← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 109

Sashe 2

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Asalinsu...
Mu'azzam saraki shine cikakken sunan sa,
babban ma'ikacin government ne Wanda a q'alla Albasshinsa duk wata zai tasamma 5 million, sannan gefe guda ga manyan kasuwancin sa da yake yi na shigo da gold, diamond. motoci, yana saidawa 'yan kasuwa, sannan kuma ga gidajen mansa Suma Sama da guda 15,
shiyasa kaf fad'in nijeria babu inda zakaji an ambaci sunan *Alhj "mu'azzam saraki*" ba'a san shi ba,
Yana yawan zuwa kai temako a gidajen marayu, isslamiyyu, data Almajirai, haka nan inya samu change yakansa direbensa ya jasa ya kai sa anguwannin dayasan akwai talakawa sosai mabuq'ata ya dinga yi musu kyautar ban girma Harda masu muhalli duk yana basu wa marasshi, irin wadanda ruwa ya zubdawa gidaje,
Shiyasa har murna suke marassa q'arfi ace yau ga Alhj mu'azzam saraki yazo sunsan ranar take salla a wajen su, dan zai basu abinda zasu yi shekara 3 dashi suna juyawa dan kasuwanci,/ noma, ammanfa ga masu burin cikinsu,
Shiyasa addu'a kullum Shanta mu'azzam saraki yakeyi a maban bantan bakunan Al'umma.
Asalinsa d'an katsina ne, mahaifinsa Alhj muntari saraki ya rasu tun yana Q'arami, a hannun mamansa hajara ya taso wacce yake kira da Annah, Ta haihawa kafinsa Amman duk Allah yayi musu rasuwa yaran tun suna q'ananu,
mu'azzam ne yayi tsawon rai cikin rayawa ta ubangiji Allah.
Cikin dangi suke luntsum shiyasa mua'azzam Sam bai san maraici ba, Allah yabasa dangin baba da mama masu zuciyar yi.
Q'anen mamansa shine ya tsaya kan karatunsa har ya girma ya had'asa aure da babbar d'iyarsa umaimah dashi mu'azzam d'in ya nuna yana sonta Wanda dama itama umaimah hakan yake a cikin zuciyar ta.
Lokacin har ya fara Aikin gwamnati harma ya gina gidan sa plate house mai kyau, anan suka fara zama kusan tsawon shekaru 12, sannan akai masa q'arin girma Wanda hakan ya kaisa aiki garin Kaduna shekara 5 kenan da komawar tasu kd, Wanda tun tsawon shekarunn nan Allah bai basu haihuwa ba, lokacin arziq'in sa kuma sai q'ara bunq'asa yake,
Duk bayan lokaci sukanje katsina su d'auko Annah tai musu kwanaki a gidan takoma can katsina,
Bacin sunyi sunyi da ita kan ta dawo gidan da zama taq'i fur, sai dai a zuwan tazo musu Hutu ta koma can.

Wanda yau kwananta 11 kknn da zuwa gidan d'an nata Hutu,
dan su kansu 'yan uwansa ba q'aramin cin arziq'in Alhaji mu'azzam sarakin suke yiba,
Wannan kenan.

***
Washe garin ranar ta Asabar dukkan su 2n mua'azzam saraki da matarsa umaimah suka dinga jinsu cikin farin ciki haka nan, bayan sun gama break fast ne nan umaimah ta shige jikin Annah tanawa mu'azzam gwalon tarigasa d'alewa jikin Annahn tasu.
Lokaci d'aya kuma ta tashi tace "yawwa Annah daman nai niyar bazan fad'i wannan mafarkin nawa a gabnsa shi d'aya sai anan gabnki, dan wataq'il abinda Nike so yai mun kmr ynda nasa rai zaiq'i amin cewa ammn in agabnkine zakisa yayi mun"
ta q'arshe maganar kanta a langwa6e.
dukkan su daga mu'azzam saraki har ita Annah sun zubawa umaimah ido da tunanin mita mafarkato??
Annah tace
"to shiknn 'yata fad'a muji muna sauraronki,
Cikin sunne kai qasa umaimah tace
"Annah jiya ne nayi wani mafarki,
Wato bayan munyi nafilar dare mun kwanta barci,
Nayi mafarki ne wai gani da wani yaro ga hannuna Wanda bai wuce shekara 3 ba, wlh Annah yaron kyakkyawan gaske ne kuma,
nazo wucewa nagansa zaune cikin wasu yara da yawa suna wasa, yana ganina yazo da gudu ya rungumeni kamar ya sanni yana fad'in "Mammy na !" "Mammy na !"
zan zauna dake,
ki kai ni gidan ki wajen babana....!!!
"Annah wlh nan muka zauna da yaron cikin yaran munata wasan tare Amman yaron nan yana manne jikina nima naji banson rabuwa dashi,
Dan a lokaci d'aya naji q'aunar yaron a raina, to muna nan zaune zuwa bayan wani lokaci saiga wata mata tazo ta kwashi yaran har dashi yaron Wanda da q'yar ta samu yabar jikina suna tafiya naga yanata waiwayena tareda mun bye bye,
nima bnsn snda na d'aga hannuna ina masa bye bye ba, har naga sun shiga wani babban gida Wanda naga an rubuta a saman gidan saman wani q'aton symbol, *GIDAN MARAYU*,
to kuma a dai dai nan na farka hankalina a tashe ,,
D'an dakatawa tayi sannan ta miq'e zaune tayi durq'uso a gabnsu tareda had'a hannayenta biyu muryarta na rawa taci gaba da cewa "Annah? nuree? dan Allah Ku yarda Ku amince muje gidan marayu mu samo yaro Wanda zai yayemun damuwar rashin q'waina a duniya, wataq'ilama ta sanadiyyar kulawa da marayan Allah ya jiq'anmu ya bamu namu rabon, Dan wnda ya temaki mabuq'aci tabbas Allah bazai q'i saka masa da mafi alherin sa ba,
Annah nasan kunsan haka kuma, dan Allah Ku amshi q'oqon barana da nazo muku dashi" magana takeyi wasu siraran hawaye na sauko mata a fuska.,
dukkan su sunyi tsit Sai Annah ta dubi mu'azzam saraki shima ya dubeta kuma,
Duban umaimah Annah tayi tare da girgiza kanta tace....

Xayyneb💤💤 .
[10/11, 2:44 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊

Story and writing
by
Xayyneb 💤💤

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.
Chapter 2 · 0% Book details