← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 109

Sashe 41

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daban kamar maqiyinsa gifted?? Mike damun mutane ne sake for god!!??,, mahabeer kuwa tun kan mukhtar yabar wajen yana gefe baice musu komi ba kamar baima jinsu amman yanajin komi shirun dai yayi musu dan baida buqatar magantuwa a maganar, dan jiyake maganar tasu ma hawar masa kai yake,,, saifa yanzu da shi bash din yake masa wannan tambayoyin, Yana shirin basa amsa ne yaji wayarsa tayi ringing,,yana kallonta har ya katse batareda ya daga ba dan sunan bleesing ne akai yasan kan maganar zuwan dayace zaiyi ne yau kuma yana sane sharewa kawai yayi baiyi niyyar zuwan ba, haka nan ma yaji itama yanajin haushinta. kashe wayar ma yayi gaba dayanta sukaci gaba da firansa da bash anan wajen, Allah ya temakesa ma bakinsa yabar zafin shine ma qarin nutsuwan tasa. a washe garin ranar ne momy umaimh taja ummu hani sukaje kasuwa itada tai mata siyayyan kayan sawa isassu, hadda su baffanta taimawa suma, kayan make up dasu English wears gyalulu suma duta sayawa ummu hani din, daga nan wajen Tailor suka nufa tai masa bayanin yanda takeson dinkunan na ummu hani din su su kasance na zamani sosai sosai. daga nan suka dawo gida, gidan momy ni'ima suka shiga, har wajensu baffa ummu hani taja momy umaima sukaje ta gaishesu cikin girmamawa tabasu kyautar dinkakkun kayan data siyo musu suma. har bakin gate ummu hani taje ta kirawo baffa shima yaga kayan. nan sukaita godia suna jinjina alherai irin na mutanen wanda fa d'azu d'azun nan shima mua'zzam saraki daya shigo gidan wajen alhj Muhammad baffa na zaune bakin get yayi masa kyautar dubu hamsin, haka jia shima alhj Muhammad yabasa dubu d'ari wai albashinsa dud yawansu fa??? shikuwa wane irin mutanen kirki ne Allah ya had'asa dasu ne haka?? Shikam godia ga Allah itace a kasance kullum a bakin su baffa da yiwa bayin Allah nan addu'a,, haka baffa kad'do ya koma ya zauna wajen gadinsa yana cigaba da Sauraran 'yar qarmr rediyonsa yadan kishin gid'e da carbi hannunsa yana lazumi. momy umaima ta jima tana fira da mama binte ummu hani kuwa dad'i kawai tsakeji ganin ynda mah dinta ta d'auki iyayenta da muhimmanci sosai take girmamasu kamar nata Alhalin suna qasa dasu km,, sakin jiki tayi tana daga kwance qafan mommonta idanun ta a lumshe tana jin farin ciki har ranta. batasan sanda barci yadauketa mai dadi ba a saman qafafun mamanta wanda rabon data kwanta haka a qafafun maman nata tayi barci tun suna garinsu,, koda momy umaima ta tashi ciki ta shiga wajen momy ni'ima da sallamarta, wacce take zaune saman pray mat ta gama salla tana zaune tana addu'a,, samun waje momy umaima tayi daga kujerun falon ta zauna idanunta nakan momy ni'ima ganin yanda tasa gefen hijab tayi saurin goge qwallan data kucce mata daga idanu bayan shafa adduarta datayi,, "subhanalla qawata miya faru haka? Kina hawaye? Cewar momy umaima tayi maganar cikin tausayi,, momy ni'ima tana son bude baki tayi magana amman ina ta kasa danjin da tayi wani gululun abu mai d'aci taji ya taso mata ya tsaya a maqoshinta, nan da nan taji wani kuka yazo mata ta duqan da fuskarta saman sallayar tana kuka mai girgiza jiki tana mai fad'in "ya Ubangiji Allah ka bayyanar mun da yarona dan nabiyirrahmati ya Allah,,, kuka take dan jitake kamar lokacin ne aka sace mata jinjiranta mahabeer,,,saukowa momy umaima tayi daga kujerun ta zuqunna a gabanta ta d'ago da kanta ta d'ora bisa qafafunta tace "dan girman Allah qawata ki daina kuka haka kada ciwon ki ya taso haka, kinsan mai hawan jini ba'ason aga yana shiga damuwa, tsagaita kukan nata momy ni'ima tayi cikin kyarmar murya tace"wlh qawata ni kaina bada son raina nake kukan nan ba,! wlh zuwan mun yakeyi bansan yanda zan fidda abin a raina ba wlh har baban boy naima alqawalin daina sa damuwa a raina amman dayake zuciya batada qashi wlh bansan sanda zuwan kukan ke iskeni ba saidai kawai injini ina yinsa!!"" taqarashe maganar cikin cigaba da share hawaye da farin hijab dinta. "Kici gaba da haquri qawata dan Allah mudage dai addu'ar nan komi yayi tsanani maganin sa Allah kinjiko?,,, nan momy umaima tayi ta dannarta harsaida taga tasaki jikinta sannan. riqo hannunta momy ni'ima tayi tace "nagode qawata sosai lallai kincika aminiya tagari banyi zaton raina zaimun sanyi ba saida kika mun tunasarwar nan ngd ngd,, bari na kawo miki abinsha",, dan dai kawai momy umaima taqara farantawa momy ni'ima rai yasa ta miqe tace a'a mije can insha kinsan nima ai yar gida ce,, tare suka hau sama acan suka zauna suka ida firar sai bayan la'asar sannan momy ni'ima tarako momy umaima har wajensu ummu hani lokacin harta tashi tana linkewa mamanta kayanta dana baffa,, daga nan suka wuce gida. Suna shiga kuwa wata mota na sawo kai cikin gidan, basu tsaya ba suka wuce ciki suka zauna falo momy umaimah ta dauki remote ta kunna tv takoma ta zauna kan 3 seater tadubi ummu hani tace "ummu hani na jeki debomun dambun naman nan na jiya wanda kikaimum naji dadinsa sosai fa d'iyata,,gskia zuwa yanzu ban haufin diyata koda nakaita gidan miji ta iya kominta na irin kalolin girkinmu dana koyar dakesu ko ummu hani na? Cikin kunya ummu hani tabar wajen da dan saurinta,, da 'yar dariyar momy umaimah ta bita tace aranta "ina ruwan ummu na badai kunya ba, sallama taji tana amsawa tareda duban qofa ganin hajia aina ce momyn hannat, a gaba sai hannat din a baya, sakin fara'a momy umaimah tayi tace "ah hjy aina sannunku da zuwa, yawwa hajia umaimah, zama sukayi tareda qara sabuwan gaisawa momy umaimah tace kin rigamu shigowa knn da inata tunanin qoqartawa naje wajenki nai miki bangajiya, nafita waje d'auko kaya"hjy aina tayi dariya tace "Kinjiki hajiya umaimah kayandama har sun qare na turamiki balance naki ma account tun jia kobakiji shigowarsa bane?" "a'a naji bndai duba bane tukunna cewar momy umaimah din. Hjy aina tace "kumamadai tayaya zakiyita yawo da wannan ciki haka Masha Allah ai kinyi nauyi harki iya zuwa wajena? ,, murmushi momy umaimah tayi tace "uhmm aikinsan anason excercise ga mai ciki sosai, hjy aina tace "eh hakane dawata ya wannan kuma, yanzun wane watane kike haihuwa? wannan ne koko? dan muje mu sissiyowa baby kaya,, kafin momy umaimah tace wani abu saiga ummu hani ta fito daga cikin kitchen din hannunta daukeda plate na danbun naman wanda ta xubowa momy umaimah din ta shigo falon ta ajiye a gaban momy umaimah din tace "mah Gashi" yawwa ummu hani na sannunki to, gaisheda hajiya aina ummu hani tayi wacce ta tsura mata ido taketa kallon ta, dan iya saninta dai batasan momy umaimah da wannan balarabiyan yarinyar ba cikin gidan nan .... amsawa tayi ta juya wajen hannat tace mata "sannu,, gani tayi hannat din ta daure fuska tana watsa mata harara a Kaikace,,, hakanan hannat taji tsani ganin aljanar yarinyar nan cikin gidan nan tasan yanda taketa wannan mugun zunzurutun kyawun mai dauke hankali ba abinda zai hana ta dinga yiwa mahabeer dinta feleqe dashi kuwa a cikin gidan , niko nace Allah sarki hannat kallon kitse kikewa rogo,,,ay ynda kikasan su sare junansu cikin gidanna haka sukeyiwa junsa kisan mummuqe bare har akaiga batun wani son burge d'ayan su. Ita kuwa ummu hani ganin yanda wannan budurwar ke mata kallon ukku sisi yasata aranta cewa "tofa ikon rabbu 🤔,??,,, minayi miki ke kuma to? Inban manta ba wannan shine gani na biyu danai miki ban kuma yimiki wani laifin ba bare?!" ba 6ata lokaci itama kuwa ummu hani ta mayar mata da irin kalan nata kallon ta miqe tsaye jin momy umaimah tace taje ga wayanta can sama a gudan dakinta taje ta d'auko mata. mafarin knn tabar wajen.... hannat ta bita da kallon mamaki...zuciyarta tace"lallaima,,!! wato wannan qaramar qaraman yarinyar har ta isa ta mayar mun da kallon rainin danai mata da tsana??!!, qutawa tayi ta gyada kai gamida maida qaton glass din idanunta tana cigaba da cizon yatsa a 6oye. sai lokacin ne momy umaimah tace ''aa hjy aina ba wannam watan nake haihuwar ba sai wata na gaba insha Allah". hjy aina da magana ke faman cinta cike cikin bakinta ta dafa qafan momy umaimah tace "keni ba wannan bama yanzun dai,, wannan buzuwar yarinyar hjy umaima a ina kika samota kuma? Nasanki da yaye yaye fa wlh,, "wannan wacce tabar nn wai kike nufi hjy aina? cewar momy umaimah tana Murmushi. "Eh ita nike nufi fa,,inji hjy aina din. Murmushi momy umaimah tasakeyi tace ''wannan ai ummu hani knn, muna zaune tare da ita anan tana tayani aiki su kuma iyayenta suna nan gidan qawata nan maqotanmu hjy ni'ima matar alhaji Muhammad aminin nuree na suna tayasu aiki da kulada gida suma, kama haba hjy aina tayi tace "ban fahimceki bafa sosai hajiya umaima ina kuka hadu da ita da itayenta kuma?? da zuciya day'a momy umaimah takwashe labarin komi ta fadawa hjy aina na ynda har su ummu hani da iyayenta suka hadu dasu kuma suka kasance a tare har ynxu. kama baki hjy aina tayi sannan tace "amman wlh hajiya umaima banta6a sanin kinada qaramar kwanya ba sai a yau din nan, zuba mata idanuwa momy umaimah tayi tace "kamarya yaya hjy aina?? qaramar kwanya kuma dani kamar yaya kuma? hjy aina tace "mm eh qaramar kwanya nace kamar yanda kikaji dai na fad'a,, haba haba hajiyata, kinsan kuwa yanda buzaye sukeda mugun sihiri kuwa? har kika iya ajiye wannan zuqeqiyar kyakkyawar yarinyar nan cikin gidan ki batareda tunanin komi ba? baki tunanin zata iya tai miki siddabaru irin nasu ta koreki cikin gidan ta aure miki miji? to wlh na rabaki marmaza marmaza ki kori buzuwar yarinyar tukun daga cikin gidanki tunkan ta zame miki qarfan qafa mai wuyar 6alluwa har sai an sare qafan sannan,,"!!! karaff wannan maganganun na hjy aina sai a cikin kunnen ummu hani,, batace komiba ta ida isowa wajen ta miqawa momy umaimah wayan bata jira komi ba ta juya da sauri2 tayi cikin dakinta. hannat tabita da kallon shegiya qwamma kibar gidanma wlh inda bana uwa da uba bane ko hankali na yafi kwanciya. da gudu ummu hani ta ida shiga dakinta ta fada bisa gado ta
Chapter 41 · 0% Book details