← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 109

Sashe 26

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*Xexen Fasaha*✍🏻
[10/11, 2:46 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊

Story and writing
by
Xayyneb 💤💤

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.

🌊🌊🌊🌊🌊
🅿2⃣5⃣.
🌊🌊🌊
A cikin toilet kuwa ummu hani tsananin tsari na cikin toilet d'in ya dauke mata hankali taita bin ko ina da kallo harda ta6awa take ma wani lokacin,,, qarshe dai haqura tayi ta yo wankan ta fito daureda baqin gyalenta babba na kayaynta,,cikin sauri sauri ta dauki rigar datagani wacce tasan itace mah tace ta sanya inta fito ta zura gudun kada wani ya fado cikin dakin yasata ko mai bata tsaya shafawa ba a jikinta,,,
Subhanalla ,,lokacin data zura wannan rigar yanda kasan jikinta aka dinka,,ba qaramin kyau tayi mata ba, ta dan matsa jikin mudubin dake dakin ta kalli fuskarta tayi haske sosai lips d'in nan nata kamar ta shafa musu pink d'in janbaki a hankali tayita bin jikinta da kallo,, ita kanta tasan ta d'an fad'a ta rame sa6anin yanda tazo garin daga garinsu,,
sauke idanunta tayi a q'irjinta da tudunsu yasa har suka dago kwalliyar gaban rigar gaba dayan su yanda kasan tasa foshop amman ba ita bace bra ce normal kawai a jikinta mara soso ma,,, hakama wugunta taga rigar ta fiddo mata shop dinsu gaba daya wanda hakan yabawa shafaffen cikinta fito da nasa kalar shape d'in shima,,,
sauke ajiyar zuciya tayi ta miqe tsaye tareda ware gyalan kayan da nufin ta yafa ta fita can wajen mah d'in dan batasan ko akwai aikin da zai matan ba,, tana gama ware gyalan ta gansa dan firut a hannunta.. Saroro tayi ta na mai bin gyalen da kallo cikin mamaki,,,yanzu ana nufin da wannan dan fingilin gyalen zata fito? "kammmm tabbbb d'i jammm wai,, ,,
abinda ummu tace knn tana mai qara fiddo fararen idanunta waje dan ita kanta tasan wannan gyalen bazai iya saya mata halittar taba da wannan rigar ta fiddo mata su waje,,
daura sa tayi akanta tayi ribom dashi ta hanyar kamo tulin gashin kanta ta qulle dashi da qyar sannan ta tuqe ta saki jelar tana reto a bayanta har wajen bombom nata,, sannan ta dauko mayafinta wanda iskar dakin ta ec tuni ta busar dashi ta yafa abinta bisa kai har ya sauko mata iya tsawon hannayenta sannan taji tayi dai dai,, falon ta nufa lokacin momy umaima harta dawo falon ta zauna tana jiran fitowarta,,dama tayi saurin fitowa ne dan gudun kada ummu d'in ta fito falon ta rasa inda zata ganta dan falon babba ne sosai,,,
da Oyoyo diyata momy umaima ta taro ummu tareda zaunar da ita gefenta ita kuwa ummu hani Murmushi kawai takeyi itama kamar yanda momy umaima take yi itama,,,, gskia kan Allah mai had'a so tsakanin bayinsa ita kanta ummu hani ya zuwa yanxu tana alfahari da mah d'in nata sosai sosai kamar yanda ta dauketa itama,,,
"kinyi kyau diyata sosai,,, cewar momy umaimah tana 'yar dariya, ummu kuwa cikin kunya tace"mah mi zaayi miki ne yanzu na aiki sai nayi miki? "
"aa diyata bari sai kin qara hutawa sosai kinga azumi kukeyi yau amman zo muje kichen na dan fara gwargwada miki yanda zaki yi amfani da electronics na cikinsa,,,,
haka ta kama hannun ummu hani suka shiga kichen d'in wanda yake qaton gaske shima cikeda kayan amfani nan taita gwargwada mata yanda abubuwan suke dayake ummu nada brain na saurin daukan abu koyaya aka koya mata shi shiyasa nan da nan ta fahimci yanda abubuwan suke,, sun jima a kichen d'in sosai dan har har Friedrich momy umaima ta had'a mahabeer d'in nata a gabanta dan tasan Yana kusa da dawowa office mafarin knn ta jefi tsuntsu biyu da dutse daya wato tayi masa girki kuma ummu ta ga yanda ta had'a komin ta,, mafarin knn ta yanke a zuciyar ta kullum zata shiga kichen tofa zasu shiga tare ta rinqa wayar da ita wasu abubuwan da dama danta kula yarinyar nada fahimtar ta,, sai wajen biyar da rabi sannan suka baro kichen tasake jan ummu suka nufi dakin annah wacce ke zaune tana lazumi da carbinta,,
Zama momy umaima tayi itama umnu ta zauna a qasa tasake gaisheda da annah cikin faraa annah ta amsa da fad'in ummu yaya kikaji gidan namu da baqunta ko?
cikin Murmushi ummu tace
"a'a annah"
Murmushi momy umaima tayi tacet"kamar kuwa kin sani annah har yanzu ummu taqi sakin jikinta fa,,, annah cikin sake qaruwar fara'arta tace "zata canza umaima indai tana zaune wajenki,,dariya sukayi tace "hakane annah wlh bnson miyasa ummu tashiga raina haka ba cewar umaima Tana mai kamo hannun ummu d'in,
Annah tace "nima ta burgeni umaima tun sa'ilim da yaron nan yai mata karo Wlh bata nuna bacin ranta ba dudda kayen da tayi qasa sosai,,,
bakomi annan ai haka akeson nutum mai juriya akan kowane abu na rayuwa zakaci riba in kai hakan inji umaima sannan ta qara da cewa"amm annah mi zan girka muku ne na buda baki naga kunada sauran awa d'aya da rabi kan ayi kiran salla,,Anna ta riqe baki sannan tace"a'a umaimtu ya daga dawowar ki daga asibiti jinya zaki koma kichen kuma aiki?
haba haba ki barsa kawai na gode ita ummu dai ta girka nata taci ita,,,
"A'a wlh annah yanzu banjin sauran kowane irin ciwo a jikina yanzun haka ma tun d'azun muna kichen nida ummu ina gwargwada mata wasu abubuwan harma girki nayiwa mahabeer,, "lail'ahaillla ke yarinyar nan da gaske? Yanzu dawowar ki har kika iya shiga madafi kiyiwa wannan tuzurun mijin nawa abinci kina fama?
"Hyyyy my swwet kakus na,,, cewar mahabeer da dawowar sa knn daga office briefcase dinsa ma tana sagale a kafadansa kot dinsa tana riqe da hannunsa sai 'yar farar rigar dake jikinsa da lakatayig din wuyansa ya qaraso wajen ya zauna tareda fad'in "washh ya jinginar da bayansa jikin momy umaima ya saki dan guntun Murmushi sannan yace''huhhhh momy wlh yau tunda naje office ban samu kaina ba sai ynzu,, annah ta dubesa a cogane tace "to wani ne ya hanaka zuwa aikin kwana 2 bare kazo kana cika mana kunnne aiki aiki,,, yamutsa fuskarsa yayi yace "haba annah ta jinya fa na taya momy na asibiti to ina ni ina zuwa wani office dan Allah,, ni kinga bafama dake nake magana ta ba tsohuwar nan kiyi shirunki zaifi,, "naqiyi nayi shirin koko zakasa zare ne da allurai ka dinke mun baki eye??
Wata 'yar siririyar dariya yasaki yana fad'in calm down my kakus maida wuqar irin Dan wasan nan nefa na jika da kaka..... maganars sauranta sai dai yaji ta laqafe masa a tsakan kanin lips dinsa sakamakon arba da yayi da ummu hani zaune daga dayan gefen da momy umaima take tana kallonsa,,,wata iriyar harara watsowa saitin wajen da take baisan sanda ya miqe tsaye ba tareda watsi da kayan hannunsa ya nunata da yatsansa na tsakiya yana magana bakinsa na rawa rawa dan har a cikin ransa yaji ransa ya 6aci na sake gamdakatar da tayi da yarinyar kuma wannan karon har a cikin ma mainhouse dinsu kuma a dakin kakarsa ma abin sonsa kullum farin cikinsa da ahalinsa suyi wasa da dariya abinsu da kakarsa gefe ga momynsa na tare masa shine kuma zasu jajibo musu wanan fitsararriyar yarinyar a gida salon ta qara ganin wallensa tasamu hnyar qara raunsasa abinda ya tsana knn kuma raini,, shiyasa kulum annah take fada akan sai yaita faman Kama rai yana dauresa ita batasan natural haka yake ba abin a jininsa ya taso,,, sake daure fuska yayi katamau sannan yasamu damar cewa "annah waimi ke kawo yarinyar nan cikin ahalinmu ne dan Allah?
plsss Anna ku sallameta tabar nan gidan mu kadai mun isa mu bawa ahalinmu farinciki bawai sai wasu sun shigo jikin muba,, "
saida ya qarasa maganar sa taz ya tsaya Yana maida numfashi tareda muzurai kowa binsa yake da ido a wajen ummu kuwa dauke fuskar ta tayi daga gefensa aranta kuwa cewa takeyi "oh ni ummu *daga taimako*?? Sai mutum ya zamemun qaya a karo na 2 da sake haduwa tun asibitin?
kuma shine abin yake ta *bibiya akai*???,,,,
wani dan siririn tsoki taja a can qasan ranta sannan tace "wlh dai dai irin kace ni mlm,,, amman kuma fa a tsakaninmu knn, bazan taba gwada wa su mah hakan ba kuma,,, kaida ka siya taqamar nima zan dinga siyar maka da tawa kalan a 6oye a 6oye bayan idanun mutane,,,
d'an fitinar mutum kawai dakai,,,
tayi maganar tareda murguda bakinta,,,
jitayi annah na cewa masa
"em hemm em hem,,to tsohon kakanmu,,kagama bamu umarnin koko da saura ka qarasa muna sauraran ka sosai sosai????
Marairaice fuskarsa yayi yace haba dan AllAh annah ki gane man yarinyar nan sam batta da..... Miye haka mahabeer na? Cewar momy umaimah ranta adan 6ace,, shiru yayi ya kasa furta komi shi knsa yayi mamakin yanda momy umaima ta nuna rashin jin dadinta akan wannan maganar dayayi akan yarinyar,,, wato harma ta fara shiga tsakanin su da su knn?? rabon dayaga sauyin fuskar momyn tasa shi baima iya tunowa amman gashi lokaci data wannan yarinyar ta janyo masa wacce bai dauketa a bakin komi ba sai irin sune masu fitowa daga garuruwansu suna yawon bara a titi titi rareda kwana a titi hankalin su kwance,,,
gyada kai yayi a hankali yaxee
"yi haquri momy,,,
Momy umaimah tace "ba komi mahabeer na wannan itace wacce zata dan dinga taimakamun a wasu ayyukan na gida mafarin zuwan nata knn,,, momy kina nufin 'yar aiki knn?
"a'a mataimakiya dai,, dan ummu ta wuce yar aiki a wajena,,,
wani abu yayi tunani a ransa na cewar lallai kin kawo kanki yarinya zaki gane bakida kunya,,dan da kanki zakibar gidan nan mu zuba ni dake hmmm,,,,
nan da nan ya dan saki fuskarsa yace ohk momy,,
hakanma yayi ay,,, ni zan wuce side dina momy na warwatsa Yana maganar yana yamutsa fuskarsa kamar dole ne aka sashi yinta,,""
hararsa annah tayi tace qafan gaba ta gaida ta baya dai,,,"" ficewarsa yayi yaqi bata amsa,,
girgiza kai momy umaimah tayi sannan tace
"kai ohh mahabeer na Allah shirya myn kai ka cika fitina wlh,,,"
anna tace"hmm kunsan haka knn ma ashe kuke ta sa masa idanu yana tsulan tsiyarsa a cikin gidan nan,,
Murmushi kawai momy umaimah tayi ta kauda zancen da tace
"yanzu annah nasan dai kinason kunun tsamiya da qosai in kin kai azumi bari naje sai na hada miki ko??"
ganin annah na shirin sake musawa yasa momy umaimah tayi saurin tashi ta kamo hannun ummu suka bar dakin suka koma kichen suka fara harhada kayan dazasu aikin dasu suna gama had'a kunun tsamiyar suka rufe cikin samis sannan momy umaimah ta juyo markadadden qullun qosanta daga cikin blander din data gama markadawa sai qamshin tarugu da albasa yake markadan,, nan ta fara soyashi ummu tana tsamewa dud abin nan momy umaimah daurewa zuciyar ta kawai takeyi dan yanda qamshin qosan ke bugunta jitakeyi kamar zata zazzage 'yan hanjin cikinta ne saboda ynda zuciyar nata ke tashi,,,
''ummu cigaba da soyawa zanje falo in dan kwanta dan kaina ciwo yake mun ga kuma juwa unaji,," cewar momy umaimah tana mai miqawa ummu din tsinken juya qosan da matsaminsa,, kar6a tayi tace
"to mah Allah sawaqa"
"Ameeen ummu,,,"
da sauri ta fice ta koma falo ta kwanta sai a lokacin ne tasamu relief na abinda ta keji amman dudda haka ta sanya hankicef a fuskar ta dan tanajin qamshin qosan na mata gizo a hanci,,
"hyy momy na ykk?,,, Allah sa yaya mahabeer yadawo dai daga office ,
dan yau ko zan kwana momy sai naga yaya,,dan na kwana biyu naje wajen dady shiyasa"
hannat knn takeyin maganar bayan ta ajiye ledar kayan da momyn tata ta aikota ta gwada wa momy umaimah din kalar samfir din kayan business din nasu data ce zata ayko ta ta kawo matasu ta gani,,,
Chapter 26 · 0% Book details