Sashe 74
Mahabeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maman manal (Matar doctor) Allah ya hutar da zuciyar nan dai🤪😎 🌊🌊🌊🌊🌊 🅿4⃣6⃣ 🌊🌊🌊 Mahabeer kuwa ana cikin tsula ruwan saman nan yaja hannun sera basu tsaya ko ina ba sai falon gidansu, sunyi sa'a ba kowa kuwa a cikinsa nan ya zaunar da ita ya zauna nesa da ita kadan ya sake zuba mata idanunsa farare da suka ida washewa yanzun gaba dayansu, a hankali ya bude bakinsa yace "in tambaye ki sera man?,,,,, saurin gyad'a masa kai tayi alamun tana jiran tambayar tasa, gyara zama yayi yace "naceba toke bakida wani saurayi ne ke? sera tace ''em em ina dashi amman babana keson aura munshi ni kuma bana sonsa kai zance masa ina so,, hade fuskarsa mahabeer yayi tamau yace ''shuhhhh🤫,,!! kinga ni nan da kike ganina ga al'adarmu dud wata mace wacce mahaifanmu suka zab'a mana to mu su mike aure sam bama bijerewa umarnin iyayenmu kuma ninan da kike gani anmun aure matata tana gida nigeria kuma sannan ma kisani sera ni banda tsarin zama da wata mace sama da d'aya dan haka na gode da sona da kikeyi kawai dai inaga mu cigaba da zumuncin mu kawai hakanma is okey, ok? sam sam bataso jin hakan daga garesa ba harya miq'e zai juya ya tafi tayi saurin tashi tace "please sss waitt mahabber,,, ni koda baka aureni ba to kawai mu more rayuwarmu mana dan daga ganinka nasan zakayi qwazo ga mace please yhu agree?,, zuba mata idanunsa yasakeyi aransa rayawa yake miyasa sam bature baisan wani wai kunya ba?. a fili kuwa sake gimtse d'aurarriyar face nasa yayi cewa yayi "nooooo noooo sera hakan ba kyau, addinin mu ya hana adultery at all but now just kije ki auri zabin babanki wanda ya baki nikuma nagode da kulawarki kaina,, harya juya zai tafi tace da sauri "to naji amman tsayani na d'auko kayan wanki mu kaiwa sister dinka dan sun fara sake taruwa, mungode dan tana qoqari fa,,, tayi hakanne kawai danta samu ta bisa don ta dunga kallon sa kotaji dad'i dan kwata kwata bata gajiya da kallon kyansa ko Kadan a rayuwarta kkda kuwa ace zasu kwana a hakan ne bata damu ba ita,, dan dakatawa yayi bai jiyoba taji yace "wankin ya isa haka na hanata daga yau, ku dinga badawa ana wanko muku kamar yanda muma muke bayarwa dan aljannun wankin sun tashi daga kanta yanzu ta daina yi"!,, daga haka yayi wucewarsa yabar sera nan da cizon yatsa ganin haqarta bata cimma ruwa ba, pridge ta bude ta dauko wata qatuwar kwalbar giya ta zauna anan t dinga kwankwad'a saida tayi tatil sannan ta baje wajen tana surutai. tundaga falo kuwa ya dunga jin kukan ummu 'rasssss!!!! yaji gabansa ya buga, miye yafaru da ita to???!!! tambayar dayaiwa kansa knn, gudu gudu ya haye saman benen ya bud'e d'akin nasu ya shiga cn ya hangota bisa katifarta ta wni duq'unqune tanata kukanta, zama yayi gefenta yana fad'in "ke? ke? mine yafaru haka?, yayi maganar yana qoqarin riqo tafukan hannayen ta a cikin nasa,, da sauri ta warce hannunta daga nasa tareda dalla masa wata iriyar qatuwar harara ta koma taci gaba da kukanta mai shessheqa, mamaki abin ya basa kuma gashi taqi fada masa mike faruwa bare yasan kan zaren, miqewa tsaye yayi ya d'an wani tab'e red lips d'insa har zai wucewarsa yabar wajen harya fara taku biyu yaji yakasa barin wajen gaba day'a, tunowa da yanayin daya kasance da yarinyar d'azun yaji hakan yasake dawo masa, tunowa da santsin fatar jikinta da cikar mamanta burinsa kuma, tofa shine yasake sashi wani kwad'ayin qara tsayawa wajen wataqil kozai samu mai mai inyayi sa'a, a haka din kuwa ya dawo yasake zama yace cikin had'e fuskarsa "wai keto bazaki iya fad'amun abinda ya farun bane koko? mtsss zaki wani bi cikamun kunne da kuka kuma kinsan natsani hayaniya a tattare dani ko? cikin kuka yaji tace ''ai dole kace haka man inda katafi kaja waccen banzar kiristan sera din kun tafi wani waje tare ni kuma katafi ka barni babu abinda ya dameka,, ni kawai yanzun wlh banson ganinka dan Allah amakson na roqeka katafi ka koma can wajen kwanciyar ka inda daman... daman ba tare muke zama ba katafi katafi pleass amakson,,,, zuba mata idanunsa yasakeyi yana kallonta cikin nazari tuni ya fahimta babu abinda yake damun yarinyar face kishi,, kishi??? yasake tambayae zuciyar tasa,, to intana kishina knn tana sona kuma?,, wani b'oyayyen murmushi ya d'an saki gamida fiddo harshensa ya lashi red lips dinsa sosai yace "ke sona kikeyi ne har zakiyi kishi na daga na dan fara d'an latsaki d'azun? yayi maganar yana ciccijewa tareda shan qamshi, a fusace ta dago kai ta dubesa tace "wa keson naka? tabb!! Allah sawaqa mun wlh na soka kawai dai ina tayasu mah kishin kana tarayya da arniya ne"!!,, tayi maganar da qarfi sannan ta koma taci gaba da kukanta,, yatsunsa yasa guda biyu ya toshe kunnuwansa jin qarar kukan ta ishesa kuma sai yaji baji dad'in furucin ta datayi na bata sonsa datace, wani zafi zafi yaji a can qasar zuciyar tasa, kuma yaji sam yau yakasa yi mata fad'a bare wani zare mata idanunsa da wata tsawa kamar yanda yake matan, hasalima saiya bawa kansa laifi akan miyasa ya kama hannun sera suka tafi gashi yanzun yasa ranta ya baci tana kuka shi tsoron sa day'a ma kada wani ciwon ya sameta,,, dafe kansa yayi jin qarar kukan nata ya sake lunkuwa dole yasa sa tashi ya koma makwancinsa bayan ya d'age labulen dake tsakaninsu danya samu damar kallonta sosai batareda yasan dalilinsa nayin hakan ba,, tunani yakeyi a zuciyar sa bayan ya kwanta na shin wai wannan son datake nuna yanawa sera miyeshi? shi so din yaya ake ganesa? shi baisanma yanda so din yakeba bare harya yisa, dan siririn tsoki yaja dan rasa gane amsar dayake tambayar kansa da ita, runtse idanuwan sa yayi a zuciyarsa yace "mata matsala ne da saka wa mutum ciwon kai, haka suka kasance har tsawon kwana 2 sam ummu hani fushi take da mahabeer sosai ko ganinsa ma intayi da zarar ta tuno abun sai haushi yasake cikata iyakarta dashi ta kaimasa copee dinsa dud dare kamar yanda ya saba sha, sam mahabeer yakasa nutsuwa baisan daliliba, abun yakai yakawo har school inyaje tunanin yarinyar da damuwarta hanawa ransa saqat suke, kamar yanzu daya fito wanka daga toilet yagama shafe jikinsa da lotions dinsa gamida bin kowace ga6a ta jikinsa da wani sanyayyen perfume nasa ya shirya cikin q'ananun kayansa yarasa tayaya zai b'ullowa lamarin yarinyar da damuwarta da rashin ganin walwalarta ya hayyaci rayuwarsa, wata dabara ce yaji ta fad'o masa arai nan yasaki wani muskilin murmushi kawai yaci gaba da taje sumar kansa a gaban mirow dan ga alamun zai fita ne, da yake lokacin 2 ne na rana basu jima da dawowa daga school ba, yana hango ummu hani bisa katifara ta juya masa baya kamar mai barci amman tunani ne kawai takeyi can qasar zuciyarta tana yawan tuno abunda ya faru a tsakaninta dashi saitaita tuhumar kanta akan mima yasa ma harta biye masa mutumin dabawai sonka da qaunar ka yake ba, wata zuciyar tace mata "toke ummu miyasa ne zaki damu akan wani bai sonki? toke son nasa kikeyi ne? da sauri ta girgiza kai tareda turo d'an bakinta tayi jin tayi saurin runtse idanuwan ta tarasa tunanin da zatayi ma, jin wayarta dake gefen kanta tana ringing yasata dauka "sister nabee amaryar mu i miss you,, abunda take fadawa naneela knn data daga wayar,, ganin mahabeer ya fita daga dakin yasata bisa da kallo tana yatsine fuska ranta taji ya dan baci kadafa ace wajen sera zaije??? rassssssss taji gabanta ya fad'i, jitayi idanunta sunyi qwal qwal qwal tana shirin sakin kuka taji nabeela tace "habawa amarya yaya amarcin da dad'i ko?? da sauri ummu hani ta saita kanta ta dawo nutsuwarta danta ma manta suna waya,, wani iriyar qararren murmushin dole tayi sannan tace "aimu mun tsufa da amarci sister saiku sabbin hannu ay,, dariya nabeela tayi tace "kai wlh abun da dad'i kuma da wahala sis, har ummu hani zatace mi!? saitayi saurin yanke maganar da cewa ina angon halan ya fita? nabeela tace "eh yanzun nan nasamu ya qyaleni ya futa office,, nabee tace kinsami sister? girgiza kai ummu hani tayi cikin sanyin tace "a'a sister,,dariya nabee tayi tace "yanzufa in gaya miki sweet nawa ya gogar dani da daddan abunnan uhmmm har banson ya fita wlh ya barni a gida banson mata suna kallemun shi sam,, murmushi ummu hani tayi tace uhmm bakida dama sister" iya haka ta tsaya da maganar tunda batasan yanda abun yakeba ita kam bare har ta qarar,, nan suka jima suna fira sannan suka ajiye wayar,, su annah da momy umaima ummu hani ta kira sukaita suma har annah na tsokanarta da cewata gaida raggon mijin nata haka suka kasance cikin fira mai dad'i sannan sukayi sallama, har ranta ummu hani yanzun taji sauqin damuwar tata sai dai bataji dad'in yanda su baffan basuda waya dataji muryarsu suma yanzun taji dad'i a ranta, kwanciya tayi sosai tarasa mike mata dad'i ma haka ta kwashe tsawon awa biyu sannan taji ana danna intercome, abayarta ta dauro tazura bisa kayan jikinta ta sauko qasan falon ta isa ta bude qofar,, zaro fararen idanuwanta tayi waje dukknsu cikin gigita tareda dafe q'irjinta ganin yanda wani mutum mai sanye da fraren kaya ga alaman dai doctor ne, to shinefa taga ya riqo mahabeer ta kafad'arsa shikuwa mahabeer sai fmn sake langwabe msa yakeyi a jikinsa idanunsa a lumshe yake furta "arghh! wash!! cikina doctor marana ciwo muje in kwanta kona samu sauqi ban jumurin tsayuwan,, kuka ummu hani ta saka tana fadin "doctor please tell me..miye... miya samesa,, wayyoni Nashiga uku ummu hani ni yau"!! nanta qara bude baki tana kuka doctor yayi alamun ta basa hanya zasu wuto ciki,, da sauri ta wuce kuwa ta matsa harda ita aka kamasa aka kwatar bisa kujera sai faman matse matsen fuska yake alamun mai ciwo muraran,, dan babu wanda zai gansa yace ba ciwon gaske bane yake ba, dagowa doctor yayi ya dubeta yace "ya kuke dashi ne madam ? cikin rawar murya tace yay.. mahh.. mahabeerrrrr.... Mim...