← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 109

Sashe 25

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

dayake ita yau bata jeba asibitin cewar dady mua'zzam d'in ta zauna itama ta huta tunda yaune zasu dawo gida suma,,, baffa kaddo da bintey kuwa sai bin gidan sukeyi da kallo dan tunanin su babu irin wanan hadadden gida a nan inba qasashen turawa ba,, ita kuwa ummu tana daga gefen mommonta tsaye danji takeyi kanta na sarawa kadan kad'an idanunta sai faman lumshesu takeyi ahaka suka qarasa har falon gidan,,, sun zauna momy umaima ta cika musu gabansu da kayan lashe lashe daqyar suka samu suka tsakuri kadan dan ba sabawa sukayi da irin abincin ba,, dama ita Ummu yau monday azumi takeyi koda Anna tace ke Ummu baxakici komi bane? kinfa zama 'yar gida kibar d'ari d'ari dan Allah dud daya nefa Allah ma bai banbanta ba dud abin halitta ne daga garesa,,, ,,, qara sunne kai tayi tana qara jawo mayafinta cikin Murmushi tace "si annah azumi nakeyi yau litinin shiyasa,, "annah tace "ohhh Allah sarki yarinya mai ibada,,, nima azumin nan nake yau,, allah shi bamu ladan to,, aminn su baffa da dady mua'zzam suka amsa,,, momy umaima tace "ni wannan lullu6e naki ummu da kikesha narasa gane kansa,, incan asibiti kin boye fuskarki aimu nan sai a saki jiki a bude ko??? tayi maganar da Murmushi a fuskarta,,, baffa yace"Allah sarki hajia ai ita ummu hani haka take ko gida bata cika zama haka ba,,, murmushi kawai momy umaimah tayi ta qudure a ranta lallai zata mayar da yar tata kamar kowa ce cikakkiyar budurwa indai ana kwana ana tashi,,son ummu hani jitakeyi daga cikin jinin tane yake,,"toni zan shiga ciki cewar annah tareda miqewa tana fad'in "bismillahee Allah wahidul qahhar,, bin annah da kallo momy umaima tayi lokacin dataga tashin nata ta koma daki tasan salla zatayi sannan shima dady mu'azzam ya tashi yacewa su baffan su tafo ya kaisu gidan maqocin abokin nasa inda zasuyi aikin,,dukkansu sukaje harda momy umaima d'in sunyi saa alhj Muhammad d'in na nan nan suka tarbesu suma sannan daga bisani suka gwadawa baffa dakinsa na bakin gate wanda zai dinga kwana shida iyalensa, babban daki ne daukeda kujeru guda 5 da carpet inka dauke masaukin baqi dake gefen dakin nasu,, sannan cikin dakin akwai qurya mai daukeda gado sai katifa a qasa harda makewayi keda a cikin dakin da dan qaramin kicin shima,, anan su dady mua'zzam suka wuce masallaci shima baffa yayi alwala ya shimfida buzunsa nan wajen gate daga gefen benci ya tada kabbara shima ta salla,,, acan cikin daki momy umaima ta jira saida su bintey da ummu suka yi salla sannan tace"to nima zan tafi da 'yata a namu gidan mamansu,, tayi maganar fuskarta a sake,,, dayake bintey tasan itama ummu hani d'in zata zauna can wajen momy umaima d'in dan tayata wasu ayyukan shiyasa itama cikin faraa tace "to shiknn hjy mungode da kulawar da kukeyi damu Allah saka,,, amimm cewar Momy umaimah a haka taja hannun ummu hani suka fita daga gidan suka nufi nasu,,,, zuciyar ummu cikeda farin ciki na ganin cewa sun samu mafaka itada iyayenta sai fatan Allah shi ida nufinsu na ganin anwa mamanta aiki ta samu lpia,,, suna shiga kai tsaye 6angaren ta momy umaima tayi da ummu tace ta zauna nan zata dawo yanzun,,, ruwan wanka ta had'a mata sannan ta dawo ta kamo hannunta takaita har bakin qofar toilet d'in tace tayo wanka,,saida taga shigarta sannan ta dawo falow ta shiga wani daki daban inda kayanta suke na sawa ta fiddo wata farar doguwar riga msi adon duwatsu a gabanta da dan siririn farin mayafinta ta koma wannan gudan dakin data kai ummu tayo wanka ta dora mata su bisa gado sannan ta matso bakin qofar toilet d'in tace "ummu in kin fito ga kaya nan kisanya na ajiye miki su bisa gado,, ina jiranki a falow inkin gama "daga haka ta fita tareda jamata qofar dakin ita kuma ta wuce nata dakin dan gabatar da salla itama,,,,,,
Chapter 25 · 0% Book details