← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 109

Sashe 102

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*For your only xexen Fasaha novels group, all of you love you so much*❤ 🌊🌊🌊🌊🌊 🅿5⃣4⃣ 🌊🌊🌊 Dukansu mota suka shiga bayan sun sa inna indo itama nan suka nufi asibitin,, Suna isa aka shigar dasu d'aki nan aka fara dubasu ita inna indo targad'e tayi a yatsa yayinda shi kuma mukhtar aketa q'oq'arin yi masa d'auri a q'afa dan gaba d'aya sun karereye ihun sa dud ya cika wajen sabida d'aurin q'afar da ake masa dan wata futinannen azaba kawai yake sha, ganin haka nan take bash ya d'auki wayarsa yakira baban shi mukhtar d'in babu jimawa kuwa sai gasa yazo saman mashin dinsa shida Mustapa qanen mukhtar din,, su kuwa su dady mua'zzam suna zaune nan bisa kujeru mahabeer sam yakasa zama har yanzun zallar mamakin abinda mukhtar ya shuka masa kawai yakeyi amman babu komi yaje dan kansa nakasar ma daya samu kadan daga sakamakon wanda aka amincewa mawa knn yayi ha'inci, ya kuma godewa Allah da har gskia ta bayyana yy kuma alfahari da aboki na qwarai irin bash mai hankali da hangen nesa, shiyasa har gaban bash yaje ya zauna ya dafa kafad'arsa ahankali bash ya d'ago ya dubesa su ka yiwa juna wani murmushi, rungume juna sukayi cikin muryarsa mahabeer ke cewa "ngd bash ngd qwarai hak'ika ka cika aboki na gari Allah shi barmu tare,,, ''amunn" cewar bash dafe kansa mahabeer yy bayan ya janye hannunsa daga jikin bash yace "dole ne na dangana d'an iskan nan ga police ma bash dan bazan wai barsa haka ba inna barsa haka banwa kaina adalci ba nikega" girgiza kai bash yayi sannan kuma yace "kada kayi haka gifted ka barsa haka kodan ma sabida iyayensa ka qyalesa kawai Allah na nan ay" shuru mahabeer yy dole dai ya haqura badan yaso ba dan babu wata alfarmar da bash zai nema a wajensa bai masa ba, su dady ne suka qaraso wajensu suka zauna nan Dady mua'zzam yace "dudda abinda ya faru mahabeer kayi haquri kada kace zaka daukaka maganar nan dan nasan ka da zuciya kayi haquri sojana kamar yanda Allah ya saka maka ya fito mana da gskiar magana to kayi haq'uri dan lalurar da ke jikinsa ma ta ishesa ishara , taune lips d'insa mahabeer yy yace "naji dady amman kuma wlh narabu dashi har abada bashi ba wajen aiki na,, murmushi dady Muhammad yy yace "daman ai wannan ta rigaya data wuce shi kansa nasan ai kunya ma bazai bari yazo ba" "hakane kam gskia" cewar dady mua'zzam din shida bash,, duban Dady Muhammad dady mua'zzam yayi yace"amman aboki na naji ka ambaci sunan wannan tsohuwar daman ka Santa ne can da?" girgiza kansa Dady Muhammad yayi sannan yasaki ajiyar zuciya yace "tabbas na santa sani ma na sosai kuwa, itace wacce na taba baka labari mai aikin ni'ima wacce tatafi garinsu tun bayan b'atan mahabeer bamu qara jin labarinta sai yau din-nan fa da dalilin dalili na qaddara data fuddomu har Allah yasa kuma nayi *gam da katar* da ganinta kaga kuwa muddin ni'ima ta ganta nasan ba qaramin dad'i zataji ba a rayuwa dan sun shaqu shaquwa kam bata wasa ba kuma,, kan Dady mua'zzam yace wani abu saiga likita ya fito ya iso wajen yace "zaku iya tafiya gida da ita babar yanzun haka inda ba wani ciwo taji ba shi kuma yaron nan gskia zai yi wuyar yuyuwa koya warke qafafunsa bazasu cigaba da taka doron qasa ba dan gaba day'a qasusuwan sa sun karkarye a hatsarin nan kuma mun debi jininsa dan shima muyi tes....,,, dakatar dashi mahabeer yy yace "bamune danginsa ba mu kawai iyaka kawosa mukayi ga iyayensa can kaje kai musu wannan bayanin bamu ba" doctor yace "ok i don't know but no problem kwa iya tafiya din kamar yanda nace" haka su Dady sukayi balance sannan suka fito da inna indo tana fmn d'an d'ingisa q'afar tata har suka shiga mota suka nufi gida. falo suka shiga gaba day'a nan suka taras dasu annah har la okacin suna tare kenan amn wannan karon harda ummu hani zaune gefe daya tana riqe da baby manal cikin jiknta, amman kuma dud jikinta yai mata sanyi jin wai mukhtar abokin mahabeer ne yajaza wannan rigimar,, kai duniya ina zaki damu gskiya tai qaranci mutane babu tabbas sai d'ai d'aya na Allah. zaunar da inna indo mahabeer yayi, duknsu suna qara mata sannu, su annah sai kallon rashin sani dai suke mata,, da sauri kuwa dady Muhammad ya juya ya fice daga falon bai jimaba sai gasa sun dawo shida momy ni'ima, ai momy ni'ima na arba da inna indo kamar yanda dady Muhammad ya fad'a da sauri ta isa inda take suka riqe juna suna tsananin murna da farinciki dudda tsufan da inna indo ta qarayi amman hakan bai hana momy ni'ima shaida taba nan taken, momy ni'ima tace cikin hawaye "inna indo ashe munada rabon sake ganawa? inna indo ina kika shige ne? babu inda bamuje nemanki ba amman shuru gashi kuma bamusan garinku ba tun muna nema har muka haqura,, inna indo tana qoqarin bude baki tayi mgn sai kuma akaga ta fashe da kuka tana cewa "Alhamdulilla nagode Allah ni indo Aisha daban mutu ba batareda na gamu da mutanen nan na fad'a musu inda amanar su take ba, o'ni na gode Allah jalla wa azza,, zuba mata idanuwa kawai Dady Muhammad yayi shida momy ni'ima. d'agowa tayi ta dubi momy ni'ima tace "uwar d'aki na yau zan fayyace muku *sirrin b'oye* wanda ya jima da b'oyuwa sama da shekaru kusan nawa,, shin kokunsan cewa d'anku mahabeer yana raye bai mutu ba kuwa? cikin wata iriyar azababben razana suka fara magana dady Muhammad yace "inna indo mi...mim... mikike son cewa haka ne? gyad'a kai tayi tace "tabbas kuwa kamar yanda dai kukaji na fad'a muku haka ne, cikin wata muguwar futinannen bugun zuciya momy ni'ima tace "wa.. wa ya d'auke mana shi ne to inna dan Allah?! sannan kuma yana ina yanzun? inna indo tace "in bazaki manta ba aranar da aka dauke mahabeer nazo miki da magana kan cewa kisa ido sosai akan d'anki dan bn yarda da takun saqar hjy laria ba amman sai kikace a'a ga tunaniki na ta gyaru alhalin ni aranar naji abinda naji gameda suna son sace sa suje su kashe sa dan baqin cikin ita hjy laria din bata haihu ba,, inna indo na fad'in haka momy ni'ima ta kife wajen ta fashe da kuka tana dukan jikinta tana fad'in "minayi miki ne haka hjy laria da kika tsaneni kika rusan farinciki na? miqewa tsaye tayi zata fice da sauri dady Muhammad ya tarota tafara qoqarin qwacewa tana kuka take cewa "nika wlh ka rabu dani sai naje ta fiddo mum dud inda yaro na yake,, saida qyal yashawo kanta sannan ta dawo ta zauna tana cigaba da kuka, su kuwa su dady mua'zzam gaba day'a sun cika da al'ajabi kan abubuwan da suke ta faruwa dasu haka kamar almara. inna indo ta dubi momy ni'ima tace "ki sauraran da kyau uwar d'aki na yanzu koda kinje wajen hjy laria batasan inda yaro yake ba nice nan nasan inda yake danni ce nayi ceton rai na d'okesa nabar gidan dashi a ga6ar lokacin da suke neman cimma mummunan burinsu ni kuma na daukesa na kaisa inda nasan za'a basa cikkayiar kariya da kuma kulawa kamar kowane yaro. kamo hannuwanta momy ni'ima tayi tana share hawaye tace "Alhamdulilla inna indo dan Allah to ina yarona kika kaisa wlh kin tado min tshohon miki na jinake zuciya na kamar zata fashe tsabar duka da take mun yanzun haka" inna indo tace "bai hannuna tun lokacin dana daukesa nabar gida dashi na kaisa gidan marayu a nan na badasa nace musu zan dawo nan ba da jimawa ba in karb'esa, to koda na dawo gida naga anata bid'arsa ganin ynda hankalin ku ya tashi nikuma shiyasa nakasa jurar ganin hakan shiyasa a lokacin na fake da cewa zan tafi gida dan ban jurar rashin yaron kusa dani ku kuma sai kuka sauko kuka dinga tausana kan kada in tafi ammam dudda haka na dage akan dai lallai lallai inason zuwa gida gano babana da bai lpia nayi hakanne ni kuma dan in tafi in barku nadan wani lokaci in yaso sai daga baya in dawo in fad'a muku gskia lamarin da yasa nai hakan danku d'auki mataki to sai kuma gashi kuma dai a wansheka ren da naje gidan namu da daddare muna kwance kawai naji an daukeni an tura cikin wani qaton buhu an qulle an tafi dani an ajiye wani waje wlh nan naji ansa itace manya manya anata fmn dukana ina qulle cikin buhun tun ina iya kuka da motsi harta kai ga na gaza ko motsa hannuna haka mutanen da ban san ko su suwaye ba suka tafi suka barni jin wani day'a daga cikinsu nacewa dayan daga gani na mutu inda ga jini nan na fitowa a buhun kuma na daina motsi ma, wlh bansan inda kaina yake ba sai dai farkawa nayi na ganni a gida ashe da gari ya waye nan maqotan mu suka kwance buhun da nike ciki ganin nice yasasu suka gigice a rude suka kirawo babana suka shigar dani ciki, haka babana yaita mun magani tsawon shekara da shekaru dayake dud gab'ban jikina babu inda basu nakasa ba, wlh sai a hankali nafara iya zama harta kai ta kawo ina miqewa baba na na koya mun tatata harna fara d'an daddogara wa da kaina da sanda, da tafiyar tayi qwari nakuma samu lpia sai na bawa baba na labarin abunda ya faru dakuma yanda na dauki jinjirin naku shine a lokacin na nuna masa inason in zo nan birni wajenku in kaiku ku dauko yaronku a lokacin shikuma yace a'a bazai yarda in zo ba dan bai son nima ya rasani inda ni day'a ce a wajensa dan ya tsorata matuqa da labarin dana basa na hjy laria gani yake in na koma na fadi gskia kamar nima zata sa a nemi kashe nine, to nikuma dole na haqura dan bn iya sa'insa ba da baba na ba tun ina 'yar qaramata bare yanzun da mnyanta ta kama ni,, haka na haqura naita kulawa da babana dayake ya tsufa
Chapter 102 · 0% Book details