← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 109

Sashe 24

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🌊🌊🌊🌊🌊 🅿2⃣4⃣. 🌊🌊🌊 Maganar Anna ce ta katse ta daga tunanin ta data keyi jitayi tace"eh hakan ma nada kyau sabida mataimaki dad'i ne dashi,,, sauke 6oyayyen ajiyar zuciya ummu hani tayi tirq'ashiii... wanna shine ake cewa ga qoshi ga kuma kwana yunwa,,, abinda itada iyayen ta suke burin samu kenan aikatau amman kuma gashi taji ana cigiyar masu yi tayi shiru,, anya kuwa in taci gaba da shirun nan nata bataso kan taba kuma batai butulci ga Allah ba daya basu komi a sauqaqe batareda shan wuya ba,,,? babban muhimmin abinma ciwon mamanta,, yanzu dud inya sake tasowa mata yaya zatayi knn da rayuwarta??? kada ki bari damar nan datazo miki ummu hani ta kucce miki ki bude baki kiwa bayin Allahn nn jawabi dan samawa mamanki mafita da babanki dakuma ke kanki d'in nan dasamawa mamanki lpia kokwa koma gida kan lokaci,,,,,. hannunta da momy umaima ta riqo ne yasata sauke ajiyar zuciya tareda d'agowa da fararen idanunta ta saukesu a kanta wannan karon cike da qwarin gwiwa,,,, "mikike tunani haka 'yata?? momy umaima tayo mata wannan tambayar cikeda dan nuna kulawarta a kanta,,, a matsayin ta na wacce tazo wajenta taganta a cikin wannan hali haka,,,. dan Murmushi tayi tareda Dan satar kallon momy ni'ima datake zuge zip d'in jikkarta jin wayarta na ringing..... sauke ajiyar zuciya ummu hani tasa keyi a karo na 2 sannan ta maida gaba dayan hankalinta ga momy umaima cikin dan rawa rawan muryarta tafara da cewa "t.. to.. za...zan ma su baffa ...na maganar aikin d kuke mgn akai... daman dai muma munzo garin nan ne neman inda zamu samu aikin yi sai kuma wannan hatsarin ya ritsa damu harya kaimu da zuwa nan asibitin kuma gashi cikin yardan Allah munji kuna cigiyan wanda zasuyi muku aiki nasan baffa na inyaji hakan zaiyi musu aikin shida momma na a gidan,,,"" tana kaiwa nan tayi shiru kanta na qasa dan sauraran amsar tata,, Kafin momy umaima tace wani annah tace "ayya kaga ikon Allah,,, Allah sarki to shiknn Muhammadu kaji ko?,," tayiwa alhj Muhammad magana ya matso sosai dan girmamawa yace "na'am annah" tace "ga shi ana ta maganar nemo masu aiki wa gidan naka da kace kanaso ynxu, to gashi wannan yarinya.....ta danyi shiru sannan ta dubi ummu hani tace "ammm yama sunanki 'yar nan??? ta tambayi ummu hani,,, cikin girmamawa tace "ummu hani sunana" Yawwa to kaji Muhammad ummu tace iyayenta suna neman irin aikin da kace kanaso za'ai maka kaga shiknn ma abu yazo a sauqi ko,,, "eh hakane annah masha Allah yanzu zamuje in mun tashi daga nan can wajen iyayen nata dan mu qara maganar sosai da sosai domin jin ta bakinsu suma kuma koko? ,, "eh hakane kam gaskia,,," cewar dady mua'zzam saraki,,, duban ummu hani momy umaima tayi cikin Murmushi dan har a zuciyarta taji dad'i na zata kasance kusa kusa da wannan yarinyar wacce gaba daya tagama shiga ranta, taji dad'in ita da bama ta samu gurbin aiki wajen ni'ima ba sai su iyayen nata da suka samun,, hakan yasa ta dubi mua'zzam saraki tace "yawwa nuree nikuma saina dauki ita ummu d'in tana tayani dan wani abun wanda ba'a rasa ba a cikin gida koya kagani,,,? "bakomi wifey na indai hakan yayi miki to nima yayimun,,," cewar dady mua'zzam da yayi maganar cikin sakin fuskarsa wanda ga alama annah ma taji dad'in fad'in haka d'in da tayi itama dan yanda fuskarta ta nuna hakan itama a lokacin kamar ta shi dady mua'zzam d'in,nan suka gama shirya in zasu wuce zasuje can gunsu baffa d'in... ana tsaka da haka Saiga doctor lurwan ya shigo ya qara duba jikin momy umaima yaga komi lpia nan yayi musu bayanin abubuwan daya kamata ta dinga amfani dasu ta fannin ci da sha kuma zuwa gobe da safe za'a basu sallama,,, yana shirin fitane amman ya dan tsaya tareda yiwa dady mua'zzam d'in bayanin cewa an samu gidajen amman sabuwar anguwa ce guda gidajen suke jere da juna,, daddy mua'zzam yace"to shiknn babu komi zuwa dare zan ganka doctor " d'an rusunawa doctor lurwan yayi yace "shiknn alhaji,,," sai alokacin ma ne shi ya lura da ummu hani dake gefe gefen momy ni'ima a zaune knta a duqe,,, yayi mamakin ganinta tareda wadan nan mutanen amman saiya share kawai yasa kai ya fice,, ummu tana shirin miqewa taga mahabeer ya dawo dakin,, dan haka sai ta koma ta zauna a dabarance da nufin inya ida shigowa d'akin ita kuma sai ta wucewarta,, dan bata son kusanci dashi ita tunda ta gane shi d'an saurin hawa ne a lokaci qanqani na saninsa datai,,ga kuma taqama irin tasa da nuna isa da fad'in rai dud shi daya tayi mgnr a zuciyarta tana mai yatsina 'yan siraran pink lips dinta, a bayansa kuma wata mace ce wacce kallo daya zakai mata kasan cewa kiristan ce,, sabida iriyar shigar dake jikinta wani irin mini sikert ne iya cinya sai body hug a jikinta ta dora wani tulin gashin doki bisa kanta sai wani baqin gyale iya kafada data yafa la66an nan nata manya masu tudu dasu sun sha wani pink na janbaki sai shining sukeyi tana faman taunar cwingum q'as q'as wanda Kaida ganinta kasan lallai idanunta suke bude tarr fiyauu dasu da sanin maza iri iri fuskarta har wani yellow yellow takeyi na tsabar mai dataci,, gaishe dasu dady mua'zzam tayi sannan ta matsa gaban gadom da momy umaima take tadan dafa qarfen gadon ta dan rusuna tace "hyyy momy ya jiki,, tin kan momy umaima ta amsa d'in tayi miqewar ta tsaye tana cigaba da taunar ta,,, "lpia pha,,," Abinda momy umaimah tace mata knn momy ni'ima da annah kuwa mamakin ganin ta kawai suke,,, a zuciyar momy ni'ima kuwa fad'i takeyi miye ya had'a mahabeer da ita wannan kuma datake ta rawar jiki haka,,?? wasu ledoji na oesis ta ajiye gefen qafar annah tace "grandma gashi abawa momy ba yawa,,, momy umaima tace"angode da hidima" ummu hani ganin yanda wannan budurwa ke rawar jiki tana shisshige masa shi kuma bai ma san tana yiba dan Yana can wajen su dady mua'zzam shi,,, amman jefi jefi taga yana dan maido hankalin sa wajen fisha sannan kuma ya dauke yana wani ta6e lips. yatsina masa fuskar ta tayi lokacin da idanunsu suka qara karo da juna harara ta sakar masa a kaikaice sannan ta dauke fuskar ta tareda miqewa tsaye tacewa su momy "zan koma can daki mah kada su baffa suga shiru ban koma ba,,, tana maganar ne cikin nutsuwa,,momy da momy ni'ima sukai mata godia har annah na cewa zata zo itama anjima ganin maman nata da jiki,,, tazo dai dai wajen su dady suma tai musu sai anjima anan dady mua'zzam d'in yace saimuje tare ko haj Muhammad wajen baban nata muji daga bakinsa shima,,"to shiknn tashi sukayi suka wuce ta gefen mahabeer suka nufi qofan fita dayake ta fad'a musu room d'in 'yan hatsari suke gado na biyu, "amakson" abinda ta furta masa knn lokacin data zo giftawa ta kusa dashi tai wucewarta tabar dakin ya bita da kallon wato ta sake maimaita mun kalmar nan knn ko?? dafe kansa yayi miyasa yarinyar dabai sani bs har take neman sakasa cikin damuwa da al'amurran tane wai??? mitake nufi da kalmar nan da take yawan jefanshi da ita wai??? runtse idanunsa yayi yasake budesu sannan ya tashi ya koma wajen su annah ya zauna tareda fad'in "annah ki taimakamun ki fad'a myn ma'anar kalmar nan ta *Amakson* da waccen buzuwar yarinyar ke fad'a mun,,, plzzz annah ya qarashe maganar Yana mai had'a hsnnunsa waje daya kamar zaiyi kuka,,, dukkansu wajen da kallo suka bisa harda bleesing data samu zama a dayan kujerar itama ta harde qafafu waje daya tana binsu da idanu,,,,,, Momy umaima ta dubi annah tace "miya faru tsakanin mahabeer na da ummu annah? Momy ni'ima tace ''nima dai da tambayar da zanmasa knn kika rigani,,, Annah tace "ku rabu dashi baida gaskia ne shiyasa take ce masa hakan,,, nan annah ta fad'a musu abinda ya faru tsakanin nasu da ummu a lokacin,, Momy ni'ima ta dubesa tace "ayya d'ana,, miyasa haka??? sinne kai yayi qasa sannan yace"ban lura bane momy,,, yo daman taya zaka kula kataho kana sakar wa mutane irin zuciyar ka a hanya ja'irin mutum kawai,,, dariya sukayi shikuwa miqewa yayi ya dubi annah yace "dan Allah fada mun Anna maanar kalmar kinji annah ta??? dayake bleesing ta saba ganin dramar tasu intaje gidan nasu sai abin ya dinga sake bata dariya itama,,, Annah tace"bafa zan fad'a ba nagaya maka kaje can wajenta ka tambayeta in ka matsu saika jin,,, Fuuuuu yabar dakin fuskar a tur6une bleesing tabi bayansa bayan tayi musu Allah qara sauqi annah ta bisa da fad'in "haka dai ka saba can kaika jiyo matarka ta banu kam ammn bafa da wannan kiristan nake ba dan babu aure a tsakanin ku nama fad'a ma shashashan yaro kawai wanda bai san inda kan sa ke masa ciwo ba,,, Momy ni'ima dariya kawai takeyi itada yayinda momy umaima ke fad'in "ni ai nasaba da wannan karon battar tasu indai mahabeer da annah ne,,,,, dady mua'zzam sun tattauna da baffa kuma shima cikin jin dad'i yanuna amincewar sa,,bugu da qari yace ko goben ma saisu tafi inda likitan yace gobe ne ranar sallamr tasu,,, har a cikin zuciyar baffa kaddo yaji dad'in wannan aikin da ummun tasa tai musu silar samu cikin sauqi da hukun Allah,,basu jims ba suka tafi suma,,, mahabeer kuwa suna barin hospital d'in da blessing school dinsu ya maidata shi kuma daganan ya wuce wajen su bash,,,, washe gari kamar yanda likita ya fad'a haka ya basu sallama duknsu kuma akayi sa'a dud a lokaci daya ya rubuta musu sallamar dan haka gaba dayansu a dady mua'zzam d'in ya daukesu da kansu a motarsa dayake mahaber ya wuce office shi,,, driving yake momy umaima na gefensa suna fira cikin farinciki da annushuwa,,jefa jefa kuma takan juyo baya taiwa su ummu hani magana cikin kulawa,, ummu kuwa ita ji takeyi dud sanyin esin motan ma ya takura mata harta fara karkarwa na son yin masassara abinka daba'a saba ba daman,,, qarfe 2:30 suka dira a harabar gidan mua'zzam saraki,,har wajen annah ta iso tana musu barka da isowa cikin murna
Chapter 24 · 0% Book details