← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 109

Sashe 65

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ya iya bare shi daman gashi ba gwanin son magana ba ko musu musumma da iyayensa wanda bai saba ba dan haka yace "to dady sai anjima bakomi"!!! yayi maganar yanajin wani sabon q'una a ransa. bayan ya kashe wayar ne ya miqe tsaye harya d'auki day'a daga cikin bags dinsu guda 3 sai kuma yayi wani tunani ya duresu nan yaja ya tsaya ransa a b'acen ya sake duban ummu hani dake tsaye wajen wani glass mai cikeda ruwa dawasu qananun halittu masu kyau tanata shafawa taji yace "ke..?!!!!!!!,,,,, a hankali ta juyo tana kallonsa amman batai magana ba, cikin figitacciyar muryar sa dataji ta daki dodon kunnenta yace "keee!!! wai badake nike ba zaki maidani d'an iska iye?? kin koma kina kallon wani wajen daban ma ko,? fararen idanunta ta sake zuba masa a cikin nasa tace cikin sansanyar muryarta "naji kace ke ne shiyasa banyi zaton dani kake ba ay" tayi maganar tana mai sake d'auke idanun ta daga garesa cikin tsananin jin haushinsa itama, a zuciyar ta kuwa cewa take daman nasan za'a rina ay, masifarka saita hayyaci rayuwata a yanzun. jitayi yace "ohkey to ba za'a fad'i sunan naki ba danni bama wai sanin sa naiba, kuma bnda buqatar sanin nasa dan abu mai amfani nikeda buqatar saninsa ni a wajena bawai marar amfani ba kuma daga yau ma kijini da kyau da sunan ke zan dinga kiranki dashi kuma kikace zakimun rashin kunya wlh zaki qara sanin koni waye dan yanzu mun baro nigeria bawai a gabnsu annah bane bare ki fake a bayansu ok? dan haka kuma yanzun ina mai qara umartarki da cewa kizo nan!! kallonsa kawai takeyi lallaikam wannan mutumin baida mutunci ko kad'an amman ina roqon AllAh daya dorani a kanka mugu kawai dakai. abinda take fad'a knn a can qasan zuciyar ta, a hankali take takowa harta iso gabansa taja ta tsaya tana jiran sai kuma mi yanzu,, gani tayi yayi nuni da yatsansa ga jikkunan dake zube a gabansu yace "oya oya hurry up,, carry go one by one kikai munsu saman dakin can'' yayi maganar fuskar sa murtuqe babu alamun sassauci yanda kasan bai taba sanin taba a rayuwarsa haka taga ya juye mata at the same time, kauda fuskarta tayi daga garesa ta kai dubnta ga jikkunan tana tunanin ta yanda zata iya hawa saman dogon benen can dasu,, amman batason ta nuna masa karayarta dan kada ya rainata inyaga gazawarta bare kuma harya samu damar sake cimata wani sabon rashin mutuncin nasa ma, a hankali kuwa ta sunkuya ta sa hannunwanta guda biyu ta d'auki jikunan ta fara tafiya dasu ga jikin qafafunta, shikuwa yana zaune a wani dan kushin ya harde qafanunsa cikin na juna yana binta da kallo,,,dud bayan taku daya biyu ukku sai ummu hani ta dan tsaya ta huta tana sauke ajiyar zuciya a haka harta samu takai dayar sama ta dawo ta dauki dayar itama daqyar da jibin goshi tasamu ta kaita saman ta dawo zata daga ta ukun knn qarfinta gaba day'a taji ya qare mata, taji ta kasa d'aga jikkar ko Kadan, dole tasa ta ta duqa qasa ta kwantar da jikinta saman jikkar tana sauke numfashin wahala, shikuwa yana gefe yana sakin wani sabon b'oyayyen murmushi sai amsa wayarsa yakeyi da bash hankali kwance yana karkad'a kafansa, kallonsa tayi kawai ta lumshe idanuwan dan ta rasa wani iriyar sunane yadace ta kirasa dashi ma yanzun? banda qishirwa babu abunda ke nuqurqusarta lokacin kuwa,, sake lumshe idanuwan ta tayi na wasu 'yan mintoci sannan tasake budesu ta hango wani dogon pridge, cikin qarfin hali kuwa tasamu ta miqe tsaye ta fara tafiya harta isa ga fridge din ta bude taga lemukane kala kala a ciki sai kuma ruwan, da sauri ta dauko roban ruwa jikinta har wani kyarma kyarma yake na tsaban qishin da takeji ta lumshe ta ta bude murfin knn zata fara shan ruwan taji anyi saurin fusge gorar ruwan daga hannunta, da sauri kuwa ta bude rufaffun idanunta takai dubnta garesa yana tsaye qiqam a gabanta tsayuwa irinta ingarman namiji cikin kakkausar muryarsa taji yace "bari kiji ke kinyi kad'an da kisha ruwan nan wlh kozaki mutu kuwa matuqar baki ida yin aikin dana sanyaki ba, wasu hawaye ne taji sun sulalo mata tasa hannun ta babban dan yatsa ta gogesu sannan ta tafi wajen dayar jikkar ta tattaro dud wani sauran qarfinta ta dauki jikkar tafara tafiya zuwa sama da ita itama, dan kanta kaita ta duqa saman hanya yafi sau 20 sannan ta samu takaita can inda sauran suke sannan tazo saukowa tagamu dashi shima yahau saman yana tafe yana shan gorar ruwan masu sanyi daya amsa daga gareta, ya rab'ata ya wuce ta gefenta ko kalloma bata ishesa bama ya shige dakin tareda bugo qofar dakin da qarfi, girgiza kai tayi kawai ta samu tasake lallabowa ta sauko qasan takoma wajen fridge din ta sake dauko wata roban ruwa tasha tasha sosai sannan ta zube bisa carpet din wajen tana mayarda zafaffen numfashin ta waje, q'irjinta kuwa sai faman sama da qasa sukeyi dan tsabar fita hayyacinta da tayi, tayi matuqar gajiya banda wanka babu abunda takeda buqata lokacin, dudda tana jin yunwa inda bawani abinci na kirki taci ba da zasu tafo, shi dama bacin abinci yake ba inzaiyi tafiya har yanzu hakan yake bai canza ba, dan haka ba biye masa taiba tadan tsakuri kad'an cikin tursasawar momy umaima ma, ga salla tanaso tayi tayi kuma. shiru tayi tana tunanin yanda zatayi jitayi muryan sa daga saman ya sake cewa "ke?? zo nan, d'aga kanta tayi sama taga har yayi komawarsa cikin dakin da harara tabi bayansa takusan minti 10 sannan ta yunqura ta tashi ta hau saman ta shiga cikin dakin ta gansa a tsaye ya riqe qugu daga bakin qofar dakin taja ta tsaya tace ''gani amakson, wani takaici ne yaji ya qara kunno masa narashin sanin taqamaimain wannan ma'anar sunan datake kiransa dashi haryanzu? danshi tunda suke zai iya cewa bai ta6a jin yau ta ambaci sunansa ba, kuma shi yaji dad'in hakanma dan baida buqatar daman ta ambaci sunansa din daga bakin ta, ita kuwa sauke idanuwanta tayi daga kansa tadinga bin tsarin dakin da kallo. gado day'a ne tagani mulmulalle dark blue bedsheet dinsa sai wata katuwan katifa qasa shafe da tattausan bedsheet cotton light blue shima sai toilet sai wajen kwalliya da saka kaya. rassss!! taji gabanta yayi mummunan fad'uwa... "badai a daki day'a zamuna rinqa kwana dashi ba???!! tambayar data bawa zuciyar ta knn, kanta samu amsar tambayar nata taji yace "dalla duba nan mlm kin zauna kinawa mutane kalle kalle tsiya mtss,,tsiyar baqauyen mutum knn sai anyi masa da gaske snn, har a ranta matuqa taji zafin abinda yace matan sosai. "kiduba nan nace ko?? taji yasake maimaita mata maganar, d'agowa tayi ta dubesa ya janye fuskarsa daga tata yace "nan bisa wannan katifan ne makwancinki sannan ga jikkar ki nanma na ajiye miki kusa da itan" yasa hannu ya saki wani labule (hijabi)mai shara shara a tsakanin makwancin nasu ya raba su 2, sai akabar toilet a tsakiya knn, ya jiyo dubeta yace "in kinason wani abu kuma bance kimin mgn ba ki rubuta min a cikin paper ki ajiye min zan gani you comparehend? ok? miyau ta hadiye sannan ta girgiza kai alamun "yeas"! juyawa taga yayi ya shiga toilet din ya rufo ga alamun wankan zaiyi shima. komawa tayi da baya ta fad'a bisa katifar tata ta rungume jikinta waje day'a ta lumshe idanuwan ta a fili tace "matsalar kane hakan malam, nima hakan yaimun ay sosai🤷🏻‍♀wallahi" "tayi maganar tana d'aga hannuwanta tareda tabe siraran tausasan pink d'in lips dinta tana sauke numfashi a hankali ....
Chapter 65 · 0% Book details