Sashe 103
Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sosai kuma, lokacin kusan komi na rayuwa nike masa hatta ciyarwa nike surho da aikatau in dinga ciyar dashi dan 'yan uwanmu ba kulawa suke damu ba inda bamu dashi wai. ana haka wataran na wayi gari ran baffa na yayi halinsa naci kuka harna gode Allah haka nai ta binsa da addu'a, ni day'a naci gaba da zama a gida dan 'yan uwa babu wnda ya yarda naje na zauna a gidansa,, nikuma shine nayi qudarin koda zan mutu saina zo nan birni na fad'a muku boyayyen zan cen nan, dan haka yau da safe nai sallama da yan uwa akan cewa zanyi dan tattaki haka na hau mota natafo saida magrib na iso nan garin nakuma je can tsohon gidan naku nagamu da maigadi yace hjy laria din bata nan nace masa wajen hjy ni'ima nazo ay daman nan yace kun tashi har yaimun kwatancen inda kuka koma to kuma akan hanya tane ta tafowa nan gidan har na qetaro titi kenan wannan hatsarin ya ritsa dani to kunji yanda abun yake" kowa ya tausayawa rayuwar innah indo anan falon momy ni'ima ta dage akan sai sunje gidan marayun amman dady Muhammad ya hana yace su haqurarwa zuwa gobe in AllAh ya kai da rai da lpia dan yanzun dare yayi har 12 ta wuce. dole ta haqura suka barsa sai goben. daren ranar daga dady Muhammad har momy ni'ima babu wanda barci ya ga idonsa dan farinciki dakuma q'aguwa gari ya waye kosa sa d'ansu a ido suma abun shekara da shekaru. wanshekare tun qarfe takwas na safe dukkan kafatanin iyalen mua'zzam saraki sune suka raka su dady Muhammad zuwa gidan marayun tun akan hanya ganin gidan marayun da aka dosa yasa gaban su dady mua'zzam dana mm umaimah fara dokawa kuwa suma, basu qara tsinkewa ba saida suka shiga office dinda rabonsu dasuka shigesa sama da shekaru knn tun randa sukazo aka basu jinjiri basu qara zamnsa ba inba yau ba, nan annah ta basu cikakken bayanin itace wacce takawo ajiyar yaro a shekarun baya..... nanta warware ma mutumin komi da lalurin daya hana ta dawo karbar yaron kan kari sa6anin yanda tai musu magana akai na zata dawo karbarsa nan bada jimawa ba in komi ya lafa . dudda tsufa da annah ta qara sosai amman hakan mlm mukhtar bai hanasa gane itace wacce ta kawo mahabeer ba a rud'e @ shekarun baya ba,, nan ya aika nani tazo itama yai mata bayanin kowacece aiko itama nan ta gane inna indo nan aka d'auko littafin da suke sa dud wani history na yaron dake cikin gidan dakuma wand suka kar6esa ,,a hankali cikin nutsuwa mlm mukhtar ya dago kai ya dubi su Dady mua'zzam ya kuma dubi Dady Muhammad, girgiza kai yayi snn yayi dan Murmushi yace "Alhamdulilla aboki ya rainarwa dansa d'a knn? kai masha Allah,, cikin rashin fahimta dady Muhammad yace "ah nifa bn gane ba mlm mukhtar? kan mlm mukhtar ya ce wani abu tuni har dady mua'zzam ya katsesa da cewa "hmm nasan daman komin kuwa daren dadewa gskia zatayi halinta, shuruya danyi sannan yace "haj Muhammad kamar ynda mlm mukhtar yace aboki yayi rainon d'an abokinsa to haka abun yake dan ni dama tunda naga mun shigo gidan nan kuma mun shigo office din nan nasan magana ta qare... nan dady mua'zzam ya fad'a musu ynda sukazo suka karbi dan nasu mahabeer a lokacin, yana gama fad'an hakan ya juya ya dubi mahabeer daya daskare a wajen jin abinda ke wakana kamar a mafarki,, dafa kafadarsa dady mua'zzam yayi yace "sojana komi kaji hakane dan tabbas ranar wanka ba'a b'oyen cibi dadyn ka Muhammad da momyn ka ni'ima sune asalin iyayenka ba muba kamar dai yanda kaji komi an maga warwaresa yanzu a gabanku" dady mua'zzam yaqarashe maganar tareda share qwallar data zubo masa sannan ya miqe tsaye ya kamo hannun mahabeer ya kaisa ya zaunar gabansu dady Muhammad da momy ni'ima yace ga d'anku nan ya dawo hannunku kamar yanda muka d'au alqawari wato idan iyayensa suka bayyana zamu miq'asa garesu" mamaki kawai ummu hani keyi momy ni'ima kuwa tsabar farinciki kamar ta zuba ruwa qasa tasha daman yanzun ashe kenan mahabeer dansu ne? ashe sonda take masa har cikin ranta ba banza ba son d'a da uwa ne? sujada kawai tayi qasa tana cigaba da yiwa Allah kirari da godia. kuka kawai momy umaimah ta fashe dashi aiko da sauri mahabeer yayo kanta ya rungume gefen jikinta yana zybda hawaye shima ganin abun zaiyi yawa yasa su dady mua'zzam da Muhammad sukayi bankwana da su mlm mukhtar bayan sunyi abinda ya dace sannan suka dunguma sukayo gida nan aka zazzauna falo annah kam kasa cewa komi tai itama dan a boye take goge hawayen fuskarta dan sabo kam yafi qarfin wasa bare nasu sabon da mahabeer tun abun yana jinjiri gashi yanzun harya girma yazama cikakken mutum dole ne kuwa suyi kuka. nan falon ya d'auki shiru saidaga bisani dady Muhammad ya dauki wayarsa ya bugawa hjy laria yace komi takeyi tazo nan gidan alhj mua'zzam abokinsa yana jiranta yanzu yanzun. ba'a jimaba kuwa sai gata ta shigo falon gidan itada qanwarta hjy safia. wajen zama suka samu suka zauna ta tsorata kuwa hjy laria sosai ganin irin wani wulaqantaccen kallo da dady Muhammad din yake aika mata dashi. dady Muhammad ya nuna mata inna indo yace "kokin shaida wannan baiwar Allahn? sai da hjy laria ta qare mata kallo sosai sannan ta dafe qirji da hannuwa bibbiyu tace "na shiga ukku ni hjy laria daman indo kina raye su goga sukace sun kasheki? daura hannuwa tayi bibbiyu saman kai jin da tayi subutar baki dan rudewa, dady Muhammad yace "kaicon ki muguwar mata to d'ana mahabeer da kikai burin kashewa to Allah ya nufa bai mutu ba gashi nan zaune daram a gabanki a raye cikin rayawa ta Ubangiji Allah" yayi maganar yana nuna mata mahabeer dake zaune kansa na masa mugun ciwo da sara,, sannan yace "kuma billahel azeemu koki fadan gskia ko yanzun nan kijiki prison dan wlh d.p.o. zaki gani yanzun nan ganin idanunki yatasa mun qeyarki gaba kuma wlh har duniya ta nad'e ba zaki fito ba a gidan jarin din ba zakita zama har kita girbe mugun irinki da kika dad'e kina shukawa saiki zauna can kita cin amfanin girbin naki har illa masha, fashewa tayi da wani kukan dantasan komi yace tofa saiya aikata inka layance masa gskiar da ya nemi ji wajenka dan kaifi day'a ne shi tasan da hakan kuma tuni shiyasa dud iskancinta batayi a gaban idanunsa ko, a tsorace tace "ka yafemun alhj wlh zan fadi gskia wlh dud sherri shedan ne ne,, daka mata tsawa alhj Muhammad yy yace "karkice mun wani shedan ne hjy laria wlh kema muguwar shedaniyar kanki ce nasan da hakan tuntuni qyaleki kawai nikeyi dan haka maza imun maganar ynda kika shirya sauran shi tuggun naki ina sauraronki. cikin rudaddiyar murya hjy laria tace "lokacin da muke tsara zamu dauke jinjirin domin muje mu kashe sa kawai sai mukaga alamun mutum ta bakin qofa a wajen, na tura safiyya taje taga waye tana fita taga indo ce a wajen tsaye sai taga indo din tayi saurin wucewa jin motsin zaa fito knn,, nikuma koda ta fada mun hakan na tabbatar da cewa lallaikm taji sirrinmu mafarun knn na ajiye qudurina na sace yaron da niyyar saina koyawa indo din hankali sannan in dawo ga yaron, katsam naji labarin babu yaro daga baya naji ance itama indo din ta koma garinsu nan nasa akaimun binciken garin da indo take da zama da kuma gidansu, ba'a jimaba muka gano hakan kuwa shiyasa natura aka saceta akaimata duka dan kawai in huce hushina to wannan shune gskiar mgn dan Allah alhj ka yafe mun bazan qara ba na tuba nabi allah nabi ka". girgiza kansa Dady Muhammad yayi yace "ina takuma q'are gskia ta fito bori kuma yakar boka wlh harga wllah hjy laria bazan cigaba da jurar munanan halayenki ba dan haka kije na jnye sauran igiyar aurena akanki inda daman nata b'a yimiki 2 a baya ynxun ga dayanki nn na cika miki" ai da gudu hjy laria ta kwasa tayi waje tana kururuwa da fadin "Allah ya isa bata yafe ba an cuceta kuma dukiya ce tayagi iyakar rabonta danmi inya saketa aiba shine autan maza ba" ahaka safiyya tajasu suka tafi sai tsinewa indo suke ganinsu itace dud ta jaza musu wannan masifar to'an saketa hankalinsu ay ya kwanta matsiyatan itada ni'ima din. tun a hnya ta kira masu kwashe kaya dan tayi alq'awari ko kwana daya bazata qara gidan saba tabar masa tsiyatakunsa yazo yayi dud yadda zaiyi dashi "munafikin shima", cewar qanwarta safiyan. acan kuwa dady Muhammad ya dubi Dady mua'zzam yace "kada ku damu abokina mahabeer dan mu ne mu duka dan haka har yanzun hannunku yake dan ko babu ranmu kai mai riqe mana shine, burunmu yacika inda mun gansa da ransa bawai ya salwanta ba, dan haka kada kuji komi zaici gaba da zama hannunku inda dud ana tare",, dasauri mahabeer ya rungume dady Muhammad cikin murna hakama yaje wajen momynsa ni'ima ya matse hannuwanta ya kwantar da kansa a bayanta yanajin wani farinciki idanunsa na sauka ana annah ya dage mata gira ta yi Murmushi tace "ja'irin gske kaiko? dariya duka falon sukayi momy umaimah da ni'ima sukace "kai annah keda jikan naki" Murmushi annah tayi tace''a'a nabar muku kuyita kaya" daga haka ta shige dakinta nan dady Muhammad yace "to hj mua'zzam yaushe diyar tamu zata tare gidanta? Murmushi Dady mua'zzam yy yace "ko gobe yy ko? Inda yagama komi na gidan nasa anan bayanmu gidan yake". da sauri momy umaimah tace "a'a nuree abamu sati daya sabida mu shirya yar tamu muma kam,, murmushi su dady kawai sukayi suka cigaba da firarsu ta abubuwan da suka faru a rayuwar tasu duniya kenan. yayinda mahabeer yafaki idanun su dady ya kashewa ummu hani ido aikuwa ta sumburo d'an pink lips d'inta ta dauki baby manal ta shige dakin momy umaimah ya bita da kallo yanda yaga mazaunanta na jujjuya shiyasa yaji hankalin sa ya daukantu harda hadiye yawu, saida momy umaimah ta bugo hannunsa tai masa alama dasu dady na wajen sannan ya