← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 109

Sashe 36

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

*Xexen Fasaha*
[10/11, 2:47 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb 💤💤

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.

*Assalamu alaikum 'yan uwa musulmai, ina fatan kunyi sallah lpia? Ubangiji Allah ya qara maimaita mana ganin wata shekarar sallar cikin qoshin lpia da wadata Amimmm.*
🌊🌊🌊🌊🌊
🅿3⃣2⃣
🌊🌊🌊
Yamutsa fuskarta tayi tareda runtse idanunta jin yanda qafafun sukai mata wata irin zurrrrrrr ta shigar wani sabon zafin,,, da qarfi ta dafe qafafun nata tareda fad'in "washhhhh!!! mah, q'afana zasu cire,, tana maganar ne tana yarfe hannunta idanunta a runtse,,,
da sauri annah da momy ni'ima da ita momy umaimah din suka taso suka qaraso wajenta suna fad'in "ya ilahe, ummu yaya qafar take miki ne?? cewar momy umaimah tana shafa mata saman tudun qafafun nata, sosai takejin kamar zata zubdawa ummu hani qwallan tausayi kan ummu tayi wata maganar ne wayar nomy umaimah ta shiga qara da sauri ta d'aga wayan ta duba tana fatan cewa Allah sa mahabeer din ne amman sai taka sunan mua'zzam saraki (nuree) ya bayyana kan wayan da sauri ta d'aga wayan tana sallama yayinda momy ni'ima tsananin tausayin ummu da qafanta ya manayeta hakan yasa ta zauna gefenta tareda rungume ta a barin rabin jikinta tana rarrashinta harta cewa "inna koma gida zan fadawa mahaifanki halin da kike ciki ummu hani dan suzo su ganki,, cikin sanyin murya kalar ta ummu hani wacce zafin ciwo yasa muryan nata qara yin qasa sosai tace "a'a aunty kada kifadawa su baffana rashin lpia na dan Allah,, cikin duban mamaki momy ni'ima tace ''ah miyasa to ummi,,,?
cikin cije lips dinta tace"hankalinsu zai tashi sosai kuma ummana bata son jin tashin hankali ne dan ciwonta yana tasowa ne,, girgiza kai annah tayi tace
"kai Allah sarki,, to niimatu barsu da maganar kinji? Mudai fatanmu Allah bata lpia"
Sauke ajiyar zuciya momy ni'ima tayi tareda da cewa
"to shiknn ba komi "Allah shi bada lpia"
Aminnn"
cewar annah,,dai dai nan momy ni'ima ta shigo dakin bayan firarta d'azun lokacin da nuree yai kiranta.
zama tayi tareda cewa ''sannu ummu na, ya qafan yanzu?,
duban qafan nata ummu hani tayi zuwa lokacin ta rage mata zungar nan sosai bisaga d'azun.
a hankali tace ''yasha babban da d'azun mah yy sauqi,,, " yawwa ummu na hae naji dad'i,,, annah tace
"dudda haka mafi kyau akai ta asibiti unaimatu dan aduba qafan nata sosai abata magunguna ma in ta kama,, " momy ni'ima tace "gskia ne annah kam hkn"
Momy umaimah tace "eh annah yanzu ma fitar danayi na sauka qasa falo ashe nuree ne ya dawo daga tafiyan nasa yai mana suprise saida na sauka sannan na gasgata dawowar nasa kamar yanda yace mun a waya yana falon qasa in sauko in gani",,girgiza kai annah tayi tareda cewa "kai mai sunan manya ya saba mana haka ai,, bari na sauka to nima sai nai masa ya hanya",, annah tayi maganar tana mai yunqurawa tsaye tareda fad'in cewa"bismillahi Allah tada baiwar ka,, qara gyara zaman hijab dunta tayi tana mai cigaba da lazuminta sannan ta dubi momy umaimah tace "kidai ci gaba da gwada number wannan shanshanin mijin nawa ko a dace, in kuma kinga lokaci na niyyar qurewa ki kaita da kanki kawai zaifi basai an wani jira yazoba inda shi dai yanzunnan zaka gansa cikin gida amman fit lokaci daya kuma zaka nemesa ka rasa, indama ace ko wajen yarinyar ma da zai aura yake wannan zaryar dasai musa rai ma da auren nasa nan kurkursa Amman ynxu haka in kin bibiya suna cen tareda su mukhtar ana nan ana anata faman kiransa shuru.,,
Murmushi momy ni'ima tayi tareda cewa ''ai mana afuwa anah mahabeer din nawa ai shima patient ne bai jima da miqewa ba,, annah tace ''an taba yin patient da dan karan yawo kuma ni'imatu???
'yar dariya momy ni'ima tayi batace komi ba, yayinda annah ita hattama fita daga wajen,,
"da sauri momy umaimah tace "yawwa qawata ga number ma ta shiga bari nai masa magana"
bayan sun gama wayar ne tace "yawwa gashi nan ma tafe wai ashe yaje office ne ni bnsanma ya koma ba dan ko breakfast baiyi ba yabar gidan nan,,, " momy ni'ima tace "ai dan nawa jarimi ne shiyasa kike ganin muhimman al'amurra daga garesa" tayi maganar cikin Murmushi, itama murmushin Momy umaimah tayi,, tashi Momy ni'ima tayi tace "zan koma gida amman zan dawo anjima ummu hani inga yanda qafan yake kinji? tayi maganar tana mai kallon ummu hani cikin sakin fuskarta,,, ajiye fuskarta ummu hani tayi qasan laps dinta tace"nagode aunty,,, har qasa momy umaimah tarakata tafi sannan ta wuce side din mua'zzam saraki ta iske harya shiga wanka, dawowa tayi ta koma kichen ta fara had'a masa sauqaqqen abinci wanda tasan bazai dau tsawon lokaci ba,, tans cikin aikin ne taji yo muryan mahabeer daga can falo yana fad'in "momy ns ina kika shige ne naje side naki baki nan,, ajiye knife din hsnnunta tayi wacce take yanka cabbage dashi ta fito falo tace "gani nan mahabeer na,, tun dazun nikeson ganinka zanturaku hospital ,,"
miya faru momy na??"
Yayi maganar yana wani langwabe wa tareda dora goshinsa a saman kafadanta,, shada kansa tayi tace ''ba tyme mahabeer na maza jeka fiddo moto ina zuwa,, cikin mamaki ya sauke fuskarsa daga kafadanta ya bar falon a ransa tubsnin mizaiyo kuma a hospital?? shiga dakin momy umaimah tayi ta kama ummu ta miqar tsaye da qyar sannan ta dauko mata gwadon mayafinta baqi wanda tagansa kusa da ita a saman gadon ta d'ora mata abinta bisa shimfidadden gashin kanta wanda wutsai biyu na gashin dogaye sosai suka sulalo bisa fuskarta gefe da gefe saboda tsaban santsin gashin nata shiyasa gyalen baima zama sosai a sama gashin gar Saida momy umaimah din ta qara janyo mata shi ta rufe mata kusan rabin fuska dashi kamar ynda ita ummu hani din take Yana abinta in batasa niqab ba,
Kamo hannunta tayi a hankali tana mata sannu har suka sauko nan falo suka wuce harabar gidan inda mahabeer ya fito da motan nasa yana daga ciki zaune kunnensa saqale da Bluetooth dinsa yana gyada kai idanunsa a lumshe ga alama da abinda yake sauraro acikinsa,,
a haka har suka qaraso dai dai motar sukaja suka tsaya momy umaimah ganin yanda yarufe idanunsa yasa tasa hannunta ta zare Bluetooth din kunnen nasa,, da sauri ya bude tsumammun idanunsa ya waresu a bisa fuskar momyn tasa yace cikin shagwabe wa "oh momy sorry banga isuwan zuwan kiba ne, harga Allah sam shi baima lura da wata ummu hani ba wacce ke bayan Momy umaimah ba, saida yaji momyn taje "ummu zaka miqamun wajen doctor lurwan qafadunta ne batajin dad'insu sakamakon faduwan da tayi a bisan su, tayi maganar tareda bude bayan motan ta kamo hannun ummu ta zaunar da ita sannan ra rufe motan tareda dan duqowa saitin glass din din motan setin da yake zaune sai faman qunci yake kan abinda momyn ke shirin sashi aikatawa wannan 'yar Qauyen yar rainin hankalin yarinyar.
"dan Allah mahabeer na kabi mun ita a sannu nasan ka da gudu da moto kaga batajin dadin jikinta kuma patient baida buqatar sake wata wahaltuwan akan wacce yake ji ma a jikinsa kaji ko mahabeer na??
gyada kai kawai yayi sannan ya tada motan momy umaimah na masu a dawo a haka har ya bar get din gidan Yana fita kuwa titi ya maida abinsa a kune yaci gaba da jin music dinsa,
sannan ya qurewa motan gudu fuuuuuuuuu kakeji kamar suna saman iska tuni ummu hani ta gigice ta sakar masa kukan nata da qarfi dudtabi ta qanqame jikinta katamau ta rungume cikinta danji take kamar zaya zazzago mata 'yan hanjin ta waje,, Kai mahabeer ba qaramin maqetacin mutum bane saikace ita tasa shi kaita ne??zare Bluetooth din yayi a kunnen nasa ya barsa a jikinsa,,sarai kuma yana jin sautin kukan nata amman yayi burus da ita yahau tabe lips dinsa ma, a ransa yake fad'in "yarinyar nan bazaki ta6a jin dad'i na ba, inda bakida kunya,,harni zaki sawa abu a hanya in taka na fad'i?? Hmm yau sai naga qaryan girman kanki,,, kina talakan ki kawai sai fad'in ran tsiya kinfi qarfin ki bude baki kiyi mgn ko? Hmmmm,, naki wasa ne 'yar aikin momy,,,
wani wawan burki taji yaja wnda yayi masifan gigitata har batasan santa tayo wata iriyar doguwar sukuwa ba ta dawo gaban motar ta durqushe jikinta na rawa har tama mance da ciwin qafafun nata ta zuqunne samansu tana makyarkyata.
wata tsawa ya buga mata yana fad'in "keeee!!! dalla matsamun da wannan qazamun jikin naki daga qafana kobaki jiba??,, stupid girl kawai,,, mtssss,,, qafa yasa yana shirin tureta batasan sanda ta riqe qafafun nasa katamau tana kuka ba cikin muryar ta take fad'in "wlh amakson kai mugu ne kuma bazan sake kaba saika maudani gida inkai baka son mahaifan ka ni inason nawa,,
"ke wakike fadawa magana koni sa'an yinki ne? "wlh ni nace ka maidani gida dan basona kake ba zama ka iya kasheni naga alama,,, wai bazaki sakar mun qafa bane kosai nayi ball dake ne anan eye?
ahankali ta sakar masa qafafun ta koma ta zauna kusa da mazaunin direba tans sauke ajiyar zuciya.
dubn raini ya bita dashi wani dogon tsoki yasake ja sannan ya maida hankalinsa atitin yaga shanun da aka koro har sun gama tsallakewa sannan ya tada motan ya daura gudun daga inda ya tsaya,,,
a firgice ta bude rufaffun idanunta rareda fiddo fararen idanunta waje jin gudun ma ya finada jitayi wata irin juya na jujjuyata jin tana shirin faduwa yasata saurin kamo gefen farar t shirt dinsa ba ta riqe gadamau,, buge hannun ta yayi daga saman rigan nasa da sauri takai hannunta kan nasa ta riqe sityarin motan wani wawan burki mahabeer yaci ganin yanda take shirin sasu qundun bala akan titi,, da sauri cikin juriya ta samo ta fito daga cikin motan tana layi harta yarda gyalen anan qasan wajen ta zuqunna qasa tana faman kakarin amai,, a fusace mahabeer ya fito daga motan ya iso gabanta ya sa hannayen sa ya damqota ya miqar da ita tsaye yana faman jijjigata da qarfi yayinda gashin kanta dud ya warwatse bisa jikinta da q'irjinta har zuwa qugunta,,
Cikin tsananin 6acin rai yake fad'in "baki da hankali ne kike niyyar kasheni da sauran rayuwa na? kaji macuciyar yarinya,, "
dudda ummu hani tana cikin halin galabaituwa bata hana ta magana daqyar ba tana cewa "A... Amak...sonnn sa.. sai na fadawa mah,,,kanta ida maganar yasa hannunsa ya maida nata baya cikin mugunta,, lokaci daya qirjinsu ya had'e waje day'a bazato ba tsammani yaji wani Shocking nabin kowane saqo da lungu na jikinsa cikin dauriya ya ture komi yakeji gameda emotions din jikin nasa yafara magana a masife ta hnyar kamo qasan habanta fuskarsa na kallon nata ya zuba mata kalar idanunsa cikin nata yana zaro mata su yace "momyn tawa zaki kai qarana wajenta? Ashe rashin mutuncinki yarinyar nan har yakai haka?
tanason qwacewa daga garesa amman taji riqon nata da yayi bana wasa bane dai ashe, d'agowa tayi ta watsa masa kallo da fararen idanunta tass dasu dasuka sauya launi na ja ja sabida kukan datake yia lokacin,
wani irin kallo wanda yafi kama dana mugu ga wanda akewa shi toshi fa ta dinga watsa masa cikin qunan rai,, yatsina fuskarta tayi ta murguda masa bakinta,
cikin dauriyarta ta bude baki zatayi magana da niyar cewa ya sakar mata fuska danji take cikinta na qara juya mata a lokacin ,, tana ma sake jin Wata sabuwan juyan da tuqowar amai a dalilin gudun motar nan nasa daya haifar mata sai ji kayi ba zato
Kyaaaaaaa!!!!!,,, ta sheqo masa aman da take qoqarin yowa tun d'azun ya fito,, dud ta wanke masa farar rigan jikinsa dashi har cikin bakinsa ya shige ba shiri ya hadiye aman sakamakon sa'ar da tayi ya bude bakin nasa da shirin qara daddan q'ara mata wasu zafafan maganganun nasa daya qunso su tun daga cikin zuciyar sa har suka gangaro zuwa cikin saman halshen bakinsa Yana shirin furta masa su da niyyar suyi mata qunci a rai dan daduwan quncinta shine qaruwan farin cikinta, sai akayi rashin sa'a kuma reshe ya juye ga mujiyaaaa,,,,!!!
Chapter 36 · 0% Book details