Sashe 30
Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
🌊🌊🌊🌊🌊 🅿2⃣8⃣. 🌊🌊🌊 .... Hannat wacce ke zaune a inda take, dan ita a tunanin tama ta wuce gida. agogon hannunta ta kalla taga tara saura a lokacin. qarasawa tayi wajen ta tana cewa "ah hannat ashe kina nan baki tafi gida ba? Miqewa tayi tsaye tace "eh wlh momy dama ke na tsaya jira ki fito inji jikin na yaya mahabeer? Murmushi momy tayi har ranta takejin son mai son mahabeer dinta, dubnta tayi tace "kada ki damu hannat komi yayi sauqi sosai yanzu amman ya kamata kizo kije gida ko? "ok momy daman yanzu mukai waya da momy nace mata yanzun zan tafo,,, "yawwa hannat ai qwamma kada dare ya qara yi kuma ki gaishe mun da hajiyar taki sosai fa, kidai ce mata komi knn dai zamuyi waya zuwa gobe insha Allah." To momy good night cewar hannat da take dagawa momy umaima hannu harta fice tabar falon, a zuciyar ta taso sake ganin yah mahabeer din kuwa aman ta qudiri gobe zata dawo taga jikin nasa kota samu cikakken relief a zuciyar ta. hannat tana barin falon kuwa momy umaima tana shirin juyawa ta shiga d'aki itama taga fitowar ummu hannunta daukeda plate din da tayi amfani dasu da nufin takai kichen ta hadasu ta wanke da sauran kyn na can. tsayawa momy umaima tayi ita sai a lokacin ma ne ta tuna da cewa zata kai mata wani kunun inda wncen ya zuben. "mah barka da dare" Abinda ummu hanin tace knn tana niyyar durq'usawa qasa. da sauri momy umaima ta riqota gefen jikinta tace "kada ki durqusa ummu na hakan ma yayi tuni narigaya dana shaida tarbiyarki shiyasa kika shigar mun rai farat daya ummu na, ammm fatan dai kinyi buda baki lpia ko? cikin Murmushin ta na shigewan dimples dinta a fuskar ta tace ''eh mah" "masha Allah to ummu na AllAh shi bada ladan,, Amman kiyi haquri jina da kikayi shiru munyi dake zan kawo miki kununki amman ban zoba, wlh mahabeer na ne ya sil6e ya fad'i akan qafarsa awajen da kika yi 6arin kunun shiyasa, saida aka shafa masa magani sannan muka samu ya miqe ya koma dakinsa da qyar yana dangisawa to kinji dalilin da bn zoba din" Dammmmm!!!! gaban ummu yayi wani irin bugawa a lokacin datake sauraran bayanin daga bakin momy umaima din,, tuni tasan halin mahabeer a zuwa yanzun,, tasan kuma zaiyi wuya ya barta bayan yasan cewa itace silar cin qasar sa a yanda sike 'yar tsamar nan dashi,, wani irin numfashi mai qarfi taja wata zuciyar ta taji tana cewa lallaikam wlh *da sauran kallo*..... (my next novel insha Allah ). dafata da momy umaima taji tayi ne yasata saurin dawowa daga balaguron da tunaninta ya tafi,,. "miya faru ne ummu naga kinyi sararo haka lokaci day'a? cikin in ina in ina ummu hani ta dan zura hannun ta day'a Tana sosa qasan kanta sannan tace "t..to kuma ..mah shi yasan nice na zubar da kunun qasa ban sani ba? nazarinta momy umaima ta shiga yi in few minutes tuni ta gano cewar ummu na gudun mahabeer din yasan hakan kan wani tunaninta na daban wanda bata gane musu ba, shima yace bazai haqura ba inda tayi silar sashi jinya,,, ita kuma gashi an fada mata dud ta sauya a lokaci daya to why?? "kinji mah? Abinda taji ummu din ta qara tambayar ta knn,. dafa ta momy umaima tayi tace "nuree ne yayi mamakin miya kawo kunu ne a wajen....... nan ta fad'a mata tundaga sanda hannat ta fad'a kunu ne a qasa a wajen adan taqaice sannan ta dan yi shiru na yan mintina sannan tace"amman dai kada ki damu indai mahabeer nd bazai ce komi ba yasan tsautsayi kinji ko Ummu na??? cikin son 6oye halin da zuciyar ta take ciki ta kama gyada kai alamun amsawa, dai dai nan dady mua'zzam yasake fitowa dan sauraran labaran sa na NTA. kamar yanda ya saba,, gaishesa ummu tayi ya amsa cikin kulawa ahankali ta zame zuwa kichen. har ta gama wanke kayan hankalin ta bai gareta sam zullumin mizai biyo baya daga mugun mutumin nan kawai takeyi. koda ta gama dakin annah ta shiga da sallama dan tayi raayin shiga wajen tsohuwar ne kobs komi tasamu sauqin abinda ke muntsininta a lokacin. iskewa tayi annah har ma ta kwanta abinta hannun ta riqeda cazbi tana lazuminta. Jin sallamar ne yasa annah tashi zaune bayan ta amsa cikeda faraa take cewa"ummu ce ashe zoki zauna to, kinkuwa kyauta kinzo taya tsohuwa fira,, cikin Murmushi ummu ta zauna qasan carpet din ta gaisheda annah ta amsa cikin kulawa. "kinganni nan yau banjin 'yan fita falon shiyasa ban fita ba,, Ansha ruwa lpia ko ummu? "lpia lau annah" tayi maganar tana mammatsa yatsun hannun ta cikeda d'ari d'ari. haka annah taita janta da fira tun tana matsewa harta kai ga tasaki jikinta tana taya annah firar itama. dady mua'zzam ne ya shigo shida momy umaimah nn dady mua'zzam yace "annah kuzo muje gidan Alhj Muhammad domin muyi musu barka da zuwa a maqotanmu kuma babban aboki a gareni. Anna tace "hakanma yayi to bari na dauko mayafina sai muje ko,, har cikin ran ummu hani taji dadin tasu dan dama har yanzu ranta naga son ganin iyayen nata. Kamo hannunta momy umaimah tayi tace "muje ummu ko? dukkansu suka d'unguma sukayi suka fita maigadi na musu adawo lpia a haka har suka isa gidan dayake baffa ya fito waje lokacin mafarin knn suka samu qofar get din a bud'e. Ya fito ne siyo ma maman ummu din kifi anan wajen titin dawowarsa knn suka hadu. baffa ya gaisheda su annah suka amsa dukkansu cikin faraa sannan suka wuce ciki shima ya shigo tareda rufe qofan ummu data tsaya har ya gama rufe qofan yayinda su momy umaimah suka wuce ciki ganin ta tsaya wajen baffan nata. ta gaishesa baffa ya amsa cikin jin dad'i har cikin dakin da bintey take suka shiga da gudu ummu ta qarasa wajen maman nata ta rungume ta tana Murmushi. nan sikai ta fira ummu tanata fad'a wa iyayen nata kirkin iyayen gidan nata su kuma suna qara qarfafa mata gwiwa akan taci gaba da musu biyayya kamar iyayenya sannan ya qare da cewa "banda sa ido ga abun wani ummu kinjini ko? , cewar baffan. "insha Allah baffa" Yawwa ummu na nasan daman baki hakan tunatarwa ce dai Allah dai shi yi miki albarka, musamu mi samu kudin aikin nan da zaiwa mamanki komayi mu koma gida cikin yardar AllAh " "amin baffa." Bintey tace "to kije kada kuma su nemiko,,baffa dake warware qumshim ledar kifin yace "zokici kifin nan ummu dudda babu yawa kan ki tafi,, yasanta dasan kifi shiyasa. tsoka day'a ta dauka sannan ta yi musu saida safe ta shiga can cikin gidan a falo ta samesu nan ta gaisheda alhj Muhammad da momy ni'ima sannan ta koma can gefen momy ni'ima ta zauna. sun dan jima suna fira a tsakanin abokan sannan da suka tashi tafowa sukayo musu rakiya suma har bakin gate momy ni'ima tace "hjia umaima imsha Allah gobe zan shigo ganin dan nawa,, to shiknn hajia ni'ima Allah shi kaimu lpia. a haka suka bar gidan suka koma nasu. Annah da dady mua'zzam suka wuce room dinsu yayinda momy umaima tace "ummu wannan dakin da kike shine naki kinji ko? gyada kai ummu tayi tace "to mah" Yawwa ummu na to kije ki kwanciyar ki sai da safe ko? "to momy Allah tashemu lpia" "Ameen ummu. a dakin kuwa ummu ta jima tana sake kallon tsaruwar sa da kyansa, ba wani abu bane mai tarkace a cikinsa ba iyaka gado ne mai lulube da tattausan beedshet akai, sai durowas da mirow harda dan qaramin deep freezar sai kuma can 6angaren toilet dake gefe. kwanciyar ta tayi tareda lumshe idanun ta ciwon mahabeer ne kawai ke ranta a lokacin tasan sam baida kirki mutumin nan tarasa ya zata kaya tsakanin su inya warke, anya kuwa zai barta kamar yanda mah din tace kuwa??? qara gyara kwanciyar ta tayi tareda sake lumshe idanun ta tanata irin tunanin nata a haka barci yayi gaba da ita cikeda mafarkai ciki kuwa harda na mutimin nata. tsawon sati 2 mahabeer yana Yana gida baije ko ina ba yana jinyar qafarsa yayinda ummu keyin kaffa kaffa dadud wata hanya da tasan zata hadasu,,yayinda kullum hannat tana manne da gidan,, Kullum Ummu saita je ganin mamanta da baffanta in ta gama ayyukan ta,,, yau ta kama juma'a ne ummu ta gama girkinta da momy umaima tace tayi mata jefin dan wake dan Yau jikin nata ya motsa batajin dadinsa sosai gashi dady mua'zzam bainan yaje dubai annah kuma tana dakin ta tana hutawa. lokacin ta koma dakinta tayo wanka ta shirya cikin kayan da momy umaima ta bata jia wato wannan riga da wandon fakistan din sai rawa sukeyi kuwa a jikinta. babu wani make up a fuskarta shiyasa fuskar tayi fiyau abinta gwanin sha'awa. parking gashin ta tayi gefen kanta sannan ta dauki mayafin kayan ta nada sa akanta nan da nan ummu tasake fitowa da usulin kyanta babu wanda zaiga ummu bai ji buqatuwar cewa ta zama mallakin sa ba. fitowa tayi tashiga kichen ta dauko abincin momy umaima ta nufi dakinta tayi sallama ta shiga ganin bata nan ne yasata tunanin kotana wajen annah mafarin knn ta juya ta koma dakin annah dun, anan tasamesu zaune suna fira, har cikin ran ummu taji dadin ganin yanda mah din tasamu lpia ba kamar d'azun ba. zama tayi tana 'yar dariya dariya ta murna bayan ta gaida annah tace "mah gashi na gama danwaken da kikace" "kai ummu nagode fa sosai naji dadin ganin dan waken nan yanzu yanda niketa jin kwadayin nan dan na zata ma sai dare zaki yi mana" Murmushi ummu tayi tace "annah kin iya cin dan wake ma kuwa? tayi maganar a tsokane dan itama yanzu ta saki jikinta ta mayar da annah kakarta,,, "lalala ummu karkice zaki biyewa mahabeer na fa kuna tsokanar mun uwa" cewar momy umaima tana dariya itama,, annah cikin raha tace "rabu dasu umaimatu,,zanyi maganin sune a gidan nan ay, hijira zanyi gobe in koma katsina sainaga wanda zasu tsokana,,fiddo fararen idanunta ummu tayi tareda ruqo hannayen annah