Sashe 53
Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
aiki cikin nasara Alhamdulilla wan shekare suka dawo gida amman baffa yace bari dai yajira konanda kwana 3 ne kamin alhj Muhammad yasami wani sabon mai gadin,, da gudu ummu hani ta shigo gate din gidan dan ita batasan ma anwa maman tata aiki ba, sai yanzu datana kichen taji dady mua'zzam nafadawa momy, tana zuwa kuwa jikin mama bintey ta shige tana qyalqtalta dariya itama mama bintey din rungume 'yar tata tayi cikin farin ciki , d'agowa ummu hani tayi ta dubi maman nata cikin tsabar murna tace "mamma na shiknn ynzu kin warke baki qara wanna ciwon mai wahalan dake komai sani inyi ta miki kuka? tayi maganar tana share hawayen fuskarta, abinka da ummu hani mai d'an karen saurin kuka, saurin kukan nan naki dai yana nan ba inda yaje cewar mama bintey. d'agota mama binteyn tayi tana share mata hawaye tace "ya isa haka ummu hani na ba kuka bafa ya kamata kiyi ba murna zamuyi da godia ga sarki Allah dakuma bayin Allah n nan iyayen gidanmu dasuka riqemu da gaskia da riqon amana kinji ko? gyada kai ummu hani tayi ta kwantar da jikinta ana mamarta idanunta rufe cikeda tunanin cewa da gasken gaske dai fa tafiyar nan tasu gida ta qarato ba wasa ba?, jikinta taji ya qara matar mata anan, sai data d'an jima sannan ta lallaba cikin mutuwar jiki ta tashi tatafin. tana shiga gate din gidan kuwa ta hango amakson ya shige mota ko kallon sa ma batayi ba taci gaba da tafiyarta ita batashi take bama damuwarta kawai take wa renon haquri a lokacin. ganin yanda ya durdafafota da mota yaqi kaucewa sabida a setin hanyar da motar zata fice daga gidan ita ummu hani din take tafiya akai, cikin sauri tayi gefe ganin yana shirin bugeta dan shi sam baida niyyar kauce mata ma, da kallon harara tabi motar tana sauke ajiyar zuciya hannayen 2duka na saman q'irjinta tana sauke wani firgitaccen numfashinta a fili, danba qaramin tsoratata yayi ba ganin yanda yake shirin binta saman ta da mota, a fili tace wlh amakson na tsaneka mugu kawai,! kaje allah yafika,!!!!! mugun mutum kawai wlh na lura amakson sam bakada buri saina son ganin baya na kuma nan gani nan bari wlh, inkai haquri ma ay ni kwanan nan zan baran muku gidanku ma abunku sai kayi da wata kuma badai ni ummu hani ba"! dan ni na gaji da masifan ka wlh haba mana dan Allah mutum bai ajiye komi a ransa ba sai qina daga temakon sa a baya...! haka taita surutunta ita daya harta shige falon gidan ta iske dady mua'zzam zaune shida momy umaimah da annah suna fira, wacce yawancin ta dud firan danginsu ne na 'yan katsina wacce annah ce jagoran firan ma, ita haka take tana son taga sun zauna ana maganar 'yan uwa tanan nema take umartar dady mua'zzam yaiwa wani daga cikin dangin nasu abu inta fahinci shi mutunin nada buqatar abun koma miye kuwa, shiyasa kaf family nasu suke alfahari da annah dan tazame musu garkuwa ita da d'anta, abu sai dai in basuce suna soba ,shiyasa kullum zumuncinsu qara hab'aka yake babu wani fada da tashin tashina a tsakani. dan ita annah cewa take inhar bata kyautatawa 'yan uwanta ba sukaji dad'i towa zata kyautatawa kuwa? batada kowa sama dasu kam. gaisheda su ummu hani tayi ta wuce tana qoqarin hawa sama dady mua'zzam ya kirawota tadawo ta zauna qasa daga gefen qafafun momy umaimah tace dady gani, dady Allah saka muku da alheri akan kominka wamu, tayi maganar kanta na qasa. da kallo dady mua'zzam yabita yaji tausayin yarinyar yanda yaga dud jikinta yayi sukuku shiga tunaninsa tumanin rabuwa ne dasu ya hadassa mata hakan,murmushi yayi yace"badai ummu kin fara kewan rabuwa damu kema knn ko kamar yanda naga alamun hakan sun bayyana gareki, kasa magana ummu tayi dai dai nan nabeela itama ta shigo falon hannunta daukeda wata baqar keda mai layi layi ga alamu kayane a cikinta, gaishesu tayi itama tanemi waje kusada ummu hani ta zauna alokacin ne momy umaimah tace "kamarya knn nuree? kewan rabuwa dawa kuma zatayi? ban fahimci zancen naka ba, annah "tace gskia kam nima dai ban fahimta ba, da mamaki dady mua'zzam ke duban ummu hani sannan ya dago kai yadubi momy umaimah yace "badai bakusan cewa ummu hani da iyayenta zasu koma gida ba wannan satin?,, zaro idanuwa momy umaimah tayi tareda dafe qirji da hannayenta gabanta banda dakuwa babu abinda takejin yana mata dan maganar ma kamar saukar aradu haka taji ta shigeta , tuni idanun momy umaimah suka fara jawo ruwa jin yanda dady mua'zzam yaci gaba da yimasu bayanin dalilin zamansu aiki wajensu kamar yanda su iyayen nata suka yimasu bayani shida alhj Muhammad. kwata kwata momy umaimah kasa magana tayi yayinda annah ke cewa "tofa kaga ikon Allah, aida sunyi ma bayanin komi da wlh basai ma sunjira sun tara kudi ba sannan ayi mata aiki wannan abu duddai na ceton rai? dady mua'zzam yace "wlh kuwa annah, amman hakanma Alhamdulilla inda anyi aikin an gama lpia Ubangiji Allah shi bada lpia, tuni nabeela tayi wurgi da ledar hannunta ta rungume ummu hani ta saki kuka mai cin rai, saukowa momy umaimah tayi ta had'asu waje day'a cikin jikinta ta rungume su tana share qwalla itama,tana rayawa ranta yanzu shiknn lokacin rabuwar ta da ummu hani yayi knn? Wayyo Allah ita kam bataji dadi ba, jitake dasu baffa zasu bar mata ummu hani data riqeta tamfar yanda zata riqe Beby manal sai dai tasan dud irin sonda take mata iyayenta sun fita,,shiyasa ma takasa furta komi sai ruwan hawaye kawai datakeyi. Nabeela kuwa acikin kukan take cewa "Allah kuwa sister nima binki zanyi bazan zauna ba anan nima"!! kuka ummu hani kawai takeyi itama, yanda takejin ciwon abun itama a ranta kamar zuciyarta zata fashe mata takeji. Annah kanta jikinta yayi La'asar dan dud wanda ya zauna da ummu hani dai dai da second day'a saita shigar masa rai bare kuma su da suka zauna tsawon wata da watanni tare da itan. gyaran murya dady mua'zzam yayi dukkansu suka maido hankalin su wajen sa, Umartar momy umaimah yayi data sakesu takoma ta zauna, hakan kuwa tayi takoma wajen zamanta jiki a sanyaye tana goge qwallan idanunta. dady mua'zzam yace "inason ku maido mun hankulan ku nan, zuba masa idanuwana sukayi amman still ummu kanta na qasa har lokacin tana faman shassheqan kuka. Ummu hani dube ninan sosai cewar dady mua'zzam din. Ahankali kuwa ta dago da idanunta ta dubesa tace "to dady, shiru ya danyi zuwa can yace "ummu hani mizai hana dan Allah kimin wata alfarma guda wacce zan nema a gareki yanzun? zuciyarta cikeda mamakin abinda taji dady mua'zzam din yace, yanzu ita wace alfarma gareta wacce zata iya yiwa wannan mutanen kirkin ne? Kuma wace alfarma ce wacce zasu roqa a gareta indai tanada halin abun taqi yi musu shi kuma? Cikin rawar murya tace "dady matsayin baffa na nike ganinka dashi dan haka kafadi koma miye insha Allah bazan gaza yimuku shiba indai inadashi. "masha Allahu to" abunda dady mua'zzam yace knn yana Murmushin jindadi, sannan ya dora da cewa "niko ummu hani inada sha'awar hada ki aure da mahabeer inhar kina ganin babu takura a alamarin, wanda nasan hakan shine zai dad'a qara qulla qullin zumunci a tsakaninmu,wannan itace alfarma danike nema ummu daga gareki naroqeki ummu hani kada kice aa d'iyata,, Kamar am watsa mata ruwan zafi ga jikinta haka taji kalaman dady mua'zzam sun dabaibayeta. a mugun firgice kuwa ta d'ago kai ta dubi annah taga fuskar annah cikeda murmushi hakama data kalli momy umaimah tsananin farinciki ne kwance a cikinta 'yar dariya dariya takeyi mai tafe da d'an sauran maqalallun hawayen fuskarta. juyawa tayi gefen nabeela taga yanda nabeela ta ruqo hannunta duka biyun da hannayenta cikin jin dadi ganin yanda nabeela tamarairece mata hadda kwantar da kai a bisa wuyanta tareda yimata alama da idanunta data amince dan Allah, hakan ba qaramin tashin hankaline yaqara baibaye ummu hani ba, ita kuwa tasan inhar ta yadda ta auri amakson tasan kashinta ne zai bushe tsab bisa tafin hannunta, anya kuwa inta amince da aurensa bata yaudari kanta ba tareda jefa kanta tashin hankalin da sai illa masha Allah yayewarsa daga gareta?,, runtse idanunta tayi da qarfi lokaci daya tareda girgiza kanta ta bude idanunta ta dubi dady mua'zzam cikin bugawan zuciyarta wanda daqyar ta bude bakin ta datakejin mugum nauyinsa a lokacin kamar an dora mata bulo,cikin muryan kuka tace ''wlh dady a rayuwata babu abinda na tsananta tsana face m,....