← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 109

Sashe 48

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*🌏impacting valuable knowledge and Entertainment is our concern🤝🏻*. 🌊🌊🌊🌊🌊 🅿3⃣7⃣ 🌊🌊🌊 Haisam kuwa da idanuwa ya tsare ummu hani yana mai sake jifanta da murmushi, cikin murmushi yace"nasan zakuce wannan mutumin ya fiye naci ko? alhalin tun daga hnya nike biye daku,, nabeela tace "dan Allah mlm kayi haquri tun can mun fad'a maka ba'a barinmu fira a gida saboda karatun mu da muke, amman bn san miyasa kaqi ganewa ba kuma??? Sakin ajiyar zuciya yayi yayinda ya dubi nabeela yace "wlh 'yar uwa bakomi ne ya kawoni nan ba sai wannan qawar taki nikeda burin samu ta zama mallakina uwar yarana in har zaku bani it..... ganin mahabeer tsaye a gabansu kamar an tullosa sai mazurai yake ran sa a 6ace yake matuqa zuciyar sa na masa wani iriyar duka dum!! dum!! dum!! wanda shi kansa bazaice ga reason na abinda yasashi hakan ba sam sam. "bakuwa a gidan nan ba to!!,, amsar da ya bawa hisham kenan yana watsa masa wani mugun hayataccen kallo,, nuna ummu hani yayi da yatsa yace "wannan da kake gani bawai tazo nan gidan bane da niyyar zama, ba madawwamiya bace bauta tazoyi, dan haka saika bari can inta koma garinsu saika bita can kuyi dud abinda zakuyin bawai a nan ba kagane? Then kasani kuma gidannan yanada tsari da doka na shigowa bawai kowa ne time zakuna ta shigowa mutane a gida ba dan haka be careful mlm ok??" yayi maganar idanunsa har sun qara yin wani jan akan nada. cikin sanyin jiki hisham ke kallonsa sarai yasan shine matashin saurayin nan d'an mua'zzam saraki wanda duniya tajima da saninsa, to amman miyasa yake masa wannan maganganun cikin zafi haka alhalin yasan ba halinsa bane wulaqanta mutane,, kallon tsakar idanunsa hisham yayi sosai ganin ynda suka rikede lokaci day'a ne yasashi had'a hannuwansa biyu yace ''afuwan,,, yalla6ai naji bayanan ka kuma ngd, amman kamar dawane lokaci ne zata bar nn din dan in tantance??" cikin tsawa mai qaraji mahabeer yace "nace ban sani ba ko?! kaga mlm ban son sake jin wani magana naka nace kumaka ba'cen da gani tun kan nasa a min ploshing dinka waje kaida wanan qwaman motar naka, mtsss daga gani kune masu hurewa yaran Mutane kunnen su." ba shiri hisham yaja motarsa ya bata wuta dan baisan mai zai biyo baya ba muddin ran mahabeer mua'zzam ya qara hauhawa da sunan b'aci kuma,, sai lokacin ya juyo yaga su ummu hani suna nan tsaye sun zuba musu ido cikeda mamakin yanda yaketa faman balbale bawan Allah da kalar masifarsa,, Kansu yanufo azafafe yace "kungs 'yan iskan yara ubanmi kuka tsaya nan kuna kallo kuma??! zan karya yarinya qil wlh na watsar anan inba kubar nan ba" yana maganar ne yana zaro belt daga jeans dinsa. habawa tuni suka ranka yana kare, qafa minaci ban baki cikin ba sai cikin gida,, tsoki yaja tareda maida belt dinsa a qugunsa ya dawo ya zauna bash dudda yace bazai qara shiga sha'anin su ba amman saida yace "yazakayi haka kuma gifted?? yaya mutum yazo wajen yarinya ka hanata kulasa? fisabililla inkai akai mawa zakaji dad'i? "wazaije din bare ai mai?? saika bari sai naje din in anmun sannan zan tantance da zafi koko babu"! daga nan banza mahabeer yai masa ya d'auki magazine dinsa ya cigaba da dubawa bayan ya d'ora q'afa d'aya bisa d'aya akan tebur d'in gabansu yana karkad'awa. mukhtar yace "qyale dan iska qilan shi zai aureta inda gashi yana hanata kula samari ay, ni wlh dazaka taimaka da kabani ita na qara,,, katsesa mahabeer yayi cikin tsawa da cewa ''ubanmi zanyi da wannan 'yar qauyen yarinyar? mizan lalumo jikinta d'an iska bare har kaimun fatan aurenta? bazan aureta ba kuma kaima wlh baka isa ka kulata ina cikin gidan nan ba muddin kuwa ka kuskura kayi hakan kuwa wlh saina b'ata ma idanu d'an iskan q'arya kawai, namamajo dakai, to wlh kayi Kad'an kasa class d'nnmu ya zube wajen wannan yar qauyen buzuwar yarinyar". Yana gama fad'in haka ya tashi ya barsu nan suna binsa da kallon mamaki dan gaba day'a sun rasa gane masa kam,,,, yaqi taunawa kuma yaqi haduwa??,, dole tasa suma sai tashi sukayi suka shige motocinsu kowa ya kama gabansa cikeda tunanin murd'adden hali irin na mahabeer mua'zzam saraki. Shikuwa ko gidan nasu ma bai shiga ba yayi shigewarsa gidansu momy ni'ima yai kwanciyarsa a falo dayake bata nan. haka ya kwanta tareda rufe idanunsa duka zuciyar sa na masa ba dad'i yakeji wanda yarasa dalilin faruwar hakan a kansa? amman shidai ya jingina hakan da irin b'acin ran da yaran suka sasa ne na shigo masu da qato cikin gida kuma suka tsaya dashi a gaban abokansa dan raini. su kuwa da gudu suka fad'a falon gidan suna haki tareda maida numfashi sama sama,, annah dake zaune a falo ganin sun shigo a hargitse yasata saurin miqewa tsaye tana fad'in "kai lpian ku lau kuwa? waye ya biyoku haka sai kace masu gudun ceton rai eye?,,, cikin muryar shassheqa nabeela tace "ai dole muyo gudun ceton bugun wahala anna daga garesa, annah tace "ban gane ba daga ina kuma,,? nan nabeela ta fada mata dud abunda ya faru duka ,, salati annah ta hauyi da sallallami tana tafa hannayenta tace ''ni 'yasu wannan yaro wannan yaro anya kuwa kansa lau yake kuwa?? baidai doke ku ba dai ko? cewar momy umaima datake fitowa daga dakinta tana dariya,, turo baki ummu hani tayi tace "mah shine ke dariyar ma kike mana ko? "to ummu hani na ai dole nayi dariya domin ynxu abun naku wlh dariya yake bani, kudai dakun hadu sai kunyi rigima kamar mage da b'era? tsoki annah taja tai wucewarta d'aka tana cewa "babu mai laifin ai sai wannan taqadarin ja'irin yaron ai, Murmushi momy umaima tayi ta dubesu tace "kubar zancen haka yarana kuyi haquri kuje kuyi wanka ku fito ga d'anwake nan da tasshi nan nai mana kuyi maza maza ku sauko muci kunji ko, da sauri suka amsa mata sukayi sama kuwa dansu na matuqar qaunar danwake dayaji mai man gyad'a. Mahabeer kuwa yana cen har Momy ni'ima ta dawo sukayita fira abinsu musamman ta q'wallo ma, dayake team dinsu daya da Momy ni'ima, itama real Madrid take shiyasa mahabeer yaji dad'in firar yasaki jikinsa sosai harda dora kansa a qafan momy ni'ima suna firansu dan yanzu yana shiga gidan shima sosai shiyasa suka saba da Momy ni'ima. son matar yake har ransa in suna tare sam baison matsawa daga gareta musamman yanda take nusar dashi tserewa qyale qyalen duniya da sake jajircewa kan temakon mabuqata bayin Allah,, ga hadissai na manzo masu dad'i datake karanto masa yana sake qaruwa dasu sosai. baibar gidan ba saida akayi magrib sannan ya wuce masallaci. ahaka watan haihuwar momy umaima ya tsaya dud wata siyayya sunyota sun ajiye,, ranar wata laraba da safe ciwon naquda ya tasowa momy umaimah babu shiri sukayi asibiti nan kuwa aka shiga da ita labour room,, doguwar naquda tayi sosai daga mahabeer har dadynsa masallaci suka shiga anan ckn asibitin sunawa momy umaima addu'ar samun sauqin naq'uda, cikin ikon Allah kuwa sai gashi ta haifi d'iyarta mace masha Allah,, daga momy umaima har mua'zzam saraki kuka kawai suke na farin ciki na ashe zasuga qwansu na gaskia a duniya?,, annah ceke rarrashinsu akan suyu shiru kada yaran su ankare da halinda suke ciki. haka suka dawo gida bayan dubata da akayi sosai akaga komi normal babu wata matsala. ummu hani takasa zaune ta kasa tsaye tunda suka dawo asibiti tana nan q'waqume da jaririyar nan kowa yace tabasa sai anyi da gaske sannan take bayarwa, har annah na mata tsiyar cewa "anya kuwa ummu hani in kika samu d'a bayan kinyi aure zaki dinga bari ana d'auknsa kuwa? dan na lura kinada son jarirai,,nabeela tayi karaf tace "nima ay annah bazan bawa kowa nawa ba kada asa masa ciwon jiki,,," annah takama baki tace "oni 'yasu dunyia ta canza yaran zamani ba kunya har kuna cewa bazaku bada yaranku ba?? ai da gudu suka tashi suka bar d'akin. momy ni'ima da Momy umaimah sunata musu dariya. kan kwana 3 dud 'yan katsina sun cika gidan kuwa anata zaman barka da Allah raya,,, ranar suna kuwa anyi shagali sosai sosai yarinya taci sunsn manal. bayan suna ne 'yan katsins suka koma da d'umbin tago mashi na arziqi. Beby manal samun kulawa take daga kowane b'angare kuwa na gidan, kowa son d'aukarta yake dan yarinya ce mai shiga rai, a haka har suka shiga wata na 4 da haihuwa. lokacin baby manal ta fara wayau hatta mamanta wani sa'in qyuya take son yi mata muddin tana hannun sabuwar ummu mmnta hani,,, kamar yau ta kama alhamis da misalin qarfe hudu na yamma momy umaima ta shiga d'aki ta samu barci ummu hani kuwa tana riq'e da baby manal suna zagaya falon tana mata wasa yarinyar na wangle mata baki, zama tayi tareda fiddo wayarta tana qoqarin kiran nabeela taji ko ta dawo daga kasuwar dataje kaiwa a dinko musu rigunan nan na roba dogaye masu gyale. sai kawai ganin saukowar sa daga saman benen dakinsa tayi da sauri da laptop a hannunsa yana q'wallawa annah da momy kira amman ysai shuru,, zubewa yayi bisa kujera yana sakin ajiyar zuciya babu abinda ke cinsa sai tsabar murna da farinciki domin school din London wacce yayi request na son shigarta a kwanakin baya shine yanzu yana dubawa a laptop dinsa yaga sun yi accepting nasa, kuma sunce a wannan watan sukeso yazo sabida sufara project dunsu. Murmushi kawai yake saki umnu hani kuwa kallonsa takeyi dan abun mamaki ya bata, ita dan bata taba ganin zallar farin ciki irin nasa ba kamar na yau tun byn haihuwar baby manal. tab'e lips tayi gamida jan tsoki, karaff kuwa sai a kunnensa kuwa. da sauri ya d'ago tareda ware idanunsa dukkansu a kanta ya dubeta tareda watsa mata harara da idanunsa cikin masifarsa yace "ke wane shegen kike wa tsoki??" Murgud'a d'an bakinta tayi tace ''yo kajini da mlm, koko kaji nace dakai nike abina ne bare?? waro idanuwa yayi waje tareda fad'in ''kutttt,,..ke?? ubanwa kika raina wa wayau ne wai ma.....?? Miqewa tsaye taga yayi yana shirin nufota, haba aida gudu ta sungumi baby manal a kafada tayi dakin
Chapter 48 · 0% Book details