← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 109

Sashe 16

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

🌊🌊🌊🌊🌊
🅿1⃣6⃣
🌊🌊🌊
Maganar da d'an jaridar yakewa mua'zzam saraki ita mamaki ma kawai ta bashi gaba d'aya,
duban bayin Allahn dake kwance a wajajen ya sakeyi ga kuma matarsa itama acan kwance,
kawai bud'an bakin sa sai cewa musu yayi, "to sabodami harni zanfi qarfin ajiye iyalina a cikin bayin Allah musulmai,?
Siyo lafiyan zanyi knn?
kun mance damai bada lpiar ne?
girgiza kai yayi sannan yace
"ninan da kuke ganina nasha ban ban da sauran,
dan ban raina mafari, komin q'anqantar waje wlh zan iya kawo iyalaine wajen nima a dubamun su muddin jama'an Annabi na halartar wajen, ban damu sai inda keda fanka da eci ba, shiru ya danyi sannan ya ci gaba da fad'in "kutuna neman lpia ya kawo kowa a wajen nan bawai hutawa ba, dan lpiar itace kowane irin hutu na rayuwan d'an Adam muddin bakada lpia tofa jin dad'i bai ganka ba aduniyar nan, kuma nasan kunsan haka kuma,
wlh koda ace nine ke ciwon nan zan tsaya anan su dubani kamar yanda ake duba sauran, dan nasan inada compidence akan asibitin nan,
*barau dikko hospital* nasan yana kulawa da jama'a ynda ya kamata komin qaramin qarfinka zasu baka kulawa ynda ya dace bazasu banzatar da kaiba,
dan haka maganata ta qarshe shine kusani Allah d'aya na sani kuma shi ke bada lipa akowane wuri mutum yake bawai sai za6a66en waje ba".
dukkansu jikinsu yayi sanyi da maganar mua'zzam saraki dan haka kowa ya sauke abin maganarsa daga garesa cikin karewar gwiwa tareda qara tabbatar da gaskiar abinda ya gama fada ynxun a cikin bakinsa,
wani daga cikin sune yayi q'arfin halin cewa "am to ranka shi dad'e zamu iya tsayawa anan har sai munji sakamakon ciwon mai d'akinka na samun sauqi dan masoyanka su gani kazo aikin alheri kuma ga ynda ta faru da iyalinka?
d'aga masa hannu mua'zzam saraki yayi yace "banda buq'atar hakan,,, kuma inda hali ku goge vidio d'in nan da kuketa d'aukanmu tun d'azun, ban son ni innayi aikin alheri sai an gwadawa duniya kowa ya gani, na roqeku daku goge dudda nasan dan kasuwanci da son qara daukaka kukeyin sa,
tsabar qwarjini dayai musu ne yasa kowanensu ya danna wajen gogewa kawai suka barshi a matsayin zasu buga labarin temakon majinyan da yayi a asibitin a newspaper dinsu inda aikinsu ne hakan,
umartar mahabeer yayi daya bawa kowanensu bander bandeer suma,
nan da nan kuwa ya cika umarnin dadyn nasa, sukuwa 'yan jarida gani suke riba biyu aisu gaba ta kaisu ma a zuwan asibitin dan d'aukan rahotan,
shiyasa basu q'ara d'aukan wani dogon lokaci ba suka tafi.
dafe kansa anan wajen mua'zzam saraki yayi yana adduar Allah bawa umaimahn sa lpia,
ba'a jimaba doctor lurwan ya fito daga room d'in da aka shigar da umaimah fuskarsa a sake cikin fara'a ya iso wajen,
mahabeer ya zuba masa ido a tun a daga nesa, zuciyarsa yaji ta d'anyi sanyi dan ko ba komi yaga alamun nasara akan fuska ta doctor lurwan d'in.
yana zuwa gaban mua'zzam saraki yace "ranka shi dad'e muje office danjin bayanin komi,
suna shiga office d'in suka zauna mahabeer ya zauna akan kujerar dake setin dadyn nasa yayinda doctor lurwan ke fuskantar su.
yafara magana da cewa "ranka shi dad'e iyalinka ta farko lpia amman ta koma barci ynxu sakamakon q'arin ruwa da muka jona mata sannan kuma munyi kowane irin gwaje gwaje ga ita mai d'akin naka har fitsarinta mun d'iba munyi reaserching akai kaga result d'in da muka samu nan ma,
nan ya isa wajen wata na'ura dake wajen yayi wasu danne danne saiga wata farar paper ta turo a qasan na'urar tasu ta aiki ya dawo ya zauna tareda miqawa mua'zzam sarakin result d'in shi kuma ya kar6a tareda fara dubawa,
abinda ya gani ne yaji jikinsa na wani irin tsumammiyar tsuma ta kyarma a lokacin, nan take farin ciki ya wani iriyar baibayesa,,, ganin abin yakeyi kamar a mafarki sai faman qara maimaita karanta takardar yakeyi wai yau shine Allah ya azurtasu da samun rabo na ciki abinda suka jima suna fata da roqon Allah shine yau Allah ya dubesu da idon Rahma ya basu abinda dukiyanka bazata ta6a siya maka shiba komin yawanta,
baiyi aune ba yaji wasu irin d'umammun hawaye nabin idanunsa suna fitowa na farin ciki.
wai yau matarsa keda 6oyayyen ciki har na tsawon wata 6 batareda sun sani ba kuma?
Kai shiko yau wace irin iriyar godia zai nunawa Ubangijin nasa yau?
Kawai saiya daga hannayensa a sama dukkansu hawayen murna na q'ara fito masa ya sunkuya qasa tareda yiwa ubangiji sujada sai fad'in Alhamdulilla ya Allah kawai yakeyi tareda kirari wa sunayen Allah kyawawa.
fiddo idanuwa mahabeer yayi da sauri ganin hawaye nabin idanuwan dadyn nasa bayan ya koma ya zauna yayinda fuskarsa ke kan qara kallon takardar da likitan ya bashi.
cikin mutuwar jiki mahabeer ya taso ya dawo wajen dadyn nasa ya leqa kansa ya fara bin takardar da idanuwa shima, ganin abinda ke rubuce shima ya basa mamaki dan tun tashinsa a gidan nasu bai ta6a ganin wani q'aramin yaro ba bayanshi,
sai ynxu ne yasan ma'anar zubar hawayen dadyn nasa na farinciki ne ba komi ba.
rungume juna sukayi shida dadyn suna murna,,, doctor lurwan kuwa sai binsu yake da kallo shima yana fara'a,,
Hamdala dady mua'zzam saraki kawai yakeyi bayan sujada da yayi ta nuna farin cikinsa ga mahalicci,
lallai sad'aqa da temakon bayin Allah ba q'aramar turba bace mai kaiwa ga gaci ba a rayuwar d'an Adam kai harma bayan ransa zata bisa ta zame masa garkuwa a ranar sakamako.
Mua'zzam saraki ya rasa inda zaisa kansa dan murna da sauri yake fad'in cewa "doctor lurwan haq'iqa naji dad'in wannan albishir d'in naka gareni dan haka na baka kujerar mecca 10 ta wannan shekar a matsayin tukwicin ka,
washe baki doctor lurwan yake tayi yana fad'in "godia nake ranka shidade, aransa yake fad'in yau kam ya dace da wannan rana yaushi washar kam.
Har d'akin da momy umaimah take kwance doctor lurwan ya kaisu lokacin ta farko, amman sai doctor lurwan yace ya kamata abarta ta qara hutawa sosai dan qwarin jikinta ya dawo normal duka.
bayan fitar doctor lurwan mua'zzam saraki ya matsa kusada ita ya zauna yace muna qara godia ga Allah wifeyna dayai mana irin babban wannan kyauta a wannan shekarar wacce ta fiyemun dukiya ta duka,,
Kallonsa kawai takeyi takasa gane nufin nasa, duban mahabeer dady mua'zzam saraki yayi yace "zoka fad'a mata abin farin cikin daya samemu my son,
yayi maganar cikin tsananin q'aruwar Murnar tasa,
har wajen kanta mahabeer ya duq'o ya rad'a mata da cewa "momny na nanda 3 months zaki bawa dady baby ni kuma q'ane a gareni haka doctor yace"
jitayi maganar kamar a mafarki abin wasu hawaye taji suna neman sulalo mata a fuskanta itama da sauri ta miqe zaune ta shige jikin dady mua'zzam saraki tana hawaye,
a zuciyarta godia kawai takewa ubangiji Allah babu adadi,, cikin rawar murya ta fara fadun "nuree... nuree kawai a take fad'a jikinsa shikuma ya
qara rungume suna dariyan murna, a fili suke qara bayyana hamdala ga buwayi gagara misali mai kyauta asanda yaso batareda tursasawa ta wani abin halitta ba,
Kwantar da ita yayi tareda shafa kanta ya sumbaci bakinta cikin so da kulawa ta tsohuwar soyayyar tasu,,,
shi dai mahabeer cikin burgewa yake kallon iyayen nasa soyayyar tabbas bata tsufa ya shaida hakan tuni batun yau ba.
lumshe idanunsa yayi sannan ya bud'esu lokacin dayaji dadyn nasa nace masa ''zaije gida ya d'auko annah ya jirasa yanzun zasu dawo,
"to dady ai kyau ace kabari ni zanje na kaiwa annah ta wannan surprise d'in" ya fad'i maganar a shagwabe kansa na mai lwangwabe,
"cikin faraa mua'zzam saraki yace "nima ina son inga kalar farin cikin da kagani a fuskar mamanka lokacin da ka fad'a matan ynxun to nima inason inga irinsa a fuskar mahaifiyata koya kace my son?
"dhat is true dady adawo lpia ina nan muna jinya nida momyna"
ya fad'i hakan tareda kwanciya gefen gadon da mommy umaimahn taken.
sukuwa iyayen dariya sukayi masa. ahaka dady mua'zzam saraki ya fice zuciyarsa cikeda farin ciki uwa ya zuba ruwa qasa yasha.
mommy umaimah ta dubi mahabeer tace "ina son shan ruwa mahabeer dina, da sauri ya miqe tsaye har Bluetooth din kunnen sa na fad'owa saman jikinsa yace
"to momy bari naje na samo miki swean water a nan waje ko,
girgiza kai tayi tace
"na zartsi nake son sha ay son"
to momy ina zamu samu na zarts,,,, maganar tasa ta katse da dawowar doctor lurwan cikin d'akin tun bayan futarsa dazun, anan yaji abunda momy umaimah tace ta so.
mahabeer yace
"doctor i don't know place,,, kokasan wajen da zan samu irin ruwan da take son sha d'in anan kusa sainaje?
doctor lurwan yace "eh inka fita anan ka zagaya ta baya akwai fanfon mono wajen wata darbejiyan icce zaka samu anan"
"ok doctor thanks bari naje tom"
anan ya fita yabar doctor yana qara gyarawa mommy umaimah drip d'in hannunta.
ta inda doctor ya kwatanta masa tanan yabi wajen ba hayaniyar komi tsit sai wata matashiyar yarinya daya fara hangowa daga nesa wacce sam sam baiga really fuskarta ba, sakamakon ta rufe rabin fuskar nata,
sai dai gazar gazar d'in baqaqen gashin idanunta da gashin girarta kawai ke bud'e dayake tasa wani baqin qyalle mai kauri ta rube rabin fuskar nata, tana duq'e tana linke kayanta data gama wankewa sun bushe tanason komawa cikin d'akin dan bata sani ba ko mamanta na son wani abun kuma.
cikin tafiyar takunsa na qasaita ya iso wajen yaja ya tsaya gabnta batareda yace uffan ba dan yarasa ta ina zai fara mata maganar ynda kan famfan yake dan ba wai sanin kansa yaiba,
jin motsin taku a bayanta yasa ta jiyo da fuskarta a hankali dan tanada tabbacin cewa babu kowa a wajen face ita dan tun d'azun sauran mutanen wajen suka gama nasu aikin suka tafi itama dantana sanyin jiki ne na aiki shiyasa takai har yanzun ,,,,,
ganin mutum tayi a bayanta a tsaye, ita tsoro ma taji hakan yasa da d'an sauri ta miq'e tsaye tareda kwasar kayanta ta matsa daga wajen taci gaba da linkin kayan ta batare da ta qara kallonsa ba.
shi sam hankalin sa ma bai wajenta ta sosaia lokacin, shi babban matsalan sa yanda ake samun ruwan su fito baisan ynda ake yiba, shiyasa ya tsaya wajen yana mai qara nazartar ynda yk dnbaisan ta ynda zai tuqa monon ba ya kawo ba,
shi sam baida ra'ayin kan wata magana ta dinga had'asa da matan hausawa dinnan dan yatsani rainin hakali shi a rayiwar sa sam,
amman ganin tsayuwar bazatai masa ba yasa ya daure ya sauke kad'an daga cikin fad'in ran nasa dan tunowa da momyn tasa nacen na jiransa ya kai mata ruwan tasha,,
da wani irin sautin takun tafiyarsa na qaqqarfan namiji ya qara qwaqqwaran taku guda 5 sai gashi a bayanta still ya sake tsayawa hannayensa a wannan karon sanye cikin aljihun jeans d'insa kamar dai d'azun,
Wannan karon kuma bata juyaba yi tayi kamar batasan yana wajen ba dan ta shaida mutum ne ynxu ba Aljan ba sabida ganin datai masa in short time,
a yatsine ya fara maganar tasa da cewa
"ke! ,,ina buqatar ruwa a cikin ta nan wajajen tayaya zan iya samun su?,,,
ummu hani tajisa sarai amman jin yanda yake maganar tasa cikin nuna isa da son ai masa abin kan dole ynda yake so yasa tayi kamar bata jishiba,
ahankali taji ya sake maimaitawa nan ma tayi burus dashi saima qara saurin qarasa linke rigar baffanta datayi ta miqe tsaye ta dauki sauran kayan tana shirin wucewa abinta batareda ta qara dubn gefen da yake bama sam.
shikuwa ganin tana shirin tafiya gashi kuma baisan yaya zaiyi ba indai ta tafi tabarsa awajen kan dole yasa ya d'an sassauko da muryar tasa qasa yace "mamana keson ruwan ne,, kuma ma bata lpia shiyasa please ki taimaka baiwar Allah!,,,,
jin ya ambaci mamarsa ce keson ruwan bata lpia da kuma temakon da yace yasa taja ta tsaya cak a wajen,,,
Chapter 16 · 0% Book details