← Book details Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 109

Sashe 31

Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

cikin kalar murmushin ta tace "wasa nike anna zanje na kawo miki kema naki yanzu ay, dariya momy umaima tayi ita da annah kawai har ransu qaunar yarinyar kullum take qara shigarsu,, anna tace "aa ni bnjin yunwa ynzu nagama cin abinci" Marairaicewa ummu tayi tace "to amman in ajiye miki ko annah zakici anjima? cikin Murmushi annah ta shafa kan ummu tace zanci ummu allah dai shi miki albarka yanda kike dad'ad'a mana kina samu farin ciki a kullum,,ameen cewar momy umaima dataketa saka danwakenta a baki tana ci harda lumshe idanun ta tosshin yasha yajin daddawa da magi d.s sai qamshi yake. "Annah mah zanje wajen su baffa in gaishesu,, cewar ummu hani tana mai miqewa tsaye,, Momy umaima tace "to shiknn sai kin dawo annah ta qara da cewa "ki kuma gaishesu qwarai2" tana fita ta koma dakinta ta zura plate shoes dinta ta tsaya gaban mirow tana kallon kanta Murmushi tayi tasan in su baffa suka ganta haka tasan zasuji dad'i sunsan cewa hankalin ta na kwance ba kamar sanda suka shiga damuwar nan ba lokacin da suke nemn mafaka. dan siririn Murmushi tayi jin gyalenta ya dan zame daga baya sabida santsin gashin kan nata yasa tasa dogayen fararen yatsunta ta fiddo jelinayen gashin kanta guda 2 dogayen gaske baqi qirin dashi gashin sai shining yake. ta gaban goshinta ta sakosu har saman q'irjinta suka hau suna yawo,, maido da gyalen tayi ta yafa sa bisa kan nata sannan ta koma kichen ta d'auki kular abincin su baffa din tanufi waje. dayake momy umaima tace in zatayi musu girki ta dinga girkawa dasu baffan nata dudda acan suma ana kai musun nasu in momy ni'ima tayi, hakan da momy umaima tace ba qaramin dad'i ummu taji ba, a rayuwa burinta shine taga komi ta samu ko taci to suma iyayen ta susamu hakan shine cikar farin cikinta. daga nesa ta hangosa ta wajen swimming pool din wajen inda yar bukkar nan take yana zaune bisa kujera ya dora qafan sa guda biyun a bisa tebir din tsakiyan wajen,, hannunsa riqeda viju milk yana tsotsa ,, batasan dai su waye kusa dashi zaune ba, ga alama dai abokansa ne mazan,, rasa yanda zatayi ta wuce ta wajen tayi dan dole saita hanyar da suken ne zata fita. ta jima tsaye a wajen datai taga lokaci na neman qure mata yasa kawai ta yanko tikitin shahada tayo hanyar wajen nasu,,tun daga nesa ya zuba mata idanunsa yau tsawon sati 2 knn rabon daya yarinyar dudda burin da yaci nason ganin nata akan qudurin nasa,, tunani yake sonyi akan wane irin kalar hukunci ne waima ya kamata yayi mata danya huce haushin sa akanta amman kuma zuciyar sa taqi basa daman yin hakan ta hanyar shagaltuwa da yayi da bin yarinyar da kallo batareda ya ankara ba,,, ganin ta kusa isowane kusa dasu itama akayi sa'a ta dago idanunta nan da nan suka had'a idanu cikin sauri ya fara maido nutsuwarsa cikin jikinsa ya yamutsa fuskarsa cikin daure fuskarsa tamm tam saida ya danqaro mata wani zafaffen kallo wanda ya haddasa wa ummu wani iriyar faduwan gaba ba shiri shikuma yasake binta dawani banzan kallo na raini yana binta da wata hararar sannan ya janye idanunsa daga cikin nata yana sakin tsoki ya maida viju milk dinsa cikin saman lips dinsa yaci gaba da tsotsar abinsa. mukhatar cikin rawar jiki da da kyarmar baki ya tabo bash da Masud da imran yace "kai kutttttt,,, wowww gayu kun kalli kyakkyawar halittar dake tunkaromu kuwa a halin yanzu?, anya ba aljana bace takeson budemin ido inyi *gamdakatar* da ita kuwa ba a yammacin nan?, dubn inda mukhtar din yake nuna musu ne sukayi suna bin wajen da idanuwa suma,,,, babu wanda zuciyar sa bata girgiza ba da ganin yarinyar ba a cikinsu suma, nan da nan suka hau murtsuka idanusu suna tunanin anya kuwa ba Ubangiji Allah ne yasa yaci dasu da rabon yin mafarki daga day'a daga cikin matan hurul ayni ba kuwa? ji sukayi gaba day'a jikinsu yai musu sanyi a lokacin musamman mukhatar uban zalama lokacin daya tabbatar da cewa Lallaikm wannan mutum ce bil'adama abin hakitta. cikin qunar rai mahabeer yasa hannu ya daki table din gabansu hatta sauran milk din da cups dake akai saida suka rigizazo qasa suka watse,, da sauri suka maido hankalin su jikinsu shikuwa sai masifa yake tsattsaga musu da cewa "haba miye haka kukeyi dan Allah kuma mukhtar?? Kun wani kun sanyawa yarinyar mutane idanu dud salon dai kujanyo mana raini kuma? Yayi maganar ransa a matuqar 6ace wanda shi kansa baisan yaya hakan ta kasance ba,, dai dai lokacin ta ida giftawa ta wuce ta gefensu cikin d'ari d'arin da takeyi gameda mahabeer din,, saida ta wuce ne harta qulewa sannan suka maido hankalin su jikinsu lokaci day'a. sauke ajiyar zuciya mukhtar yayi yace "kamm bala'encan.. waiii zillaziya... duban mahabeer yayi yace "gifted daga wane duniya gidan nan naku ya samo mun mata ya kawomun har gida dan Allah fada mun gifted?? bash yace "kaji dan iska namamajo kakai maryam din ina?? saura kwana 3 fa a daura muku aure,,? "to dan yana saura kwana 3 in aureta ban iya fasawa ne kukega akan wannan zazzafar? kai kokuma in auresu duka ai addini ya yardar mun🤷🏽‍♂ ko? " Wlh kunji ma na rantse zan iya barin auren maryam Dan wannan zata ishi mutum komi basai ya qara wata ba, yayi maganar yana sake zuqo hayaqin tabarsa. Bash yace ''kaji dan iska kanata surutai ma kasani ko matar aure ce,,?? Mukhatar yace "ohhhshet..!!! daina mun fatar hakan dakuwa ba cutu wlh kajini da dan iska mugun bakinka ya koma maka to" dammm!!!!!,,,,,, mahabeer yaji gaban sa ya amsa da maganar da yaji bash yace wai may be itan matar aure ce. girgiza kai yakeyi samun kansa yayi a fili yana furta kalmar "noooooo mukhtar noo mukhtar,,, dukansu da kallo suka bisa shikuwa hannunsa yake kallo ganin yanda jini ke dan diga sakamakon cups din daya doka d'azun da hannun nasa harta kaiga ya yanke dan shi saima lokacin ya ankara da yankewar tasa. runtse idanuwan sa yayi gaam yayinda ya ciro farin hankicerf dinsa daga aljihun sa yafara qoqarin daure wajen dan jinin ya tsaya.....
Chapter 31 · 0% Book details