Sashe 55
Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
🌊🌊🌊🌊🌊 🅿3⃣9⃣ 🌊🌊🌊 Cikin muryan kuka tace "Wlh dady a rayuwata ba abinda na tsananta tsana face muhinmancin alaq'a dake tsakanin mutane taja da baya akan abinda baifi qarfin mutanen nan ba da suka roq'i abin ba daga gareka ba kai wanda kake tareda su din ba, sai nikega babu kyautuwa da har za'ace mutanen nan da kuke tare akan yarda da amana tareda q'aunar juna har sunemi wani abun daga gareka Kai kuma ace ka gaza yi musu abin nan sai nike kallon hakan a matsayin butulci ne, to kuma balle inaga yau ance mutanen da suka kyautatawa rayuwata data iyayena suzo suna neman Wata alfarma daga gareni wacce batafi q'arfina ba ace wai nakasa yi masu ita?, dady bazan so haka ba, nayarda na amince dady Wlh kama had'a ni da koma waye zan aura nasan bazaka badani inda zan dawwama a cikin cutuwa ba dady, har a raina nike jinka kamar baffa na, na yarda2 dady wlh zanyi biyayya akai ni kuma, bazan taba zama butulu a gareku ba"! tana gama fad'an hakan ta fada cikin jkn momy umaimah tana kukan dole, babu abinda take hangowa illa irin muguwar azabar dazata sha wajen amakson muddin ta auresa kuwa, towai yasanma da maganar mane kuwa,? wata iriyar azababben faduwan gaba ne ya kuma tsirgata dan gani takeyi suna haka ma acikin gida fad'a kamar kaji inaga sun yi aure kuma zasu qara kusantar juna ma alokacin knn fa? , qwamna nan gida intai masa laifi zata iya boyewa tsawon kwanaki taqi barima ko ganinta yayi ma to can fa? shida gidansa ta ina zata b'oye masa bai sameta ya nakad'e ta yacicci aniyarta son ransa ba? fashewa tasa keyi da wani kukan mai saka ciwon kai. mamakin kaifin basira da iya tsararrun kalamai daga yarinyar dady mua'zzam da annah kawai sukeyi, dady mua'zzam yace "to Alhamdulilla Masha AllAh Ummu yi haquri kidaina kukannan dn Allah inda har kin amince zanje na sanar da iyayenki kuma domin inji daga garesu suma kamar yanda na ji daga gareki kema, kitashi kije Allah shi miku albarka gaba dayan ku,, amunn suka amsa nabeela ta kama hannun ummu hani ta miqe tsaye suka haura sama zuwa dakinta suka bar su dady nan suna cigaba da tattaunawa carbin annah na hannunta tana lazuminta. suna shiga dakin nabeela ta daka wani uba uban tsallen murna ta rungume ummu hani tana qyalqyata dariya tana fad'in "waini Allah ya temakeni yau da naga idi zindir ummu hani na zata gudu garinsu ta barni da kewa, lokaci daya nashiga damuwa cikin ikon Allah kuma take a wajen Allah yakawo mana mafita, mafita wacce zatasa har kullum zan dinga jin ummu sister na kusa dani, kai naji dad'i wlh, maganar takeyi tana fad'awa saman gado cikin murna, fashewa da kuka ummu hani ta sakeyi tana cewa "wlh sister baki sona,, zaro idanuwa nabeela tayi bayan tatashi zaune ta matso kusa da ummu hani din datake d'osane gefen gadon ita kuma, nabeela tace "Kamarya ban sonki kuma sister dan Allah? dago da idanunta ummu hani tayi ta dubeta tace "eh man dakina sona bazakiyi murna da kasance wa mata ga amakson ba, bayan kinsan yanda mike takun saqa dashi bawani shiri mike ba bayya sona zalika nima kuma ban sonsa"! Murmanshi nabeela tayi tace "haba sister miye nawani batun so da bwakkwawa juna shi a yanzun? Ai kawai da kunyi auren zakiga kamar zaku cinye juna dan tsabar soyewa, nabeela tayi maganar cikin son tsokanarta, duka ummu hani ta dora mata a baya takuwa gantsare tana "washh! billahel azeem da zafi fa sister, harararta ummu hani tayi ta ci gaba da kukanta kamar wacce akace yau babu baffa kaddo da mama bintey. Cikin son sake tsokanarta nabeela tace "haba amaryar yaya amakson kiyi shiru mana kada kisa hawayenki suyita zuba kiwa yaya mahber asaran su,, da sauri ummu hani ta miqe tsaye ta shige toilet ta maido qofa ta rufe tayi zamanta acan tana qara bude sabon shafin kukan nata dan taga alama nabeela bazata barta ba taci kukanta ba ta qoshi yanda ranta yai mata tunkan ta koma hannun mugun can qwamma tafara trening din iya zybar da hawaye kala kala a cewarta, banda dariya kuwa baby abinda nabeela ke mata hakan kuwa ba qaramin qona ran ummu hani yakeba sai dai kaji taqara sautin jiniyar sabon kukanta din, nabeela ta koma bakin qofar ta murd'a ta jita a datse tace "haba sister na wai ke kuka bai miki wuya ne da sam bakya gajia dashi ne?, bakya tsoron kada ma kanki yazo yana ciwo kuma? ki fito haka nan please sister,, banza ummu hani tayi mata taci gaba da kukanta, nabeela tace "wlh inbaki daina kukan nan ba zanje in fad'awa su dady cewa gaki nan kina rufe kanki cikin toilet kinata kuka" aiko tana jin haka yanda kasan daukewar ruwan sama haka kukan da ummu hani takeyi ya bi sarkin shanu ya dauke daf, jin haka yasa nabeela tasaki Murmushi tace "yawwa sister kokefa, ki fito dan Allah to kinji ko? saima kiga dinku nan rigunan namu dan karbo mana su yanzun" sam ummu qin tankawa tayi haka nabeela tayi tayi da ita akan tafito amman sam taqi,, dole ta haqura tafita daga dakin kuwa. jin alamun ta fita ne yasa ummu hani din fitowa daga toilet din taje ta rufe qofan dakin ta dawo ta kwanta bisa gadon tana faman sakin ajiyar zuciya had'eda kukan zuci dan na filin ma ta gagara yinsa. mahabeer kuwa yana fita daga gidan kai tsaye qofar gidansu bleesing yaja burki da motarsa yayi mata waya da cewa gashi nan kofar gida,, nan da nan kuwa sai gata ta fito daga gidansu ta shigo har cikin motar ta zauna. yana duqe da kansa a styarin motar, a duniyar ne yarasa mike masa ma dad'i tukun, "hello my heart na what happened to you? tell me your problems pleass i hear you" a hankali ya dago kansa tareda kallon ta da jajayen idanunsa kaida ganinsa kaga wanda hankalin sa ba kwance ba, rai a b'ace fuskar nan a daure yace "ya kukayi da dadyn kine ya amince zaki musulunta dun koko? kallonsa kawai take tagaza gane kansa ita gaba ma daya tun xuwansa, daurewa tayi tace "Sorry my heart na wlh nayi nayi da dady yaqi amincewa amman mizai han ma mu gudu wani garin can sai muyi auren mu? ''Keeeee???!! ya daka mata wata firgitacciyar tsawa wacce batasan sanda ta fice daga motar ba ta fito waje tana zare idanuwan ta dan tunaninta duka kawai zai kawo mata a tym din. fitowa shima yayi daga cikin motar ya iso har gabanta cikin isar takunsa yaja ta tsaya, sake daure fuskar sa yayi sam babu d'igon fara'a a gareta hakan kuwa ba q'aramin qara fiddo masa wani fannin nasa na kyau yayi ba, dai dai gabnta yaja ya tsaya yace "miye amfani guduwan?! koni an gaya miki irin shashashan mazan nan ne masu b'ata hankalin su ga mata harsu gudu subar gida em? toni ba haka nake ba, kince kuma dadynki yaqi amincewa da musuluntar kiko? cikin sauri blessing tace "eh.. eh..cewa yayi ma zai yanka ni inna sake yi masa ma maganar musulunci, zuba mata idanunsa kawai yayi yana kallonta, da sauri kuwa ta janye idanunta daga nasa dan bazata iya jurar kallon kaifafan idanun saba takeji. wani tsoko yaja cikin takaici yace "Mtsssss ok no problem inda haka dadyn naki ya zartar amman kuma kisani wannan itace rana ta qarshe nidake relationship namu ya qare na wani so haka or something like this hope you undarstand me? Kuka bleesing ta fashe dashi ta zube qafafunta gabansa tana roqonsa akan yaci gaba da sonta itadai zata shawo kan babnta, har ransa yana tausaya mata yanda ta dauki sonsa da muhimmanci haka ta azawa rayuwar ta, wanda shi ko kusa baima yi mata irinsa, shi kawai dama tun usuli ra'ayin auren jinsin sune yakaisa ga fara kulata ynda taga tana nace masa dinnan tun school dinsu bawai wani son taba, ganin yanda take qara sautin kuknta ne yasahi cewa "kiyi haquri.., nayi fatan danazo yanzu inji kince dadynki ya amince da musuluntar ki daba haufi zan nunaki darect a matsayin fiance na, amman inda har yaqi amincewa i'am sorry to say babu lokaci nina wuce,, yana gama fadin haka ya koma motarsa ya dauko check ya rubuta mata kudi masu yawa ya kamo hannunta ya sanya mata takardar a jiki tareda fadin "kyayi wani abu dasu, nina wuce till another day" daga haka ya koma motarsa ya tasheta a guje yabar gun yabarta nan tsaye dafe dakai da gudu takoma gida tana rusa irin ihunsu na kiristianity kamar zata fasa musu anguwar dan maqotansu harsun fara fitowa leqe dan a zatonsu wani mugun abinne yafaru. daga nan wajen bash ya wuce ya iske dakin bash din a bud'e amman shi baya nan, waje ya samu ya kwanta bisa katifar bash din dake shimfide a tsakiyar dakin ya kwanta tareda sa hannuwansa 2 ya rufe fuskarsa yarasa mike masa dadi kam har yanxu shi. yana nan kwance har akayi sallar magrib daqyar yatashi yayi alwala yayi salla yana nan zaune kan praymat din har aka yi isha'e har lokacin bash bai dawo ba, gashi koda ya kira ya kira wayarsa a rufe yakeji, yana gama sallar ya miqe tsaye ya fice daga dakin ya shiga motarsa yayi gida, dady mua'zzam ne ya fito daga saman dakinsa yana ganin shigowar mahabeer din yasaki Murmushi yace "yawwa sojana ina son ganinka daman" daramm!!! mahabeer yaji gabansa ya fad'i batareda yasan dalili ba, shikam yanzu yana shakkun dud wata magana dazata fito daga fannin ahalin gidansu. zama yayi kusa da inda dadyn nasa ya zauna yace "thom dady"! dady mua'zzam yace "well daman gameda maganar matar da mike nema maka ne to cikin ikon Allah ba'a'je da nisa bama mun sama maka yarinyar da mukasan zata dace da rayuwarka, wacce annah da momynka dukkansu babu wanda baiyi na'am da ita ba, ba kowa bace kuma face ummu hani tanan gidan" da wani irin mugun firgici ya dago kai ya dubi dadyn nasa baisan sanda yace "what dady?!! 'yar aiki nan gidan fa kake nufi? daga bayansa yajiyo muryan annah tace "oh daman a kundin tarihin