← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 109

Sashe 14

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

🌊🌊🌊🌊🌊
🅿1⃣4⃣
🌊🌊🌊
basu d'auki wani dogon tafiya ba sosai suka iso *barau dikko hospital* d'in,
sun firfito dukkansu a motan knn sukaji daga bayansu ta gefen titin ana musu horn alamun su tsaya,
su a lokacin ma suna qoqarin shiga a cikin asibitin dan tsayawa mu'azzam saraki yayi kadan yayinda mahabeer da momy umaimah sukayi gefe,
a bazace kuma cikin tsabar mamaki mu'azzam ya qarasa kusa da alhajin daya fito cikin motar wacce ake musu horn a cikinta.
suka rungume juna cikin fara'a.
mutumin yace "haj mu'azzam saraki kuyi mana afuwa mun san mun muku lefi dan shekaru da yawa bamu wai wayeku ba,
sai alokacin mu'azzam saraki ya samu qarfin gwiwar yin magana yace
"wlh kuwa kai dai haj Muhammad ka mancemu kawai zakace a rayuwa, sai kace ba tare mukayi childhood namu ba,?
sannan ga karatun mu da muka yisa a tare tun daga primary har kuma zuwa secondry?
amman ka 6oye lokaci daya kwata kwata har nagaji da try number ka wlh haj Muhammad,
saifa danaje can gidanka nake tambayar masu gadin nan suke fada mun baku qasar, sunce second madam dinka hjy ni'ima ne keba lpia?.
Alhj Muhammad yace "eh wlh kuwa, kasan tun shekarun baya din nan da Allah yabamu rabon haihuwar a duniya bayan dogon lokacin da muka shafe muna neman ta, sai kuma bayan Allah ya bamun ne muka neme jinjirin nan dare daya wlh muka rasa shi, tofa tun lokacin haj mu'azzam ni'ima bata qara lpia ba kullum ciwo sabo yake komawa takai ta kawo wlh sam ni'ima bata iya cin abinci ynda ya kamata, nan da nan ciwo ya rufeta ko numfashinta baya fita ynda ya dace, asibiti mun je 2 amman aka kasa gano taqamaiman matsalan nata dole muka je mecca can wajen danginta anan muka samu wani qwararren doctor ya fara dorata kan magun guna, cikin ikon Allah ta fara dangana ta hnyar adduo'e da muke xuwa munayi mata dare da rana cikin ka'aba.
tofa bayan dan lokaci jikin ya dawo normal sai kuma taqi ta biyoni gida nijeria, wai ita nan wajen iyayenta zata zauna,, wlh haj mu'azzam a hakan ta kafe kan dole na qyaleta dan nasan hakan bai rasa nasaba da rashin jinjirin nata wanda har kwanan gobe bata daina kuka kan 6atar saba,
Haka na haqura a dud tsawon shekaru nan ina zarya tsakanin mecca da nan gida nijeria nan wajen hjy laria inyi mata wata daya itama kuma can inmata wata dayan,
Shiyasa lokaci yaimun qaranci kwata kwata wlh haj mu'azzam ga kuma business komi yai mun yawa a lokacin,
ana haka kuma ita mahaifiyar ni'ima Allah yai mata rasuwa ko wata ba'a qulla ba ynzun haka da rasuwar nata, mafarin knn shi mahaifin nata ya sameta a wajen kakarta bayan an gama makokin mamar tata yanata mata fada akan ta daure dai ta haqura ta dawo nan nijeria d'in kusa da mijinta zifi sauqi har a wajensa shima.
nan suma dangin nata suka yita lallashenta harta haqura amman da sharadin cewa wannan gidan namu bazta kuma zaman saba saboda yana tuno mata da d'an jinjirin yaronta, dan acikinsa tayi renon cikinta a wajaje daban daban na gidan dan haka sai dai asamo mata wani gidan bashiba tofa kaji yanda alamurran suka kasance haj mu'azzam.
girgiza kai muazzam saraki yayi yace Allah sarki Allah jiqanta zanje in mata gaisuwa insha Allah, kuma Allah shi bayyana muku yaronku a dud inda yake, dan wlh 6atan d'a babu dad'i har ma gwamma ace maka yau Allah ya kar6i abinsa akan 6atan nasa,
idanuwan alhj Muhammad har sun fara sauyawa a 6oye ya sanya hankicerf ya goge qwalla daga idanunsa na mikin tuno dansa da yayi? Shin yana raye?
to inyana raye cikin wane kalar mutane yake yin rayuwa? ya tashi a musulmi ne ko kuma kiristan?
yaci abinci ko bai ciba?
Yana cikin matsi na wahala koko yana hali na farin ciki da wadata,?
yana cen yana rayuwa da mutanen daya tabbatar sune haqiqanin iyayensa basu ba?
Allah sarki abinda ya fada knn a fili tareda wani murmushi mai cin rai,
dafasa alhj muazzam saraki yayi yace bakomi haj Muhammad insha Allah komin daren dadewa Allah zai nuna mana shi, karage yawan ddamuwa dan Allah saboda itama ciwone damuwar, addu'ar nan da mukeyi akai mu qara zage dantse insha Allah gskia zatayi halinta.
"hakane haj muazzam ngd sosai da kulawanka"
Muazzam saraki yace bakomi hj Muhammad,,
kuma zancen mgnr gida d kk kamance da gidana na kusa dani ba kowa a cikinsa ne?
kuma kaga ai zaiyi girman gidanka nakega ko?
kadawo ciki kawai na bakashi halak malak abokina,,,
kallonsa Alhj Muhammad yk yana mamakin tsagwaran kirki irinna alhj mu'azzam saraki a duniyar nn?
dudda yasan shima yanada dukiya kamar tasa amman har baiji qyashin bashi kyautar gida ba haka ba batareda ko asin shi ba? lallaikam shiko a rayuwa yayi sa'ar aboki nagari managarci wanda yasan ko bayan ransa bazai mance da lamarin ahalinsa ba zai riqesu amana kamar yanda zaiwa nasa.
cikin tsabar farin ciki ya fara fad'in "nagode nagode haj muazzam saraki Allah shi bar zumunci a tsakani,
"haba haba dan Allah kuma haj Muhammad ai babu zancen godia a tsakaninmu kama daina dan Allah abokina''
dariya sukayi dukkansu sannan mu'azzam sarakin yasake cewa"haj Muhammad muje ga family na cen kazo ku gaisa ko?
tare suka isa har wajen nan suka gaisa da mommy umaimah nan momyy umaimah take tambayarsa qawar tata ni'ima ta 6ata 6a kwana aru
aru?
"takusan dawowa gareku hjy umaimah insha Allah cewar alhj Muhammad yana dariya amman idanunsa nakan mahaber da yake cemasa "dady morning,,,
lpia lau d'an saurayi,
baisan miya fad'ar masa da gaba ba da ganin yaron ba, saiya rasa cikin kuma a family dinsu matarsa ni'ima a cen mecca dawa yk masa kama?
koko dai gixo ne yakega ma kawai.
ahaka dai ya 6arar da zancen, sannan ya dubi muazzam saraki yace "haj mu'azzam wannan ma saurayin yaron family dinka ne shi?
yayi tambayar yana mai nuna mahaber din cikin murmushi, da son yaron kuma.
hakanan shidai yaji son saurayin ya shigesa a ransa batareda yasan dalili ba,,,,,,

Fasaha online writers f.o.w.📘🖊
[10/11, 2:45 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb💤💤

🌊🌊🌊🌊🌊
Fasaha online writers f.o.w.
Chapter 14 · 0% Book details