Sashe 42
Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
saki kuka mai zafi gamida cin rai,, saida tayi kuka sosai sannan ta tashi zaune tare da sanya kanta cikin cinyoyin ta tace a fili "wacece ke wannan matar?? Ban sanki ba? ban taba ganin kiba sai a yau, gashi kinzo kina burin rushe mana farin cikinmu Nidasu baffana na ganin mun samu kud'aden da za aiwa mamana aiki dasu ta samu lpia mu koma garinmu, yanzu in kika sa bayin Allahn nan suka koremu muka komsa garinmu to mimike dashi dazamu sayar mudawo a nemawa mamanmu lpia nata??!!!!!" sake fashewa tayi da kuka snn taci gaba da magana cikin yarensu na buxaye da cewa "Allah kawomana d'auki kacece rayuwan mamana daga ciwon nan nata ka ida cika mana burunmu ka bata lpia, ya Ubangijinmu Allah ka temaka mana!" tana maganar ne kanta na bisa cinyarta idanunta a runtse suke, kuma har ynxu hawaye basu bar sauko mata ba,, Acan falo kuwa momy umaimah jin abinda hjy aina tace yasa sam 2 ta kasa magana tayi shiru sai idanuwa data zubawa hjy aina tana kallonta kamar wacce take son karanto wani abun muhimmi ne daga gareta mai matuqar muhimman cin gaske kuwa.....