← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 109

Sashe 88

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*🌳impacting valuable knowledge and Entertainment is our concern🌳*. 🌊🌊🌊🌊🌊 🅿5⃣0⃣ 🌊🌊🌊 Annah ce ta taso daga wajen data gama sallar tata ta nufosu kenn saiga dady mua'zzam sunzo shida dady Muhammad da momy ni'ima sun shigo tareda sllma, suka zauna bayan sunwa su annah yamai jiki, jigum sukayi suna kallon ummu dake a kwance ido rufe sai shi mahabeer kuma da keta faman sakin ajiyar zuciya yana jikin momy still,, dady mua'zzam ne ya matsa tareda d'agosa suka miq'e tsaye ya dubesa yace "haba sojana ya zaka tashi hankalin ka kan qaddarrarriyar qaddarar da Allah ya nufemu da ita tuntuni kayi ehm? kaga kayi haquri a halin yanzu Ummu hani addu'ar mu kawai take buq'ata bakomi ba, bakazo ka tasata gaba kana kuka ba kayi haquri insha allahu matarka zata samu sauqi kaji ko?,, saddar da kansa q'asa mahabeer yayi yana goge jiqaqiyar fuskarsa yana cigaba da ske ajiyar zuciya nan da nan yaji take masa duka fat! fat! fat!. dady Muhammad yace "haquri zakayi mahabeer zata tashi insha Allah,,, cikin wata kad'uwar muryarsa yace "to dady na daina,amman nan d'ina ke mun beating sosai shiyasa ,yayi maganar yana nuna musu saitin zuciyar tasa da hannunsa, Dady muhammad ya dafa kafadarsa bayan ya taso daga inda yace "sorry kadinga addu'a kaji ko? Insha Allah zai bari" a hankali ya dagawa dadyn kansa alamun to. momy ni'ima kuwa tana gefen momy umaimah takasa bawa mahabeer baki ita kam kamar ma tayi kuka takeji tsabar tausayin dake ratsata nasu, zaunar da mahbeer dady mua'zzam yayi ya dubesa sosai yace "amman yaya akayi ka bari matarka ta tafo tunda london ita kad'ai haka? annah tace "yawwa nima kam abinda niketa son naji kn,,,, d'agowa da kansa daga saman qasan mahabeer yayi ya dubi dadyn nasa yace "wlh ban san ta tafoba dady naje raka su bash airport ina dawowa naga bata gida,,....!! kasa ida maganar yayi yasa hannayensa ya rufe fuskarsa yanajin wani d'aci d'aci daga can cikin maqoshin sa sosai. dady mua'zzam yayi shiru sai dady Muhammad ne yace "k to gaskia dawani abu kam,, annah tace "hakane mudai ajiye maganar har Allah yabawa ita ummu hani din lpia in-yaso maji komi daga gareta na dalalin tafowar nata hakan. shiru sukayi daga nn doctor lurwan ya shigo ya qara dubata sosai sannan yaqara tabbatar musu da insha Allah zata farko nan bada jimawa ba dan alamun hakan sun nuna daga jikinta daga jikin na'urar oxygen d'in nata,, sunyi murna sosai dajin hakan kuma. mahabeer kuwa duqar dakai yayi dan kawai jiyake inama za'a d'ibi lafiyar dake jikinsa asawa ummu kota samu lpia itama,, shi abinda ke matuqar ma daure masa kai yanda akayi ta baro gidan nasu kma harta iya kawo knta nan gida tomi yafaru haka ne lokaci daya? anya kuwa umnu tana d lapiyar brain? tambayar da wata zuciyarsa tai masa knn,, saurin girgiza kansa yayi tareda runtse danunsa a can cikin zuciyarsa yace "noooo ummu lpia nata lau danni bntaba ganin akasin hakan daga gareta ba,,,, wata zuciyar tace "to inba hakan bane kuma miya faru?? hakanan yaji kuma gabansa ya buga batareda yasan dalilin ba kuma,, jiyayi bakinsa yana motsawa a hankali yanaiwa ummu add'uar samun lpia,,, s dady Muhammad sai bayan la'asar sannan suka tafi annah ta dubi mahaber daya sa ummu hani a gaba ko matsawa baison yi dn rayuwarsu ta baya kawai yake tunanowa na tun farkon had'uwarsu har kawo rayuwarsu ta london annah yaji tasa hannunta ta tab'osa yayi saurin dauke idanunsa afuskar ummuhani da sukayi jajaye ya saukeso a kan annah,, annah tace "yakamata kaje kayi la'asar kaima kaga har 5 na niyyar yi,, jiyayi bakinsa ma kansa yai masa nauyi daman abinka da marar son fiye mgn shiyasa kawai ya tashi ya fice daga room din. momy umaima ta bisa da wani iriyar kallo cikin tsananin tausayawa dan tana lura dashi tun zuwan nasa bai iya qoqarin sa komi ckn bakinsa ba hr ynzu, annah ta dubeta tace "amman kuma umaimatu shin ke a maganganun da yaron nan yayi na gameda lalurarsa ke baki fahimci komi a ciki ba?? gu irgiza kai momy umaima tayi tana kallon ummu dake kwance tace ''a'a wlh annah ban fahimci komi ba wani abu ne? tagumi annah tayi tareda q'ara d'ora hannunta q'asan habarta fuskarta na kallon qasa sannan ta fara magana da cewa "niko dai gskia tabbas iriyar wannan matsalar ta mahabeer har tasa na tuno mai gida na Allah ya jiqansa da rahma lokacin yana raye ya tab'a samun ainahin iriyan cutar sanyin nan irinta yaron nan,, a lokacin shima ya shiga damuwa na ganin kamar yana zaluntata ne yana qwarata ata wannan fannin,,to ni kuma alkunya tasa nike gwada masa babu komi dudda kuwa ina q'waruwa d'in nima sabida rashin qarfinsa ta wannan fannin to cikin ikon Allah da Allah yanufa qarshen matsalar tazo sai yaje ya fadawa kakarsa lalumo itama Allah ya jiqanta da rahma nanta zo har gida taita mana fad'a akanmi zamu zauna da babban laluri irin wannan bamu fad'a ba an nemo magani ba inda Allah yace tashi in temaka bawa?, nan mukayi shiru babu wanda yai mgn sai bayan ta fita ne na nuna miyasa yaje ya gaya mata hakan sai "yace bazan iya zaunawa ina cutar dake ba qwamma in fadawa ita din kaka wataqil ko Allah zaisa mu samu mafita,, shiru nayi kawai danni kunya ma yasa naji mgnr dayakai batun nan ga magabata,, in fad'a miki umaimatu washe gari ina girki na tuwon amalo da rana saiga kaka lalumo ta shigo hannunta daukeda wata baqar leda nan na shimfida mata tabarma tsakar gida muka zauna naga ta kwance kullin ledar nan tafara fiddo wasu ganyayyaki na gargajiya ta ajiyesu qasan tabarmar ta dubeni tace "umaimah kinga wannan itace ake kira da *alyara* wannan kuma sunansa *cindazugun* sai wannan kuma shine *sassaqen zogale* wannan shi kuma *sassaqen lalle* sai kuma wannan 'yar jan kanwar itama kin ganta ko? Na "ce eh kaka na ganta" tace "yawwa to nasan kunada jar dawa to zaki wanke jar dawar nan saiki shanyata ta bushe sai kisa 'yar citta cikinta kibada shagon eshay a niqo miki ita in an niqota ki tankad'eta tass to garin ne zaki dinga d'ibarsa kina damawa da ruwan magun gunannan da kika dafa kina bawa mai gidanki yana sha, sai kuma wannan man zaitun ne da kuma man kanamfari dana tafarnuwa dana hulba sai wannan d'an miski shima zaki hadesu waje daya in yazo ki basa kice injini ya dinga shafasu a gabansa to komi zaiyi sauqi insha Allah, ke koda ace mace mai fama da lalurar sanyi tayi hakan zata samu lpia da yardar mai sama'u" niko shiru nayi ina kunya nai ma kaka lalimo godia haka kaka lalimo ta tafi, cikin ikon allah ba'a qulla wata daya ba da fara amfanin sa da magungunan nsa nan wlh ya warke sumul lpia kamar dama can da lafiyar sa a jiki har Allah yasa muka samu rabon mua'zzam dayake Ubangiji Allah yasa mai gidan nawa alhj saraki bamai yawancin kwana bane saiya rasu kuma yabarni da dumbin alhinin rabuwa da mutumin kirki gwarzo mai tsayuwar daka akan iyalinsa,,, annah na kaiwa nn ta fara share wasu hawayen dan famin ciwon nata data famo na tunowa da maigidan nata saraki, sannan tasake dubn momy umaima tace "zanwa mahabeer irin wannan had'in magungunan shima insha Allah kuwa da yardar mai! sama'u zai samu lpia ya dawo cikakken namiji shima kamar kowane namiji, dan da hr na sarai cikin satin nan zanje gida katsina amman nafasa sai ummu hani tasamu lpia sannan sosai" momy umaima taji dadin hakan kuwa itama, suna gama sallar magrib lokacin dady mua'zzam yadawo suna dan taba magana sama yayinda mahabeer shida momyn suna zaune gefen ummu wato sun sakata tsakiya su kuma babu mai cewa komi tsakaninsu gwamma momy umaima wani lokacin ma tana dan magantuwa a maganar su annah,, qara ware idanunsa mahabeer yayi dake kan fuskar ummu hani daya zuba mata idanun nasa tuntuni yana kallon ta batareda yayi qi oqarin janyewa bakuwa, gani yayi ta fara motsa idanunta qasa qasa zuwa can yaga ta budesu tarr tana kallon sama da sauri ya matso gareta yana qwalawa su momy umaima kira cikin rawar murya ta murna da cewa "momy mm... annah dady ummu ta farko,..! aida sauri suma suka qaraso wajen lokacin ummu harta samu ta miqe zaune da taimakon mahabeer din daya dagota da hannayensa,, su annah hamdala kawai sukeyi cikin tsanani murna. sai fmn sannu suke mata ita kuwa sai binsu take da idanunta, ahankali tayi qoqarin sa hannunta danta zare oxygen din dake fuskar nata mahabeer kuwa yayi saurin riqo hannunta yasaka idanunsa cikin nata tareda gurgiza mata kansa alamun a'a kartayi saurin yin hakan,wani kallota watsa masa cikin qarfin hali kuwa ta fuzge hannunta daga cikin nasa sannan ta koma ta kwanta tareda lumshe idanunta, sam mahabeer bai damu ba akan qwace hannu ta datai shi asali ma yadauki hakan ne abisa abunda ke damunta na ciwon datayi qoqarin cirewa shi kuma ya dakatas da itan, cikin Jin dadin farfadowar nata dady mua'zzam ya je yakirawo doctor lurwan suka dawo dakin tare,, cikin sauri doctor lurwan yaqara duddubata yaga komi normal hatta numfashinta yadawo lpia lau mafarin knn daya janye mata oxygen din tareda sake qara daura mata drip na ruwa ya tsira wasu alluran magunguna a ciki sannan ya juyo ya dubi dady mua'zzam yace "Alhamdulilla alhj komi normal ynxu nasa mata qarin ruwan nema danta samu qarin qarfin jikin nata dan zuwa gobe ma insha Allah muna sa ran ko iya sallamarta ma, ''Allah shisa to doctor cewar su dady mua'zzam din,,, da doctor lurwan zai fita kuwa saida ya dan saci kallon ummu hani da wannan nataccen kallon nasa sam ita batasan ma yana yiba danta runtse idanunta gam kamar mai barci, mahabeer ne kawai ya lura da kallon dayake matan yakuwa danqara masa harara na lamun nan ba kalar wajen wasan yara bane kama kanka da gabanka, aiko da sauri doctor lurwan kuwa yaqarashe ida ficewa daga room din, da wata iriyar harara mahabeer ya bisa tareda jan wani dan siririn tsoki, ahanka yace "banzan sakaran mutum kawani zubawa feadeer wasu ido mtsssss,, su annah sunzata ummu hani bacci takoma shiyasa suka tashi
Chapter 88 · 0% Book details