Sashe 52
Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*🌏impacting valuable knowledge and Entertainment is our concern🤝🏻*. 🌊🌊🌊🌊🌊 🅿3⃣8⃣ 🌊🌊🌊 Dady mua'zzam saraki ne ya iyayin q'arfin halin sakin ajiyar zuciya mai q'arfi tareda duqar da kansa q'asa, zuwa can kuma ya d'ago da kan nasa ya dubi mahabeer sannan ya dubi momy umaimah itama, wata sabuwan ajiyar ya saki sannan yamaida dubnsa ga momy umaimah kacokam yace "yakika kalli wannan al'amarin gameda zancen da annah tayi ne? Sauke ajiyar zuciya Momy umaimah tayi itama ta zubawa dady mua'zzam ido tace "kai ya kaji zancen ne kaima? girgiza kai yayi yace ''tabbas maganar annah a dai dai take kuma akan tsari danni gaba day'a wlh hankalina baima kai a wajen ba sam sam, burina dai shine yaje ya dawo musamu abinda zamu faranta rayukan al'ummar mu dashi na yauda kullum akan sauqin cinikayyan. Momy umaimah tace "wlh hakane nima zuciyata ta yadda da batun ananah sosai sosai sai dai matsalar nuree kasan halin d'an namu kaga mahabeer na bawai wasu 'yan mata yake huld'a dasu bare ace cikin satittikan nan har yaje yasameta ayi biki haka? gashi annah bata amince da zancen ita wacce yake harin ba, kamar mahabeer zaiyi kuka yace "dady nina haq'ura da tafiyar ma kwata kwata a barsa inda abin yazo da haka"! dubansa dady mua'zzam yayi yace "kul sojana, karna sake jin kace manufarmu ta alheri ga jama'a zaka dakatar kan an maka maganar aure? to waima sojana idan bakayi aure ba yanzu a wannan matsayin naka na shekaru sai yaushe zaka yisa?, "to dady kunfa san bawasu mata nake kulawa ba bare, damn blessing ce kuma annah gashi ta soke zancenta to yaya zanyi dan Allah ku fad'an?!!" dafe kansa yayi dayakeji yana son fara masa ciwo,, gaba d'aya falon yayi shiru bakaji qarar komi saina esi, har a zuciyar mahabeer baison yaga hankalin iyayensa na tashi gameda shi, danshi jiyake gaba d'aya ma abubuwan sun had'u sun gama d'aure masa kai tam-tam, kwata kwata kwanyar sa ta tushe ya gaza samun mafita akai, gskia annah kam ba qaramin rusa masa budget d'insa tayi ba, shida zaije school harda wani jajibo masa aure aka babu gaira ba sabar kuma? lumshe idanun sa yayi toshi wace yarinya ce yake da ma bare? wata zuciyar tace "a'a mahabeer 'yan mata fa masu sonka Allah ya hore maka yawansu ga ako'ina kaine dai da baka kulasu d'in, amman mai zai hana ka za6i d'aya daga ciki ka aura koda da kundawo zaka saketa kodan ka farantawa daynka na abinda yake san samarwa jama'a sauqi a kansa? (petroleum) "towa zan zab'o ma knn wai? tambayar da yaiwa zuciyarsa knn, hannat ce ta fad'o masa a rai, tsoki yaja dan shikam dai ya tsani mace marar da'a da kamun kai sam-sam, shi kuma ya kula haka halin yarinyar yake, ga kuma bleesing ba musulma ba bare ya fakewa annah tanan, sake damqe kansa yayi yanason samun mafita a brain dinsa amman sai qara cushe masa ma da takeyi a lokacin, momy umaimah ta matso kusa dashi tasa hannna ta dafa kafad'ansa tace "kasani fa dud cikin gidan nan mahabeer na babu wanda ya isa yaja da maganar anna dan haka wane hukunci kaika yanke na gameda yarinyar da zaka aura ku tafi taren em? ganin ya kasaka furtakomi yasa dady mua'zzam sake cewan "ka daure sojana ka fiddo mata ko kaima ka huta da gorin annah a gidan nan wanda take yi maka kullum, cewar dady mua'zzam yana masa murmushi, maida kansa mahabeer yayi qasa yana kallon carpet din wajen kamar cikinsa ne zai gano mafita,, zuwa can ya dago kansa da idanunsa da suka fara sakin kalar nasu jan saboda tsabar tention daya sanya kansa ciki,, a hankalin ya dubi iyayen nasa ya bude bakinsa kamar maiyi masa ciwo sannan yace "kaina yaimun nauyi ne dady wlh bansan miya dace dani ba dady kowa kukaga tayi maku nidai ku samamun,! bazan qi amincewa muku ba, dan qarin farinciki na rayuwata inga kuna alfahari dani a koda yaushe!!" yana gama fad'in hakan ya miqe yabar wajen yakoma room dinsa yana shiga ya fada toilet ya sakarwa kansa ruwa jiyake yanda zuciyarsa ke masa zafi da zunga d'in nan qara ya tsaya cikin ruwan yana dukansa koya samu sauqin damuwar tention din da annah ta d'ora masa a kansa. acan falo kuwa dady mua'zzam ya dubi momy umaimah yace "kinji yaro kuma da wani salon? wato muya daurawa alhakin samo masa matar? koda yake hakanma yayi ay, girgiza kai momy umaimah tayi tace "gaba day'a nakasa gane hali irin na mahabeer na wlh nuree, dud abinka bazaka tab'a iya tantance abinda yakeso da wanda bayya so ba sam wlh"! shiru sukayi zuwa can dady mua'zzam yace "babu damuwa kibar mun komi a hannunna nasan yanda zanyi ni, da sauri momy umaimah tace "nure ince dai ba cikin yaran abokan kaba zaka samo masa matar badai ko? danni nafara hasashen wacce nikega zata dace da rayuwar mahabeer na. girgiza kai dady mua'zzam yasakeyi yace "kamar dai yanda nace kibar komi a hannunna to kibari kawai ninasan abinda zanyi akai, tafiya kuma zaiyi da matarsa insha Allah kamar yanda annah tace din. tagumi momy umaimah tayi tama kasa cewa komi ita, kamo hannunta dady mua'zzam yayi yace "wifey na kada fa kidamu, taso muje mu kwanta dare yayi haka, miqewa tsaye tayi suka wuce dakinsa. kwana 2 da zancen dady mua'zzam yana zaune harabar gidan alhj Muhammad suna fira, zuwa can dady mua'zzam ya dubi alhj Muhammad sosai yace ''abokina aure nike nema fa, a mamakance alhj Muhammad yake dubansa sannan yace "aure kuma alhj mua'zzam? Kishiya zakaiwa unaimatu din kuma?, kama baki dady mua'zzam yayi yace "kai,, au afuwan kasan hausar ce da yawa fa, to ba haka nike nufi ba ya haj Muhammad, sai lokacin alhj Muhammad yace "auhow koda naji zance kam, kuma dakasa yanzun nan nazama dan rahoton hjy umaima, dariya sukayi sannan dady mua'zzam yace "gameda tafiyar nan danace maka mahabeer zaiyi a can London?? alhj Muhammad yace "aff to to na tuno, badai har tafiyar tataso haka ba? sakin ajiyar zuciya dady mua'zzam yayi yace tataso amman da wani zancen duqunqune a cikinta kuma haj Muhammad wlh,dubnsa alhj Muhammad yayi sosai yace "am bangane ba haj mua'zzam,, nan dady mua'zzam ya fad'a masa abinda annah tace akan tafiyar ta mahaber din,alhj Muhammad yace "eh hakane dan gaskia annah ta fad'a dan koni na goya mata bayan hakan💯ma kuwa, dady mua'zzam yace "gaskia ne hakan, to shine nike nemawa mahabeer din aure dan yace na nemasa shi baida wacce zai kawo mana kajini fa da yaro dn Allah haj Muhammad?, dariya alhj Muhammad yayi yace "ho mahabeer,, wai baida wacce zai kawo sai kace ba saurayin namiji ba mai jini a jiki. dady mua'zzam yace "toyaya zanyi ninasan halin 'yan kayana ay, alhj Muhammad yace "gskia kam, to ynzu waka zabar masa nekai haj mua'zzam? kan dady mua'zzam yace wani abun saiga baffa kad'do yazo wajen tareda yi musu sallama, amsawa sukayi duknsu cikin fara'a da mutuntaka, yadan duqa knn qasa zai zauna alhj Muhammad yace "a'a baba dan Allah ka zauna ga kujera nan kaima, dole yasa baffa zama kan kujerar amman a takure,, cikin fara'a shima baffa kaddo ya dubesu yace "Alhamdulilla naji dad'in ganinku haka gaba d'aya, Alhamdulilla masha Allah wlh bazan boye muku ba alhj naji dadi matuqa da yanda kuka temaka mana kuka bamu masauqi a cikin gidajenku tareda bamu aiki Allah yabiyaku da mafifici, har had'a baki dady mua'zzam yakeyi shida alhj Muhammad wajen furta cewa"haba baba babu komi an zama daya ai baba, Murmushi baffa kaddo yayi yace "hakane ngd Ubangiji Allah dai shi saka muku da gidan aljannatul firdausi ya qara lpia da arziqi mai amfani, dukkansu suka amsa da aminn baba, zuciyar su cikeda sha'awar dattakon tsohon. shiru baffa yayi zuwa can yace ''daman nazo ne in muku bayani akan maqasudin shigowarmu cikin garin nan nida ahalina ,, nan baffa cikin maganarsa da bata qware sosai da hausa ba face zallar yaren buzanci yayi ta musu bayanin mafarin shigowarsu garin dan nemawa mai dakinsa lpia da abinda yafaru har zuwa hatsarin da sukayi suka rasa kudin aikin har ka wo yarda da tayin aikin gadin da sukai musu har kawo yau dinnan da suka samu kudin da za aiwa matar tasa aiki dasu, baffa ya qarashe maganar da cewa "to mafarin knn nazo in muku bayanin cewa zamuje asibitin da matan nawa ai mata aikin kuma insha Allah a satin nan zamu koma gida dan nasan hankalin d'an uwana yana cen tashe dan tunda muka taho numban wayarsa daya bamu wacce yace mu qirasa da shi ya fadi a hanya kunga kuwa gashi mun jima a garin nan nasan hankalin 'yan uwa dole ne ya tashi danjin shirin tamu da yawa haka dai, dady mua'zzam yace "kai kai baba banjin dadin yanda tun farko baka fada mana matsalar matar kaba aida tuni an mata aikin nan"!, alhj Muhammad yace "hakane koni da zan dauki nauyin aikin inda ai samun lada ne, baffa kaddo yace "wlh babu komi temakon ma da kukai mana mun gode ay Ubangiji Allah maku ynda kuma kuke kyautatawa jama'a, da "amin,,suka sake amsawa, dady mua'zzam yace "nayi alqawalin ni zan dauki nauyin aikin mai dakinka baba insha Allah, baffa zai musa alhj Muhammad yace "dan Allah kada kace a'a baba inda ba roqa kaiba, dubn dady mua'zzam alhj Muhammad yayi yace kuma nima abokina sai dai mu biya kudin aiki tare dan kwadayin ladar nan, baffa kaddo sam rasa bakin godia yayi ma shi, banda addu'a babu abinda yake sake musu suda iyalensu. har yana rayawa a ransa da masu kudi zasu dinga yiwa talakawansu haka da duniya taci gaba koba komi da sace sace da sauran munanan abubuwa sun ragu inda daman dud yawanci babun ce ke kawo hakan a cikin *qasar mu*. washe gari dady mua'zzam ko su annah bai fad'awa maganar da sukayi da baffa ba yafiita yaje ya dauki su baffa da matarsa da alhj Muhammad suka nufi asibitin, dayake sunsan da bayanin aikin shiyasa kudin aikin suka biya kawai, dayake damanabin yanzu na indai kana dashi babu bata lokaci shiyasa nan da nan aka shirya likitoci aka shiga da mama bintey theater room suka fara aikin su. anyi