← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 109

Sashe 13

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

🌊🌊🌊🌊🌊
🅿1⃣3⃣
🌊🌊🌊
*A* mman a zucuyarsa yana fad'in "nooo annah,,
kin fad'a dai ne kawai, inajin ko bleesing bazan mata wannan bautar ba bare wata cen daban kuma,,,
shine yayi driving dinsu dady muazzam na masa kwatancen inda zasu samowa annah yad'iyan, a haka har suka isa wajen kuwa.
shi abinma ya basa mamaki sosai ynda yaga jama'a wajen a sosai kamar da rana anata siyen ganye kala kala Hadda tuwo na kowane irin tsiron hatsi kakeso tofa akwaisa wajen,,
a haka suka siyo suka dawo gida.
dakinsa ya shige ya rage kayan jikinsa ya wuce toilet ya watsa ruwa sannan ya fito ya shirya yayi kwanciyarsa tareda jawo wayarsa, wacce tun shigowar sa dakin yaji qarar shigowar messege a phone d'in sai ynxu ya bude ya karanta,,
tsoki yaja tareda yamutse d'aurarriyar fuskarsa na ganin saqon daga hannat ne,,,
yarasa gane mike damun 'yan matan yanzu wai ma dai?
qiri qiri ba kunya zasu fad'a maka suna sonka kamar dai yanda itan ta rubuto masa yanzun fa.
yanajin babu yarinyar da sauran mutuncinta zaiyi saura a ransa muddun yaga ta furtawa wani hakan da bakinta bare mashi kankat kenn.
kwanciyar sa yayi haknali kwance ba damuwar komi a ransa kota kan wayar ma bai qara biba,,,.
Washe gari asabar dady mu'azzam saraki ya sauko daga samansa a shirye cikin shigarsa ta girma. haka itama momy umaima take a shirye wanda daka gnta kaga cewan eh yess matar manya ce itan ba kwano kwano tundaga suturar jikinta da sauran ma kayan jikinta, fuskar nan tata a sake tk ga fara'a, mata mai tsabar mutunta jama'a komin talaucinka kuwa zata tsaya ta saurareka bawai dole sai irinsu ba,, wato masu hali? nooo,, ita kowa nata ne,,,
tana gefen mijinta
a tare suna saukowa suna fira suna dariya abinsu gwanin sha'awa.
a haka har suka shiga dakin annah.
suka gaisheta.
anan ne kuma shi dady mu'azzam sarakin ke fadawa annah inda yakeson zuwa dan temakawa mutanen da matsalar ta samesu ata bngaren rasa muhallai dakuma lpia, kamar dai yanda suka saban,,,
annah tace ''ayya Allah sarki,, Allah dai shi yi maka albarka ya qara bude na alheri,,
kaje kana tare da sa'a cikin rayuwa insha Allah"
"ameeen ameen annah 2, sai mun dawo to,
"annah ko zamuje ne tare dake kema dai yau?,
a cewar mommy umaima tana murmushi.
girgiza kai annah tayi tace "a'a kuje kudai,
dai Allan mai doku lpia ni zan sanya lalle ne a zunguru na,
dan ga hannayena shauran lallen ya kusa ficewa shiyasa,
tun fa wanda kika daura mun ne wancen zuwan,,,
Umaimah tayi saurin dawowa ta zauna tace "kawo na sanya miki to annah in yaso ni saina zauna nuree sai suje tareda da mahabeer ko?,
annah tace a'a baza'ayi haka ba, inda dai kun saba zuwa ku ukun dud ranar weekend to yanzun ma kuwa hakan zakuje,
kutafi ba komi ni zan sanya da kaina Allah shiyi albarka dai, umaimah kema Allah kawo miki rabon ki a duniya, dan har abadan bazan bar yi miki addu'a ba kema na ganin rabonki a duniya nan a,,,,,,,
Shiru annah tayi ganin shigowar mahabeer cikin dakin a shigarsa da yafiyi ta qananun kaya,, wannan karon farar rigace yasa da farin wando jeans,
a saman rigar ya dora wata iriyar baqar riga mai dogon hannu iya zuw wajen belt dinsa baqi, sai ya nannad'e hannayen rigar duka, wanda hakan yabawa kwantaccen baqin gashin hannayen sa fitowa shar a farar fatar jikinsa gwanin sha'awa, ga black watch dinsa nan qirar diamon sai daukan ido yakeyi wnda bayyana kud'in sa 6ata lokaci ne a wajen fad'a ma, hakama cover shoes dinsa da farar sock nasa.
tako ina mahabeer baida makusa, a tsaye yake q'arfaffan namijin gaske,,,
amman kunnen sa yaso ya dauko masa mgnr da annah tayi ta qarshe,, wnda tacewa mommy tasa ta samu rabonta? to shi dai a iya saninsa basu nemi wani abu suka rasa ba a rayuwa, tako ina Allah ya fad'ada musu gashi har suna bayarwa suma amman har ace momy na nemn wani abun kuma ta rasa a live ? to miye shi abun?
d'aga kafafarsa yayi tareda dan d'age gira d'an kasa gano amsar da zuciyar sa keda buqatar sani amman bata sani ba, share zancen yayi kawai yana mai q'ara gyara blueetooth d'in kunnen sa a tym d'in daya ida shigowa tsakiyan dakin duka.
sai yaga suma sun da sha jininsun kuma sunyi shuru da mgnr da sukeyi kafin ya shigo suna kallonsa da murmushi kamar basune suke mgnn samun rabo ba ynxun.
bayan ya isa wajen su dady mu'azzam d'in ya miq'a masa hannu shima dadyn ya miq'a masa suka jinjina a tare sannan ya d'an kwanto a smn jikin dady d'in yace "morning dady,, hope you wake well dady ?,,,
dan bubbuga bayan sa dadyn yayi yace
"I'm fine my lovely son,ina fatan kaima ka tashi lpia?
Yeah iam 5n like yhu my dady"
rabuwa yayi da jikin dadyn yaje kan cinyar momy umaimah ya daura kansa yana fadin "morning sweet momy?,,
dafa kansa tayi tana qoqarin boye fuskarta daga garesa dan perfume d'in daya sanya tanajin kamar yanason sata amayar da abinda taci dudda dadin qamshinsa kuwa.
cikin dabara ta amsa gaisuwar tasa tareda tashi tsaye tace zataje dauko jakarta data mnto ta a saman bed nata.
da sauri ta fice shikuma ya maida kansa a cinyar annah yana fad'in
"yadai matar kin farka lpia kema dai ko?,
Harararsa annah tayi tace " to da ban tashi ba daka ganni?
kaini wannan auren ma inajin fasashi zanyi ace mutum kullum fuskar mijinka gim a d'aure sai kayi sa'a sannan zai sakar maka ita?
Inaaaa bada niba to,,
qara langwa6e kansa yayi yace
"ohhhh kaga wannan tshohuwar?
to ai fara'ar zuwa takeyi ko annah ta?
ya fad'a hakan tareda watsa hannayensa yana ta6e pink lips dinsa alamun hakan ko a jikinsa.
tace "kai tafi can ni bani waje,, sai kaita zama ay har sai sakin fuskar yazo ya isheka sannan ka saketan inda ba tare kk da kayan kaba daman,,
wani irin murmushi yasaki yana mai qara gyara kwanciyar kansa a cinyar annah batareda yace komi ba.
dariya kawai dady mu'azzam ke musu yana fad'in
"ah mudai annah/'yan bada haquri ne dn wannan auren kam naku mutu ka raba keda mahabeer dinki annah, hmm wanda dmn sabo da shine muka samu ake jimawa mamu anan ba'a koma gida katsina ba,,. mahabeer yace "yesss dady na,,, da sannu ma saina maido muku da ita nan duka,,,
a lokacin mommy umaimah ta dawo d'akin tana cewa "dakuwa munji dadi mahabeer na muddin kuwa kai mana wannan qoqarin.
dariya sukayi dukansu yayinda mahabeer yayi wani 6oyayyen murmushi kawai abinsa shi,,,.
a haka suka fito nan haraban gidan suka shiga mota dady mua'zzam na gefe yayinda mahabeer ke tuqa motar mommy umaimah na baya tana amsa wayar hajiyar hannat akan kayan datace taje london ta siyo ko za'a kawo matasu ynxun tagani ,,,
anan momy umaimah take fad'a mata zasuje anguwa ne ynxun bata nan,
acan bangaren hajiyar hannat d'in ke cewa to shiknn inta dawo zata aiko mata hannat ta gwada mata kalar sampur d'in kayan ahaka sukayi bankwana.
saida motarsu ta hau titi sannan mahaber ya dubi dadyn nasa yace
"to dady yau ina zamu fara zuwa ne? muazzam saraki ya dago daga duba daily trust dinsa dayakeyi yanamai qara gyara zaman gilashin fuskarsa yace "yau dai inaga mufara zuwa can nursing home
(wato barau dukko hospital)
ta yanki cikin gari son"
"to dady"
daga haka yayi shuru bai sake cewa komi ba ya maida kansa ga tuqin sosai,,, saima qara wa motar speed da yayi suka dauki hanyar asibitin ,,,,,,
[10/11, 2:45 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb💤💤

🌊🌊🌊🌊🌊
Fasaha online writers f.o.w.
Chapter 13 · 0% Book details