← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 109

Sashe 6

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

🌊🌊🌊🌊🌊
🅿5⃣
🌊🌊🌊
*Z* ama yayi a inda ya tashi yana mai furta "bismillahe ya Allah"
da sauri Ummu hani ta matso tasa hannayenta biyu ta d'ago mamar tata ta zauna gefenta ita kuma,
tareda rungumeta a 6arin jikinta na dama, a haka baba kad'do ya d'ora mata qwaryan maganin a bakinta. binte ta fara sha har iyakan gejin da ake shan maganin.
Komawa tayi ta kwanta ta rufe idanunta.
Minti 5 da shan maganin nata taji
d'an zuwa isowar sauq'i a lokacin, taji zuciyar ta d'an lafa mata, hatta kuma da yawun ta dake tsinkewa a bakinta na kamar zatayi amai na dud in ciwon zuciyar ya motsa mata to yanzun taji ya lafa mata mafarin knn ta daina motse motsen ciwon, numfashinta ya fara dawowa dai dai.
Lura da haka da Ummu hani tayi da baffanta yasa su jin dad'i a ransu.
Da sauri Ummu hanin ta shige jikin Maman nata tana dariya mai tartare da murmushi Amman Sam takasa furta ko *A*.
Murmushi kad'do yayi shima sannan ya q'ara duban tilon 'yar tasu d'aya mai tsananin tarbiyya da girmama na gaba, ga ilimi dan tasan hadissai da dama gashi kuma tuni ta sauke q'urani wajen sauka 5,
dan a yanzu ma tana hadda ne ta kusan izu 52 ma,
Sannan ta fannin boko ma da yake lokacin an bud'e musu makarantan frimary da secondary a q'arqarar tasu Suma basai anje can birnin nasu yamai bama,
inda yanzu dai ilimi yazaga ko ina cikin duniya bawai sai za6a66en waje ba kawai.
A yanzu haka ma ta kammala frimary ta shiga secondary aji 5 knn take a yanzun.
Allah yai mata q'walwa sosai sosai kuma.
dayake dama dud makarancin q'urani babu wani karatu a duniya dazai layance masa yafi qarfin sa,
speak koyaya kai mata mgn dashi zataji kuma zata mayar ma sai dai in bataga damar mayar maka ba to wannan kuma fa.
Sai dai a ganinsa babbar matsalar da yake ganin ta addabi 'yar tasa shine rashin mgn, dud In kai mata mgn tofa kan ta maidoma amsarta zata d'au tsawon lokaci kuwa.
zakayi tsammani ma bataji ba.
Hatta su knsu iyayenta d'in sunma Riga sun saba da wannan halayyar nata gaba d'aya.
Sun lura hakan datake yi bawai sa kanta bane a'a abin a jinin jikinta yake tun mafarin farko.
Ita koda ace zata wuni tun daga wayuwar gari zuwa dare batai mgn ba hkn bazai ta6@ damun taba. d'abiarta ce hkn ita knta tasani kuma,
ta shiga jikinta sosai tun tashin ta haka tk shiyasa mutane ke mata kallon miskilar mace ta qin q'arawa.
amman in taso dan kanta taga dama takanyi magana jefi jefi ba laifi,
a nutse take komin ta a sanyaye haka habitat nata yake ita.
Sake dubnta kad'do yayi yaga ta shirya cikin uniform d'inta na makaranta yace
"Ya yau ne bazakije naku tehare
(wajen karatu)
D'in naku ba Ummu hani?
Tashi tayi ta je ta d'auko wata jikkar buhu q'arama.
wato irin ta 'yan makarantar nan mai dogon hannu.
da littafin ta wnda baifi 7 ba a ciki sai abin rubutun ta sannan ta dawo ta duq'a gefensa tace
"Baffa na shirya ma ay,
na tafi to saina dawo"
"Yawwa tabarat
(d'iyata) ta kaina, Allah shi kiyaye kinji?"
Saida ta q'ara kallon fuskar mamanta taga ta samu yin bacci sannan ta miq'e tsaye tace "Ameeen Baffa."
Daga haka ta wuce ta tafi.
Tana fita ta shiga gidan q'anen baffanta mai suna baffa indeh, tana shiga ta iske q'awar tata nahee wato 'yarsa.
tana shan fura wacce tasha nono kindirmo tayi haske sosai furan gwanin sha'awa.
Sam Ummu hani batayi niyyar zama ba amman ganin 'yar gidan nata kuma sabon damu
(fura da nono),
yasa ta zauna ta d'auki d'ayan ludayen furar ta soma sha itama.
Nahee ta dubeta tace "Ummu hani
Yau nazata ai ba zamuje tehare bane? dan naga har rana ta d'aga.''
Saida ta shanye furan dake cikin bakinta sannan ta dago fararen idanunta dasika dawo normal izuwa yanzun sakamakon ganin umman tata ta dawo lpia hnkalin ta ya kwanta.
ta dube nahee tace
Timiditen(qawata)
Mizai hana kuwa?
Kawai dai nayi kulawa ne da mama ne shiyasa na makara gun biyowa miki"
tana gama fadan hakan ta tashi tsaye.
tashi tayi tsaye itama naheen.
lokacin nahee ta maida furan d'aka mamar nahee ta fito daga d'aka ta bawa nahee naira 20 Ummu hani ma 20 kamar ynda ta sabar musu kullum. anan Ummu hani ta gaisheta suka wuce suka nufi waje.
Sukayi hanyar makarantar.
nahee nata mata zuba ita kuwa sai dai tayi gum...
dan inta bata masa tofa wata amsar bata samuwa,,, shiyasa dole nahee ta gaji da surutun nata tayi shiru ta koma masife Ummu hani tana cewa
"Ay dama gaskiar sahee datake cewa Dan kinga kinada kyawu shiyasa kike mana yanga mtss😏.
Muma ay munada kalan namu kyan ehe,,
Jin har lokacin Ummu hani taqi tankawa yasa tace
"Timiditen Nayima shiru bazan q'ara tanka kiba nima inda abun naki nima yau ya motso a kaina.
ummu hani kuwa ko a jikinta saima murmushi datayi kawai ta q'ara gyara zaman jikkarta a kafad'anta tana mai q'ara gyara farar safar hannunta irin ta garinsu mai raga raga d'in nan.
a haka har suka isa tehare d'in nasu....

Xayyneb💤💤💁🏻‍♀
[10/11, 2:44 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb 💤💤

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.
Chapter 6 · 0% Book details