Sashe 100
Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
an gaya maka mukhtar din na wasa ne akan abinda yakeso har yasawa rai? saurin canza akalar maganar bash yayi ta hnyar cewa "bari na je cikin gida na zubo mana abunci ko? Mukhatr yace "ok" haka bash yabar dakin farinciki fal zuciyarsa na samun nasarar sa dayayi akan mukhtar, yasan da cewa yayi kai tsaye ya fada masa gskia bazai fada ba amman daya bullo masa ta byn gida dayake shi wawa ne bai ganin tsananin abotarsu da mahabeer ta gskia bazaici amanar sa ba bare yayi tunanin zai zambace saba, amman har shine ya yarda zaici masa amana knn kmr ynda shi yayi da yake ance masa kowa wawa ne kamar sa kenan. koda ya dawo suna cin abuncin haka yaita cigaba da bugun cikin mukhtar shikuwa sai zuba yake raaaaaaaaa raaa zeyyyyyy, sakaran wawan, cikin wayau bash ya hana mukhatar tafiya saida akayi sallar isha'e sannan yace masa yazo su je gano annah bata lpia, yai masa qaryar hakan dan so kawai yake suje gidan dan dubun mukhtar ta cika yau a bainar jama'ar gidan , shikuwa mukhtar harda wani saurin amsawa da "to" dan muradinsa na son ganin ummu hani. haka suka shigo motocinsu har suka iso gidan kowa yayi parking ya fito bash ne gaba mukhtar na biye dashi suna shiga kuwa suka iske dady muazzam zaune a falo shida dady Muhammad wanda suka shigo babu jimawa daga masallaci suma, sai gefe daya annah ce suke zaune ita da momy umaimah suna fira ta 'yan katsina, sun gaishesu su dady suka amsa kan susake cewa wani abu saiga mahabeer shima ya fito daga ckn kicen hannunsa daukeda gorar ruwan swan lokacin kuwa har bash ya miqe ya isa ga tv ya ciro camera dinnan ya jona da tv daga inda yake tsaye ya juyo wajensu dady mua'zzam yace "yau dady zaku fahimci gskiar ainahun wanda ya sakarwa mahabeer matarsa dan zallar cin amana irun tasa nikuma nayi dabarunmu harna hillacesa na zurmasa ya bayyana mun gskiar lamarin nikuma shine nazo nima in bayya na muku domun wanke mahabeer daga zargi dan Allah yanzun ku kallo nan kugani,, mukhtar najin haka tuni cikinsa ya bada wani sauti quuuu qulululu, nan take zufa ta karyo masa lokaci daya ga ctv camera ta nuno sa baro baro yana tonawa kansa asiri,, tunkan su dady su gama kallo suka fahimci *gaskiyar lamari*, salati kawai suke da sallallami ay a guje mukhtr ya miqe tsaye zai gudu dawani mugun tsalle ko mahabeer ya damqosa ya gama kansa da bango yafara dukansa jikinsa na ciri kota ina,, tuni ya tadawa mukhtar idanu da hanci da baki suka tashi himmm sai duknsa yake yana fadin "wlh Allah ya isa mukhtar kaci bazan amanata bazan barka ba saina kasheka daqyar su dady suka jnyesa suna basa haquri mukhtar na ganinsa free tuni ya fesa da mugun gudu waje ya fada motarsa shima mahabeer ya futo ya shiga mota ya fuce tuni su dady mua'zzam suma suka biyosu da motarsu dan shawo kan rigimar data auku, gudu su mahabeer kawai suke fallawa a titi, cikin tsautsayi kuwa motar mukhtar burki ya qwace masa ya yanki gefen daji motar ta dinga gungurawa dashi ta daki wani bishiya sannan ta tsaya cak,, gaba daya hankalin mahabeer naga inda motar mukhtar din yake bai ankaraba yaji ya ingeji abu dasauri ya maido hankalin sa gabansa ganin wata yar dattijuwa ce ya banke ta zube can gefen titi nan a guje ya taka burki dai dai nan su bash da dady mua'zzam da ddy Muhammad suka iso duknsu lokaci daya, mahabeer ya fito da mugun sauri ya nufi matar nan, suma su dady Muhammad suka isa inda motar mukhtar yake daqyar suka zaqulosa qafafu sun kakkarye yakasa takasu sai lilo suke suna reto, sai dai talla talla sukai masa suka sashi a motarsu koma numfashi da qyar yake fuddowa suna sakasa mota suka dawo wajen da mahabeer ke zuqunne gaban tsohuwar wacce dadan kullin kayanta a kallabi sai nishi take sama sannan su dady Muhammad sukace "subhanalla sannu dai baba daqyar ta iya amsawa zaki iya tashi kuwa kasa magana tayi wayar hannun dady mua'zzam ya haska a fuskar tsohuwar domim rashin wadataccen hasken dake wajen sosai hankalin dady Muhammad yayi kan tsohuwar cikin tsananin mamaki da razana yace Innalillahe..inna? wannan ai inna indo ce tshohuwar mai aikina ce wacce muka nema muka rasata tun shekarun baya......