← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 109

Sashe 19

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*Uhmm to ay dad'i na da gobe saurin zuwa kamar ynda ya farun a yanzun,, 💃🏿💃🏿💃🏿,to har gashi dai wannan karon an sake d'auko mana wani sabon babyn da wuri💃🏿💃🏿💃🏿,,,inye 'yar gayun ba,,,goyo da....🤱🤰🤪😜🤣tofa mune 'yan soye a gaban murhu a wannan jiq'on😋😋😋, kisan ma da sanin cewa sai muncima naman sunan nan mutunci a wannan ranar ta soye,, kacan kacan zamuyi masa naman nan harda guzurinsa ma zamuyi a bako walle kuwa*
😂🤣😂🤣😹😹😹😹😹😹
🌊🌊🌊🌊🌊
🅿1⃣9⃣.
🌊🌊🌊
Gabaki d'aya ummu hani taji ranta na suya yayi wani irin mummunan 6aci lokaci d'aya taji hawaye na bin fuskarta sharrrrrr!!,,, watau shi talaka dai an renasa knn?
kowace iriyar maganar banza aka yabid'o za'a jefa masa ita ne batare da da tunanin komi ba,,???????!!!
share hawayen tayi dukkansu da gefen hannunta ta dubesa yana nan tsaye q'yam d'insa sai wani shegen murmushi yakeyi waishi nn yana jiran amsa,,,,, dan yasan babu abinda zai hanata amincewa da buq'atarsa yanda ya lura tana son maman ta d'in nan,,
wata iriyar muguwar harara take watsa masa cikin irin kalar muryarta take cewa
"dakata mlm,,, niba 'yar iska bace bare, iyayena sun mini isasshiyar tarbiyar dako bana tare dasu bazan ta6a yardata ba dan haka kaje ka samu dai dai kai ninafi qarfin tunaninka mtsssss,," tana kaiwa nan ta wuce ta barsa tsaye wajen bakinsa galala ya bita da kallo dan bai ta6a tsammanin qin amincewa buqatar tasa daga gareta ba,
naushin hsnnunsa yayi ya doki iska tareda fuxgar da iska ta bakinsa yace
"hmmm hooo this beautiful girl wooo, i know you will come back to me,,, even not now,, zaki dawo gareni ne nasani kodan mamanki ma baby,
Shima barin wajen yayi ya nufi sauran rooms d'in dan cigaba da duba patient d'in nasa.
sai faman tsinewa doctor lurwan ummu hani keyi cikin ranta harta isa wajen mai abincin ta siyo musu waina da miya na d'ari da hamsin har mai wainar na tsokanarta da cewa
"ke 'yar kyakkyawar buzuwa d'ana fa yace yana ciki inya girma ya isa aure,, murmushi ummu hani tayi tace "mansur da gaske kake?
Mansur yaron da bai wuce shekara 10 ba shi dai Allah ya hada jininsa dana ummu hani tun fara zuwanta wajensu siyen abinci mafarin knn cikin shirmensu na yara yake fad'awa mamansa in zatai masa aure wannan farar buzuwar zata aura masa,,,
jin ummu hani na tambayarsa yasashi saurin cewa "eh buzuwa ina sonki inna girma zan aureki kema zaki aureni ko,,,?
dariya mamarsa tayi yayinda ummu hani ta duqo kusa dashi ta shafa kansa cikin murmushi tace "mansur nifa yayarka ce kuma kaga qane bai auren yayarsa,,, ka bari inka girma zaka samu mai kama dani zaka aura insha Allah mai kirki kaji ko d'an q'anina? dariya yasaki irin ta yarinta yace
"eh na ji yaya,,,
"yawwa mansur na,,, natafi to bye bye,,,
nan sukaita d'agawa juna hannu goggo larai mai abinci cikin ranta take cewa ''mutane nawa anan wajen suke son wannan yarinyar amman taq'i basu fuska?? cikinsu kuwa harda q'aramin yaronta wnda baisan mima duniyar take a ciki ba,,, lallaikam,,,,, ta girgiza kai tareda furtawa a fili,, "farin jininki a bayyane yake buzuwar kyakkyawar yarinya, baga manyan ba harma ga qananan,, koba komi ma yarinyar tasan darajar manya dud yanda akayi ta fito ne a gidan tarbiya amman in baccin haka yanda tasan masu kyau da wulaqanci yawancinsu aida abin ba haka ba,,, dan komi tayi zatayi dai dai da ita ne dan surar ta ta biya,,,
haka dai goggo larai taita ta lullu6e ummu hani dai da addu'ar samun kamilin cikakken namiji na gari ta cigaba da saida abincin ta,,,,
tana komawa dakin ta ajiye musu abincin a qasan tabarmar dake gefen gadon ta miqawa baffa nasa sannan ta bawa mommonta a baki ta faraci saida suka gama sannan ta wanke kwanikan a bincin ta dawo wa goggo larai dasu ta dawo knn da shirin komawa d'akinsu tagamuda umaimah lokacin tasanu ta daddogaro ta fito fitsari tarasa inda toilet d'in yake,,
a lokacin dady mua'zzam bai jima da fita ba dan siyo mata ayba data fad'a masa tana da sha'awar ci,,,
"yawwa baiwan Allah zo mana kinji,,, har kusada da ita ummu hani ta matsa tace "tohm"
Umaimah tace "yawwa 'yata temakamin zakiyi ki rakani toilet dan Allah ban san takan hospital d'inba ne,,,
"to mah muje na kaikin,,,"
abinda ummu hani tace knn dan ganin matar tasan zata haifeta,, ita koba haka bama girmama jama'a d'a6iarta ne,,,
sun fara tafiya knn sukaci karo da wata babbar likita tana ganin umaimah tai saurin matsowa garesu tace "madam kin fito exercise ne?
tayi maganar tana murmushi.
nan umaimah ta yi mata bayanin abinda ya fiddota, nan likitar tace tazo ta kaisu toilet na office nasu,,, ga mamakin ummu hani sai taga wacce aka kira madam d'in ta riqo hannunta sun wuce tare,,,
har ta gama ta fito suka dawo anan momy umaimah ta dubi yarinyar dataji hakanan d'abiunta Fara'd d'aya sun burgeta harta ke cemata "kema kina jinya ne anan ta wani kenan?
murmushi ummu hani tayi tareda sinne kai qasa sannan ta dago tareda fad'in "eh mah,, ina jinyar mamana ne amman tare muke da babbana,,,
"Allah sarki cewar momy umaimah, wane room ne kuke?
"room 24 ne,,,
lokacin sunzo dai dai wajen dakin nasu momy umaima d'in,, dubn saman dakin su umaimah tayi taga su nasu room 18 ne dubnta tasakeyi tace "hakanan naji kin burgeni 'yata kinada kirki ga kuma kunya,,,
murmushi ummu hani tayi tace "ngd sosai mah,,
zan koma dakinmu gunsu baffa, tayi maganar tana dubn side d'in room d'in nasu hakanan taji ta takura, d'abiarta ne hakan batada saurin sabo da mutane ita,,
"Muje na dubosu nima inda kinzama 'yata nima nasamu 'ya ko,,,,?
'yar siriyiyar dariya ummu hani tayi har 'yar siririyar wushiryarta ta fito,, amman kuma har a ranta ita mamakin farin jininta ga jama'a takeyi,,,saita tuna Allah ne kuma ikonsa yafi ga haka, koyaya tayi 'yar mua'mala da mutum saiya sota,,
har dakin nasu umaima ta bita ta gaida baffa kad'do da inna binte,, anan tagane ma ashe sune buzayen nan na d'azun data gani ,,,bata jimaba ta ce zata tafi suma sukai mata addu'ar samun sauqi dan sun gane itace matar mutumin kirkin nan daya kawo musu temako d'azun,, ummu hani itama har d'akin da aka kai mommy umaimah d'in ta rakota nan suka iske daddy mua'zzam saraki zaune,, dayake doctor sa'a daya iske dakin ta shaida masa inda ta tafin shiyasa ya zauna zaman jiran dawowar nata.
shida kansa ya taso ya kamota ya zaunar a gadon yana mata sannu ganin haka yasa ummu hani tayi saurin juyawa dan kunyar yanda taga mutumin nawa matar tasa tarairaya, tana gaf da fita ne lokacin taji mommy umaimah tace "zo man 'yata zaki tafi babu bankwana kuma.
Sai lokacin dady mua'zzam saraki ya lura shi da ummu hani d'in ma tun shigowar su,
cikin kunya kanta a sunkuye ta qaraso wajen anan mommy umaimah kuma take shaidawa dady mua'zzam d'in temakon da yarinyar taimata da yanda ta zama gareta harma taje wajen iyayenta ta gansu,, shima yaji dad'i har ma yake tsokanar ita ummu hani da cewa "kice mun qara samun d'iya mai temako kinga saimu tafi abinmu da ita gida ko 'yar buzuwar agadez??? ,,,
Mommy umaimah dariya tayi hadda ita ummu hani d'in da kanta ke a sunkuye,
"zaki dinga zagayomu ko diyata ana gaisawa kafin mu tafi ko?
cewar mommy umaimah.
Cikin kunyarsu ummu hani take fad'in "eh mah zan dinga zuwa muku kanku tafin,,,"
tana fad'in haka kuwa da sauri ta juya ta gudu tabar d'akin,,,,,,

Fasaha online writers f.o.w.📘🖊

*xexen fasaha*✍🏻
[10/11, 2:46 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊

Story and writing
by
Xayyneb 💤💤

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.
Chapter 19 · 0% Book details