← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 109

Sashe 46

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

tace "ah to kai ka tsaya kaima ka karb'a naka man? ko juyowa baiba ya furta kalmar "naqoshi'' daga haka yayi shigewarsa d'aki, tab'e baki annah tayi tace "kaji da halinka dai ay kai day'a. Murmushi momy umaimah tayi tace "to kada dai muji kanku yau annah keda angon naki, annah tace "ahaf jinkai ai saidai Allah shi kyauta umaimatu . dariya momy umaimah tayi kawai tareda fad'in "lallaikam, bayan ta miqawa annah lemon data tsiyaya mata cikin cup din mai sanyi, qishirwar da annah keji ne yasa ta sha lemon sosai... sai daga baya ta zuge jikkar ta fiddo masu tsaraban su yalo irin manya manyan nan, guavas, tantali6o, rake, dud kayan kasuwa na kayan marmarin su na nan kasuwar katsina su annah tasa yusufu dan qanen umaimah yaje kasuwar filon bugu ya sissiyo mata su, nansu ummu hani suka wanko kayan suka dawo nan falo itada nabeela sukaita cin abinsu yayinda annah taketa musu wasa da cewa ashe ummu hani kinyi qawa bayan tafiya na? gashi harta saki qara sakin jiki cikin mutane ko babu d'ari2, dariya sukayi dukkansu wajen. tarayyar ummu hani da nabeela yau da gobe yasa itama ummu hani qara wayewa sosai, dud dressing din da nabeela tayi sai itama ummu hani tayishi, matuqa momy umaimah da annah sukejin dadin qawancensu,,dan yanzu babu inda basu kewaya cikin motan nabeela a cikin garin kd, hatta driving nabeela ta fara koyawa ummu hani Kad'an kad'an. abinda momy ni'ima take kiransu dashi kuwa 'yan biyun mah dinsu. dan har cen suke zuwa siyi mata fira insun baro wajensu baffan ta. yau da marece ne misalin qarfe biyar mahabeer ne zaune shida bash da mukhtar ango nan harabar gidan bisa fararen kujeru, suna fira, ganin shigowar wata jar mota ne a gate din gidan yasasu maida hankalin su wajen, "ya ilahee! ,,wannan qwallaffaffiyar saida ta biyoni gida knn hankalinta ya kwanta?, abinda mahabeer yace knn a qasan lips dinsa lokacin dayake kallon blessing tana nufosu byn tafito daga motan nata,,, Mukhtar ya dan tabosa tareda fad'in cewa "gafa mutuniyar ka nan gifted tazo,, kan mahabeer ya bud'e baki harta iso wajen cikin shigarta na mini skert dawata yar riga iya qugunta tayana wani dan mayafi akan gashin dokin dake bisa kanta wanda tayi gammo dashi ammata kitso sama da dubu akan nan nata, sai kuma 'yar q'aramar jikkarta dake sagale a hannunta ta iso wajen tareda zama bisa dayan kujerar tana fad'in "hey sannunku bash ango yakuke,, bash da mukhtar ne suka amsa mata shi kuwa mahabeer ido kawai yasa mata,, ganin hawaye na fitowa daga idanun blessing dinne yasasu yin mamaki matuqa na tunanin anya kuwa lpia,, jisukayi tana fad'in"haba m heart kusan sati nawa inata son mu hadu akan maganar danace maka zamuyi amman kayi banza dani heart na? why why please?? Kasan kuwa yanda zuciya na kemum gameda kai? Tana maganar ne bilhaqu duta koma kalan tausayi, jiyayi ya tausaya mata baison yaga mutum wnda yadamu dashi haka a damuwa, mahabeer dud zafin kansa shi mutum ne mai matuqar tausayi, ajiye magazine din hannunsa yayi saman tebur ya zuba mata attention nasa gaba day'a a hankali ya motsa lips dinsa yace "sorry abubuwan ne sukai mun zafi wannan lokacin shiyasa bnda tyme sosai ammab ynxu fada mun mike faruwa? har taji dad'i dataji wannan bayanan daga garesa gyara zama tayi tace "daman dady nane yace ya yarda zamuyi marriage tsakanin mu amman da sharadin inzaka barni ina zuwa churhc, nasan baza'a samu matsala a gunka ba zaka amince ko heart nawa? Zuba mata kalan idanunsa yayi cikeda tunanin lallai ma bleesing mita d'aukesa ne? Koda yakeda burin aurenta tofa saiya musuluntar da ita yake nufi a zuciyar sa? danko shi ya amince zai aureta a hakan yasan dady mua'zzam bazai taba bari ba uwa uba rigimammiyar tshohuwar sa annah. girgiza kai yakeyi tareda qara kallon ta, bash da mukhtar sudai nasu idanuwa ne, "no no my choice no, iknow my parents bazasu amince da hakan ba, why not kije ki lallaba dadynki ya barki kishiga religion namu?,, wani zuba masa idanuwa tayi kamar mai tunanin wani abu nan kuwa tuno taurin kai irinna dadynta towmey fele takeyi,, shikuwa gyada mata kai yayi yaci gaba da cewa "yess my choice,,, our religion abune mai kyau fa, Musulun ci yafi kowane addini tafe da gskia ziryan a cikinsa ba sirki.. kiyardaki shigo cikinsa danki qara tantance gskiar abinda nike fada miki my choice , bash yace "wannan haka yake, addinin musulnci addini ne kuma mai dad'i mai sauqi da sauqaqawa madam bleesing, kiyi qoqari kishawo kan dadynki ya amunce ki musulunta dan banjin dady mua'zzam saraki zai yarda da tsarin dadynki wlh, "wannan ai bama maganar ji bace silly talks knn,cewar mukhtar yana daga kishingid'ensa yana zuqar taba wanda aq'alla ba'a kasara ba zamansu gab yake da shanye one parket na kwalin tabar sigarin. shiru bleesing tayi zuwa can taja numfashi sannan tace ,, "zan qoqarta komi knn mukayi da dadyn zan fad'a ma i swear i realy love you m heart,, sakar mata lallausan Murmushi yayi yace "gud my choice thanks , murmushi tayi itama tareda miqewa tsaye tace can i go? alama yayi mata da ido na you can go??? Murmushi ta sake sakar masa tace "sorry herat na zanje karb'owa momy na saqone" tashi yayi yace ''ok no problem muje na taka miki wajen moton ko? "Yeah herta na thanks woo,, ahaka suka isa inda tayi parking motor din nata tashiga motan suna dagawa juna hannu yana nan tsaye har watchman ya bude mata gate ta fice tunkan old soldier watchman din yakaiga rufe gate din saiga wata motar tasake kunno kai a harabar gidan, wata motan again tabiyosu baya kuma. ummu hani ce ke driving din yayinda nabeela take gefenta. Cikin shigarsu iri day'a ta doguwar rigar material mai fari dajan zanen kwabo-kwabo a jiki, fatar nabeela it's beutiful shiyasa farin material din ya amsheta itama, aman kuma ba kamar yanda yaiwa ummu hani ba mugun kyau a jiki ga white skin nata sosai, mussamman ma yanda d'inkin ya zauna mata daram dam a jikinta kamar nan aka yisa. rigar gashi ta bude daga q'asanta sosai, gawani cunku na aiki dake gaban rigunan nasu,, masha Allah albarkatun qirjin ummu hani sunfi tasowa cike suke dam a gaban rigar kamar zasu bullutso su fasa mata gaban rigar nata, danma sunsa gyalen material din ya sauko musu har bisa kafad'a zuwa kafad'a, parking sukayi suka fito nabeela na cewa "yes gskia kin burgeni sister wlh ynda kikayi saurin koyon tuqi haka? gskia na jinjinawa brain dinki qawata, kice daga yau bazamu qara xuwa filin koyon driving bamako ? ummu hani na shirin bata amsa sukaji sallama daga bayansu, juyowa sukayi dukkan su, haisam yana tsaye jingine da farar motarsa new designer saurayi ne matashi shima baro wajen motar yayi yaqaraso wajensu ummu hani din yana jifanta dawani kalar Murmushi,, dud abin nan mahabeer yana gefe cikeda matuqar mamakin ummu hani, gaba day'a yaga yarinyar ta sauya masa tawani waye lokaci day'a? Itace hadda iya tuqa mota?? ransa yaji yayi wani mugun b'aci.. wato yawo tasa gaba knn ynzu shiyasa sai yajima ma baiga wulginta cikin gidan ba, dudda bawai zama yake sosai ba shima kwanannan?? wato shine gata ita fitsararriya shafaffiya daga momy zuwa annah harda gayyato musu wani qaton banza cikin gida mako? Saikace ba yar aiki ba? lallaikam yarinyar nan bata sanshi ba ne har yanzu, zaiko ci mutuncinta ne saffa saffa yanzun basai anjima ba kuwa daga ita har saurayin nata data kwaso musu cikin gida,,, , inda suke ya tunkara gadan gadan zuciyar na masa wani kalar zafi tareda sauyawar launin fararen idanunsa zuwa jajaja!!!.. ..
Chapter 46 · 0% Book details