Sashe 44
Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
🌊🌊🌊🌊🌊 🅿3⃣6⃣ 🌊🌊🌊 Momy umaimah tayi kusan minti 15 sai dai ta kalli hjy aina sai kuma ta kalli hannat harta kai ga sun fara tsarguwa da kallon nata garesu,, hjy aina ce tayi qarfin halin sake cewa "koko shawarar dana baki kina mata kokon to? inkina kokonto kibarshi kawai Allah baku zaman lpia keda 'yar aikin naki hajiya umaima" yanayin yanda hjy aina ke maganar ne kaida ka kalleta kasan da biyu take mgnr,, dan a zatonta momy umaimah tuni tahau layin da takeson d'aurata ne. burinta ace momy umaimah takori yarinyar ita kuma tabita ta siyeta da kudi ta dinga neman kudi da ita dan taga yarinyar sosai-sosai girkakkiyace babu inda keda makusa ajikinta dole alhazawa suci uban dollers akan ta qarewar ma naira. saidai abinda taji momy umaimah na cewa yasa taji abun kamar a mafarki dan bata taba tunanin jin hakan ba daga gareta,, dubanta momy umaimah tayi sosai sannan tace ''yanzu hjy aina danna temaki bayin Allah shine qaramar kwanya ta wajaba kaina knn ashe?,,,,,, yanzu hjy aina a misali ace rai yayi halinsa kuma ace baki da kowa a ckn garin nan kin tafi kin bar hannat shin zakiso ace tashiga quncin rayuwa na rashin kulawa daga Al'ummar Annabi? yanzu hjy aina in miki mai gaba d'aya madai tukun inkece ke cikin halin rashi da yarinyar nan da iyayenta suke ciki kuma sai gashi Allah ya kawo miki mutanen da zasu temakawa rayuwar ki ta inganta yanzu zakiji dad'i kuwa? Shin hjy aina mutumin dayai nufin rabaki da inda kika samu kika ra6a a wannan lokacin shin maqiyi zaki kirasa ko masoyi,?!, Hannat tayi karaf tace "momy maqiyi ne, wata uwar harara uwar ta aika mata da ita tareda danqara mata daquwa tace "uwaki 'yar banzar yarinya waya sakoki ne cikin batun? Idan na sake na qara jin bakinki anan saina fasa miki shi kuwa yayijini shashashan yarinya kawai" turo baki hannat tayi tana gunguni ta fiddo wayarta ta hau yin game abinta,, dud abinnan momy umaimah tana binsu da ido itakuwa batta fatan ace yau mahabeer zai auri wannan yarinyar dan kaida kaga idanunta sam babu d'igon kunya a cikinsu, misali ma gashi yanda takewa uwar tata wannan kallon daga magana,?! tab???,, taff ta godewa Allah ma da mahabeer bawai wani attention nasa yake bawa yarinyar ba bare tsautsayi yakaisa ga auren 'yar mace. wanda ta lura ynda hjy aina ke masifar son diyar nan tata to abin Allah kyauta koda anyi auren wani abu ya hadasu tsaf zata iya komi akai kuwa wnda hakan zai iya silar wargajewar zumuncin nasu to qwamma dai maganin kar ayi kar a soma. jiyayi hjy aina tace "shiknn kiyi haquri hajiya umaima da maganganun nawa kinsan zuciya da saqe saqe shiyasa na ga kamar hakan zai iya faruwa mafarin knn na tanka"",, tayi maganar zuciyarta cikeda takaicin rashin samun ummu hani da batai ba ta shigo hannunta. Ita kuwa momy umaimah tayi zaton har a ran hjy aina haqurin nata data bata babu komi aranta shiyasa cikin fara'a tace "hmm yawwa hjy aina nima nagode da fahimta na da kikayi kuma babu abinda zai faru sai alheri dan ummu hani yarinya ce mai tarbiyar gaske, kuma wlh koda ace mua'zzam saraki zaice yana sonta zan amince masa dan qwamma a auro maka wacce kasan halinta akan wacce bakasan nata ba, "a'a daga nan dai, cewar hjy aina tana magana tana tada uban hancin nan nata sama. danma butulci yasa ta kori baqin fatar fuskar nata da man coylean wnda muggan q'uraje na pumples kuma sukazo suka maye farin fuskar da asalin fatar da Allah yabata ta kushen. murmushi Momy umaimah tayi ta canza maganar da cewa "gashi ko ruwa ban kawo muku ba munata fira" tayi maganar tana cin dambun naman ta da small spon d'inta. Miqewa hjy aina tayi tana fmn yafa gyalenta akai tace "a'a Wlh babu komi ynxu haka ma zamu wuce gidan hjy indo ne qawata zamuje gidan bikin diyar aminiyarta shine muka biyo tanan domun inga yanayin jikin naki kema",, momy umaimah tace "Allah sarki nakuwa gode hjy aina ku gaida gida,, "to gida zaiji kuma inaga nanda 2 days zan koma sake kawo wasu kayan dan wadancen sunqare inji 'yan kasuwan danake bawa su, komi knn dai zamuyi waya kanna tafin,, "to shiknn hajiya aina Allah kaimu lokacin lpia," ''Aminn" har bakin mota momy umaimah ta rakasu sannan ta dawo falon ta zauna ta qwallawa ummu hani kira wacce ke kwance bisa gado tayi rub da ciki zuwa yanzu ta daina kukan sai ajiyar zuciya da take ta saki gamida sake kai kukanta ga Allah dan kareta daga sharren ire iren su hjy aina. tashi tayi da sauri ta goggoge fuskarta ta fito daga d'akin ta iso har inda momy umaimah take ta zauna ta d'an saki murmushi kad'an tace"gani mah har baqin naki sun tafi?,, murmushin da ummu hani taga momy umaimah tayi yasata jin wani farinciki a ranta dan ga alama momin tata bata d'auki shawarar na aminiyar nata ba,momy umaimah tace "suntafi ummu, naji falon ba dad'i ni day'a shine na kiraki kizo muyi fira kinje kin qunshe d'aki ke mai tsoron mutane ko? Tayi maganar cikin murmushi, 'yar Murmushi ummu hani ta saki tace"laaa mah nadai bari ku gaisa ne shiyasa, girgiza kai momy umaimah tayi tace "suntafi ai, Ni naji dad'i ma da mahabeer bai gidan wlh, zuba mata ido ummu hani tayi tace "sabida mi momy? Tace "saboda hannat wlh, nasan da tana nan har yanzun bawai son da take masa ne ke bnson ganiba ne a'a, ummu sam hannat tanada qarancin tarbiyya nikuma dud mai wannan halin gskia ban san inga yana huld'a dani bare wani nawa, mamanta tarigaya data sangartata sosai,,! shiru Momy umaimah tayi tace "koda yake ma mubar zancen nan ummu zo kibani labarin garinku dan ina sha'awar al'adar bikin garinku ummu inga kunsa kayan nan naku baqaqe masu adon zanen zaruruwa a jiki tareda nad'in kanku kamar na gwadanki na mayafi nn wnda dashi ne naga ake muku ku amare,, ki fad'amun yaya kuke hidimar bikinku ummu???, tayi maganar cikin fara'a. nan kuwa ummu hani ta saki jiki taita bawa momy umaimah labarin ynda ake shagulgilan nasu na aladar su cikin sanyintana murya, saida momy umaimah tagama jin komi sannan tace ''kai amman gskia abubuwan naku dai daban burgewa aladar ku kam, musamman ynda kikace dukkan dangi ke taruwa wajen auren mnya da qananan ku. yanzu dai mu ajiye wannan firan gefe najima inason in miki wata magana ummu hani, duban mah din tayi sannan ta maida kanta qasa tana d'anyin wani q'as q'as da yatsunta tace ''to mah tambayeni koma miye,, aranta tsoro take AllAh sa bawani abun taiwa mah ba dai,, jitayi momy umaima tace"a fannin addini Ummu kinada karatu tanan 6angaren kuwa? in baki dashi kada kiji kunya ki fad'a mun dan ni mutum ce mai son ilimi zan saki makaranta yanda zaki karantu kinji ko ummu hani? ajiyar zuciya tasaki 6oyayyiya sannan ta d'ago ta dubi mah din tace "eh mah baffa na malamin addinin islamah ne, kuma nayi karatun litattafan addini da dama wajensa na sauke quranin Kareem da dama yanzu haka akwai hadda ta Q'uran inayi sosai itama,,, murmushin jin dad'i da farinciki momy umaima tasaki tareda kama baki cikin zolaya tace "aaa ikon Allah, ashe ni da malama Ummu hani nike zaune ban sani ba?, sanyayyar dariya ummu hani tasaki ta langwabe kai gefe tareda fad'in "kai mah,,, "da gaske nk ummu kuma naji dad'i dakika kasance haziq'a haka gskia dud d'a namijin daya dace da 'yar nan tawa tofa babu shakka ya za6arwa yaransa uwa wacce manzon mu yayi umarnin da ita a aura, bareke ummu kin had'a komi ma wlh, kai masha Allah wlh,, ummu hani dai batace komi ba sai kanta data kwantar kan cinyar Momy umaimah,, ita dai haka take da son jin taushi kamar wata mage, jitayi momy umaima tace to batun boko fa kinyi ne shima,? "Eh mah nayi amman daga secondry school na tsaya,, "ok kina buqatar kici gaba to? Shiru ummu hani tayi tasan kota amince su baffa ba lallai ne su amince ba gskia inda bawai zama ne ya kawosu garin ba neman lpian mamanta ne. girgiza kai tayi tace "mah wanda nayi ma ya isa nasan su baffa bazasu barni bama nayi, gyad'a kai momy umaima tayi tace "hakane kam kuma umarnin iyaye binsa abu ne mai kyau, "babu komi Allah ya albarkaci wanda kika samu d'in" "aminn mah, mah sai yaushe ne annah zata dawo mana ne?, tayi maganar tana Murmushi har a ranta take missing na tsohuwar kirki annah,, momy umaima tace "nasan wannan satin mahabeer na zaije ya dawo da ita dan shima naji yana maganar tafiya daukotan next week.... sallamar wata matashiyar budurwa ce yasa su juyawa gamida amsa sallamar,, cikin fara'a momy umaimah tace "ah nabeela ce shigo shigo man, har qasa nabeela ta zauna ta gaisheda momy ta amsa cikin kulawa tace "ya mamanki? nabeela tace "tanama gaisheki momy itace ma ta aikoni tace in gaisheki da jiki kafin ta shigo (nabeela 'ya ce a wajen hjy asma'u maqotane suda momy umaimah, suna zumunci sosai,, wannan shekarar ne nabeela ta ida kammala karatunta ta dawo gida gaba day'a. nabeela yarinya ce mai kirki da son mutane sosai ta biyo halin mamanta asmau,, bazata wuce sa'ar ummu hani ba, ita kadaice wajen iyayenta a yanzu haka Wanna knn). Momy umaimah tace "Allah sarki ngd wlh sosai, ina ruwan hjy asma'u. Cikin fara'a nabeela ta dubi ummu hani tace "momy baq'uwa kukayi ne? Naga bansanta nan ba saidai yah mahabeer, "eh nabeela matsayin d'iya na ke daukanta ta, sunanta ummu hani,, hannu ummu hani ta miqa wa nabeela sukayi musabiha cikin Murmushi wa junansu,, Nabeela tace "Allah sarki momy nakoyi friend wlh dama zaman shiru a gida ya isheni zan dinga zuwa muku fira wajen ummu qawata,, dariya momy umaimah tayi tace "hakane kam nima zanji dad'in qawance kuwa nabeela da ummu koba komi zaki dinga sata fitowa cikin jama'a kin ganta nan kamar mai tsoron mutane haka take, Murmushi ummu tayi tace ''kai mah,, "eh man Ummu hani haka kike fa gskia na fad'a,, dariya nabeela tayi tajawo hannunta suka miqe tsaye tace momy zamuje gidanmu da