← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 109

Sashe 60

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

baby manal taba maqale jikin ummu hani taqi sauqa. a can waje kuwa bash ya tsurawa leben mahabeer ido ganin yanda yayi tabon digon baqi dan siriri daga gefen le6en nasa yace "miya samu le6enka ne haka kuma gifted? laso le6en nasa mahabeer yayi da halshensa yaja numfashi mai zafi ya furzar sannan ya shafa kwantacciyar sumar kansa yace "wafa ce bayaga hayatacciyar mage ta ta gidan nan"!!! kallon mamaki bash yakeyi masa yace "wacece kuma dai hayatacciyar kyanwar ka a gidan nan kuma wacce ban sani ba? hararra mahabeer ya sakar masa yace "okey inda baka santa ba shiknn, basah yace ''okeeyyy naganeta kam yanzu,kawai kacemun amaryar mu ummu hani, ai wlh serous naji dad'in wannan kyakkyawar maja din da momy ta fad'a mun dazun wadda dady ya jagoranci hada maku kaida 'yar magen nan taka, shege mukhtar ma hot-storyn nan ya wucesa ay tunda nai nasa text ynxu na tura masa na gameda maganar shiru kkji dudda nakira layinsa yaqi shiga kuma. Mahabeer yace "bansan iskanci fa bash wlh wannan bad story din kake yad'awa friend namu kuma? Pleass naroqeki ka daina kada ka jawomin abin kunya danni wannan wlh abin kunya ne a gareni bako qarami ba"!!!! bash yace "idan har na daina fad'awa friends namu Allah yai mani albarka, tsoki mahabeer yaja kawai yaci gaba ma da type dinsa cikin laptop dinsa kota kansa bai qara bibama dudda yanajin yanda yake bugawa sauran friends dinsu batun auren wannan satin, washe garin ranar kuwa masu tafiya dud sun gama shiryawa hadda su baban momy umaimah yazo daga katsina shida da amininsa baba sani dan zuwa neman auren mahaber a nijer din kamar yanda dady mua'zzam da annah suka shaida musu. shatara ta arziqi haka dady mua'zzam da alhj Muhammad suka hadawa su baffa dan Shikam baffa kaddo harya rasa bakin godia sai sabuwan add'ua dayake tasake binsu dashi. Mota biyu sukayi dady mua'zzam najan su momy umaimah da annah tareda ummu hani da nabeela, sai dayar motar dady Muhammad ne shima ke driving su momy ni'ima da baban momy umaimah da abokinsa, doguwar tafiya ce sukayi sosai wacce ta daukesu tsawon awowi sai wajen biyar sannan sukai isa cikin garin niger har cikin anguwarsu ummu hani wato darul islam, dai dai qofar gidan baffa indeh suka tsaya, dayake kusan jere gidajen su yake dana baffa kad'do, dukknsu suka fito cikin motan ummu hani tana shaqar qamshin iskar garinsu Saidata murmusa sosai sukuwa su nabeela da sauran mutanen wajen sai kallon rayuwar da jama'ar garin sukeyi haka cikin Godiya Allah, baffa indeh ne yafito cikin gida da 'yar butarsa ga hannu kansa da nadi irin nasu na buzaye yana arba dasu baffa kad'do kuwa yasaki butar qasa yayo kansa ya riqesa gam nan sukaita murna ahaka baffa indeh yayi musu jagora zuwa cikin gidansa. qaton buzu maman nahee ta shimfida musu tana maraba lale dasu bintey da kad'do da sauran mutanen, dama shi baffa indeh ko zama basu kaiga yiba ya fice da sauri yaje ya farfadowa dangi kaddo ya dawo da matarsa da ummu hani saigasu ko sun shigo gidan dayawa sosai, nabeela tana ganin shigowar fararen buzayen nn q'idaga guda dasu yasata yiwa ummu hani rada da cewa "sister wannan taran al'umar da suka shigo suwaye,, murmushi ummu hani tayi tace *fami* *(family*)nane su duknsu wannan mai baqin nadin akai shine baffa indeh qanin baffa na wato baban qawata yar uwata nahee kamar yanda nake miki labarinsu nahee da sahee abokina na nan, nabeela tace to ina shi yaya baroma da kika bani labarin sa shima? girgiza kai Ummu hani tayi tace "bayya nan cikinsu shi. maganar da baffa kad'do kewa yan uwansa ne na gameda jinkirin daya samu wajen dawowar dakuma dai sauran bayanai na abubuwan da suka biyo baya dudya fada musu, gaba dayansu sukaita godia gasu dady mua'zzam na irin taimakon dayaiwa dan uwansu da iyalinsa, baffa indeh yace "haqiqa hankulan mu sun tashi sosai gamida shirunku gashi na baka numba na waya na amman tsawon lokaci banji kiranka ya shigo gareni ba har akayi bikin nahee da qawarta watan daya wuce, amman yanzu Alhamdulilla inda kundawo lpia , babu bata lokaci dady Muhammad yashigar musuda nemawa dansu auren ummu hani, sunkuma fahimci har baffa kad'do shima yayi na'am suma kuwa babu bata lokaci suka amunce anan dady mua'zzam yake tambayarsu yaya al'adar su take ta sadaqi??? sai nan baffa indeh yayi gyaran murya yace al'adar mu bada kudi ake biyawa yara namu sadaq'i ba da raqumma ne, baffa kad'do yaso yace abar hakan amman babu yanda ya iya inda haka al'adarsu yake tun usuli. nan dady Muhammad yace "to babu komi zuwa juma'a din wato ranar daurin aure in sunzo saisu bayarda kudin raqumman a siya, nan aka kaisu masauqi sukaita kai musu abubuwan ci kala kala irin nasu har zuwa washe gari, su dady mua'zzam suka wuce da nufin sai ranar daurin aure sannan. nabeela kawai aka barwa ummu hani sukuma suka dauki hanyar komawa gida. Lokacin su baffa kad'do sun koma gidansu suma a ranar kuwa saida ummu hani tasa aka kaita har gidajen su nahee amare tagansu suma sukaita murna da ganinta, sai dare sannan suka dawo gida. dud kullum kuwa sai ummu hani taraka nabeela ganin gari nasu datace yayi matuqar burgeta sai marece suke dawowa. dady mua'zzam kuwa dud ya sanarwa yan uwa da abokanen arzuqa daurin aure. yau takama juma'a su momy umaimah ne suka fara isa gidansu amarya saisu dady suka biyo su a baya shida d'umbin mutanen sa 'yan zuwa daurin aure,mota na bin mota sama da kasa qilguwa kuwa. anguwar darul islam ta dinke d'uf da 'yan d'aurin aure bnda manyan motoci nasu abokan su dady mua'zzam baka ganin komi a wajen daurin aure. haka akataru aka daura aure lpia batareda ango ba, dan qaryar ciwon ciki yaiwa su dadyn harda lafewa kan bed kamar gaske, sai dai freands dinsa su bash da muktar da sauran abokanansu da iyayen. jama'ar wajen sai Allah sa alheri sukewa su dady da baffa. a can cikin gida kuwa cike yake da mata 'yan biki anata sanwace sanwace, kota ina ka gitta dangin amarya da ango ne ciccike awajen . amarya ummu hani zaune cikin daki tasha adonta cikin kayansu na buzayen usuli na al'adar auren su. baqaqene kayan masu adon zaruruwa a gaban rigar na ja da baqi da brown an mata nad'i akai na baqin gadonsu an saki jelar nadin ta kwanta gadon bayanta. kanta yasha kitso gwanin sha'awa yasauko mata kuwa har saman dukiyar fulanin ta, nabeela ta gyara mata girarta ta sake fitowa 'yar zurut da ita baqa qirin gwanin burgewa, momy umaima tace "kai 'yata Masha Allah ahsanul khaliqin, kinga kyanki kuwa ummu hani na?, kigodewa Allah ummu hani na, barima na qara haskaki nima, tana fad'in haka ta zuge jikkarta ta fiddo wani sarqa da 'yan kunne na gold mai kyau da maqudan kudin gaske kuma, sabuwa ce dal ta siyawa ummu hani din dan irin wannan ranar daman, tana gama sanya mata kuwa tuni taqara haska amaryar kamar ka saceta ka gudu harsu nahee da sauran mutanen wajen saida sukayi santin kyawun ummu hani suma kallonta kawai sukeyi cikin sha'awa, gashi uwa uba tayi dace da uwar miji ta qwarai. Nabeela ta jawo hannun amarya ummu hani suka fita ta bayan gida wajen fili ne sosai harda qoramar ruwa daga nesa dasu can. babu mutane masu wucewa sai jifa jifa tazaro wayarta tace "dan Allah tsaya nai miki pic yanda kika sha kyaun nan inna d'orasa a media wa friends d'ina bnsan yaza suyiba in suka ganki, wooo Allah danice da kyawun nan naki sister wlh dasai na kwad'a yaya mahabeer son raina dashi,, nan da nan ummu hani ta daure fuska jin sunan amakson dinta da nabeela ke mata zancen sa, nabeela tace "sorry sister saki fuskar kiyi Murmushi kona sa miki kuka tayi maganar cikin marairaicewa wanda hakan yasa ummu hani kallon nabeela din tana sakin wani Murmushi wanda yayi matuqar qara haska kykkyawar farar fuskarta dai dai lokacin da baffa indeh yazo wajen yanadaga bayan ummu hani cikin shigarsa ta mnyan kaya masu ruwan zuma da baqin nad'insa akai ya juya fuskarsa gefen yana qwallawa nahee kira daga cikin gidan bikin a dai dai lokacin ne kuma nabeela ta dauki foton tabasu one plasher itada baffa indeh din. tadaka wani uban tsalle kuwa tace "wow kamar sarauniyar kyawawa wlh,,, gskia sai kin biya kudin ganin hoton nan sister kinga yanda kika haska cameran nan da kyakkyawan murmushun ki kuwa????? ....
Chapter 60 · 0% Book details