← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 109

Sashe 58

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🌊🌊🌊🌊🌊 🅿4⃣0⃣ 🌊🌊🌊 idanun ta a runtse suke gam jikinta na kyarma, dai dai lokacin mahabeer ya iso gareta tareda damqe kafadunta biyu da hannayen sa yana girgza ta da qarfi tareda dauketa da wani lafiyayyen mari jikake tassss,!!! da qarfi ummu hani ta qwalla uban ihu dan jin tsananin yanda azabar zafin marin yayi mata shigar bazata, ingijeta yayi tafada jikin qyauren toilet din saigata cikin toilet tayi qasa warwas tana zaro idanuwa. ganin datayi ya shafa jikinsa yaji babu belt taga ya nufi inda cazar wayarta ke jone ya fizgota da qarfi yayo kanta, da gudu kuwa ta yunqura ta miqe tsaye ta banko qofar toilet din ta saka lock ta jingina bayanta da jikin qofar tana sauke ajiyar zuciya banda tsinewa mahabeer babu abinda zuciyarta keyi hannunta na bisa kumatunta tana sosawa da akaifu, da qarfi taji yana dukan qofar yana cewa"ki bude kofan nan wlh nagaya miki, banzar yarinya kamar ke har kin isa ki fiddo mun jini ga jikina?! tana jinsa tayi banza dashi haka yaita dukan qofar amman ko girgiza baiba qofan dole yasashi yayi q'uta tareda yarda kebel din cazar ya bar wajen ya koma d'akinsa ya shiga toilet ya wanko jinin da leben nasa ke zubarwa yasa d'an magani a wajen tareda kwanciya bisa gadon zuciyar sa kamar zata fashe masa kuwa dan baqin ciki, yana cikin wannan halin quncin ne harya samu barci yayi galaba a kansa. a toilet kuwa saida ummu hani ta tabbatar da fitarsa sama da awa daya sannan ta samu cikin sanda ta fito daga toilet din tayi saurin murzawa qofar key ta dawo ta zauna gefen gado tana qyalqyata dariyar oho dai, danko ba komi tai masa abinda tasan zai kwana cikin baqin ciki shima yau, baqin cikinsa da rashin walwalarsa shine cikar burinta daman, haka ta kwanta cikin farin ciki da annashuwa. washe gari da safe suna zaune falon qasa itada nabeela da momy harda annah saiga dady mua'zzam sun shigo shida dady Muhammad baffa kaddo na bayansu, nan su annah suka gaiggaisa dasu sannan dady mua'zzam yace "daman dai akan maganar mahabeer ne da ummu hani shine naje wajen baffan nata nida alhj Muhammad muka gaya masa batun kuma shima cikin ikon Allah yayi wa mahabeer lamunin auren ummu hani, inda dai ita din ta amince kamar yanda ya buqaci jin hakan daga garemu ya fahimci kuma daga ummu hani din har shi mahabeer babu wata matsala a tsakani mafarin kenan annah harya biyomu nan dan yai muku godia sabida gobe ne zasu koma gida inda alhj Muhammad yasamu madadin sa". annah tace "to baffa mun gode Allah bar zumunci" baffa yace "mukeda godia annah haqiqa ba mutane da yawa sukeda halinku ba na kyautatawa al'ummar annabi ba, mudai tsakanin mu daku sai godia Allah saka muku da mafificin alheri, "amunn" cewar su. Alhj Muhammad yace "to baffa gobe insha Allah zamu bika qasarku dan suma sauran dangi da 'yan uwa naku susan da zancen shirye shiryen auren, kuma baffa muna neman alfarma zuwa juma'a mai zuwa ta kasance itace ranar d'aurin aure na yaran sabida tafiyar da zasuyi din dud cikin satin nan take itama" shiru baffa kaddo yayi zuwa can yace "to masha babu komi Allah shi kaimu lokacin darai da lpia". da "aminn" kowa na wajen ya amsa, duban ummu hani nabeela takeyi wacce tunda aka fara maganar nan bnda wani irin futinannen faduwan gaba babu abunda ke shigar ta kanta na duqe qasa ko qwaqqwaran motsi ma ta kasayi. baffa yadan jima nan sannan ya koma,haka su dady sukai masa rakiya. ganin yanda ummu hani take takure yasa momy umaimah taita jansu da fira har saida taga ta dan saki jikinta sannan tace "kuje wajen momy ni'ima ku karbo mun saqo kunji ku 'yan albarka, dato suka amsa tareda miqewa tsaye suka bar falon, suna shiga falon gidan kuwa suka isketa zaune a falon tana kallon tashar sunna tv. gaisheta sukayi suka zauna bayan sun fada mata saqon momyn. cikin murmushi tace "to twince din umaimah ku jirani kadan ina zuwa,, wata yar qaramar hanya tabi ta wuce bedroom dinta bata jima ba sai gata hannunta daukeda wata leda mai sheqi qarama ta miqawa ummu hani tace "to gashi sai ku kai mata ko, nabeela tace "kai momy kin iya girki, dan wlh tunda na shigo falon nan muke jin qamshi ko ummu hani? d'an mintsininta ummu hani tayi cikin rad'a tace "kin fiye surutu sister, haka nan ummu hani taji tana tsananin jin kunyar momy ni'ima a yau fiye da kullum ma, ita kanta batasan dalilin ba. momy ni'ima tace "kaji nabeela Friedrich ce nikeyi nd vegetables kuma nasan yanzu ta ma ida dafuwa ku zauna na zubo muku, da sauri ummu hani tace "a'a momy munma qoshi ay, nabeela tace "tab sai naci nikam, kuma wlh momy itama tana son Friedrich kawai dai tsirfa ne irin nata, hararar nabeela kawai ummu hani takeyi a boye, momy ni'ima tace ''ah haba 'yata ummu ki saki jikin man kibar d'ari d'ari nanfa gidan kune kema, keda yadace kikawo wani yaci amman keza'ace ana fama dake ma ashe?, sunne kai ummu hani tasa keyi qasa sosai tana sakin murmushi tareda murza zara zaran fararen yatsunta. tashi momy ni'ima tayi tace "yawwa kokefa amaryar d'ana mahabeer insha Allah, bari na dawo, tana fita ummu hani ta dubi nabeela tace "nashiga uku sister kinji itama tasani ashe?!, nabeela tace "toya sonki sister? aminiyar mah cefa ita d'in taya kuwa zataqi sani? momy na kanta ta buga mata waya ta sanar da ita yarinya dan jia dana fito daga dakinki bayan kin kulle knki toilet din nan to ay nan falo na zauna wajen mah din har naji tana waya ma tana sanarwa mutane bikin harda maman wannan banzar hannat din, waike kin zata mah ta dauki maganar bikin nan naku da sanya? tab agaishe ki to" shiru ummu hani tayi takasa furta komi, momy ni'ima bata dau mintoci ba sai gata ta dawo da qaton plate cikeda abinci wanda yaji tsokokin kaji kota ina ciki sai tashin qamshin dad'i yake, da juns a gefen plate din abuncin kala kala shima tace ''yawwa yarana tom ku sauko yanzun nan ku cinye sa tas kafin na dawo,, ahaka ta fita da kular abincin su baffa danta kai musu suma kamar yanda ta saba kullum. tana fita nabeela tace "sauko sauko mici sister dan so nike muje gida in gwada miki wani suprise, dubanta ummu hani tayi tace "suprise wane iri kuma knn? murmushi nabeela tayi tace "kedai yi shurunki koma miye kya gani da idanunki, haka suka fara cin abincin suna fira sai ga momy ni'ima ta dawo tace yawwa ku cinye tass saina qara qaro muku ma, zaro idanuwa ummu hani tayi tace "laaaa a'a momy jinake ma cikina ya kusan fashewa dan tsaban cikarsa". nabeela tace "bawani nan kinji ta momy cikinta fa wlh intaci abinci ko dagowa baiyi shafe zaki gansa kamar ma irin bataci komi ba amman kinji tana cewa wai cikinta zai fashe dan cika... maganar nabeela ta katse jin an banko qofar dakin da qarfi an shigo, wata gajerar mata ce baqa sosai mai uban jiki taci adonta sosai na wani uba uban less ja, ta yafa gyale a saman b'arin kafad'anta tareda kashe kallabi kamar wata 'yar bariki tana tafiya cikin taq'ama jikkarta a sagale ga hannunta tana qwas qwas da takalmanta tana tauna cwingum qas qas a haka ta shigo cikin tsakiyar falon gidan tana harare harare ko sallama batai ba, Momy ni'ima na ganinta saida taji gabanta ya buga sosai dan yau batasan wane kwandon masifar hjy laria (kishiyarta) tazo sauke mata ba, a hankalin ta bude baki tace "hjy laria sannunki da zuwa ga waje nan ki zauna,,katseta hjy laria tayi cikin masifa da cewa "ke dalla niki rufa min baki haka nan kinibabbiyar mata kawai kinbi kin shanye mun miji sai kin ga dama sannan kike sako mun shi yazo wajena ko? , to wlh bari kiji dud irin asirin da kike zabga masa inada labari kuma wlh ki kuka da kanki kamar yanda nasa akaimun maganin wannan shegiyar 'yar aikin naki indo har can garinsu na tura akaimun maganinta to kema wlh ki kuka da kanki danni ba'a takani a zauna lpia a rayuwa! , tana gama fadin haka ta juya zata bar wajen saita dawo falon da baya kadan ta nuna momy ni'ima da d'an yatsanta manuni tayi mata tas tas dashi tace "kuma wlh in kika kuskura yau banga mijina cikin gida na ba nima saina lafira ya fiki jin dadi banza dangin mayu kawai",, tana kaiwa nan ta fice daga falon harda bugo qofa da qarfi bumm! nabeela ta dubi momy ni'ima tace "momy wannan kuma wacece haka? murmushin takaici momy ni'ima tayi tace "abokiyar zama nace hjy laria, ummu hani tace "to shine take miki haka wannan cin mutuncin momy? girgiza kai momy ni'ima tayi tace ni ai nasaba da ganin irin haka ummu hani sama da shekara da shekaru kinga kuwa ai yaci ace na saba da halinta ko, shiru sukayi duknsu kowane da abinda zuciyar sa ke saqa masa na gameda rashin mutunci irin na hjy laria. ganin kamar sun shiga damuwa yasa momy ni'ima ta canza zancen da cewa "kufa cinye abincin nn ko qwara bn son ganinsa a plates dinnan" tayi maganar cikin murmushi, haka suka ci abincin sosai da zasu tafi ta hada musu kayan makeup na sosai sannan suka wuce wajen su mama bintey sun jima can sannan suka dawo gida suka baiwa momy umaima saqon daga ban nabeela taja hannunta suka juya gidansu. a can kuwa momy ni'ima tana zaune a bedrom dinta tayi tagumi tun bayan sallar azhur da tayi ta fad'a zurfaffan tunani na hjy laria, hankalin ta tashe afili take tambayar mitaiwa inna indo kuma ni ni'imatu? kaiiiiii nashiga 3, kaddai tanada sa hannu daqin dawowar inna indo gidansu a lokacin? wai ita shin hjy laria da yaushe zata saduda da duniyar ne?, ita sam bata son rigima da tashin hankalin mafarin knn hadda hakan tasa taqi sake zamansu waje guda da ita hjy laria din amman Ashe gudun gara tayi zuwa gidan zago? hakan ma bata tsiraba knn??! tana cikin wannan zurfafan tunanin ne taji an zauna gefenta
Chapter 58 · 0% Book details