamar bai gama momyn ba yana shirin kwana ya shige motarsa yaji momyn tasa tace
''ah MAHABEER_? baka ga momyn taka bane ba? ba welcome ba komi alhalin da katafo kuma saika juya?
A hankali ya juyo ya sauke zafafan idanunsa a....

Xayyneb💤💤
🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb 💤💤

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.
Chapter 4 · 0% Book details