Sashe 90
Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Kar'ba nayi tare da sawa a kunnena yace."My lov kada ki janyowa kanki lalura garin san gwanintarki kin son jama'a suna ta damunki da hayaniya please dan Allah ki kwanta ki huta nace kowaye yazo kada a bude masa kofa, sannan kuma kada kisawa jikinki ruwan zafi sosai ki sirka kafin kiyi wankan."
Nace"Kayi hakuri ni kaina wallahi so nake na kwanta abin ya gagara gabadaya mutane sun hana duk wanda yazo burinsa na saurareshi wannan dalilin yasa nake tsayawa muna gaisawa.'' Yace."Ni dai na fada miki ko auntis d'ina ne suka zo ban bada damar a bude musu kofa ba." " Yar dariya nayi nace Babbar magana kenan." Yace."Kwarai kuwa keda kin dauka abin wasa ne my lov lafiyarki ita kadai nake bukata kin haihu lafiya bana so hayaniyar mutane tasa miki ciwon kai."
Nace"Ka kwantar da hankalinka babu abinda zai sameni insha Allah jama'a kuma dole kayi hakuri dasu." Yace." To shikkenan zanzo na kasa na tsare a sashen duk wanda yaga ina gurin sai ya juya ya tafi " Dariya nasa ina mamakin rashin kawaicinsa, yace."Wato kin mayar dani sakarai ko."? da sauri nace"Aa ranka ya dade kayi hakuri sai kadawo ko." ajiyar zuciya ya sauke yace."Ki bawa Lawisa wayar zamuyi magana." Sai da yay maganarta wallahi na tuna tana dakin, cikin jin nauyi na mika mata wayar ta karba a sanyaye sukai magana.
To haka kwanakin haihuwata suka cigaba da tafiya cikin kwanciyar hankali da kulawa ta kowanne bangare Mamma na iya bakin kokarinta a kaina haka nan itama Tambaya nayin nata kokarin akaina da 'yan tagwayena da suka amsa sunansu Hassan da Hussaini Maimartaba kullum sai ya aiko da safe an daukesu an kai masa yayi musu addua sukan jima a gurinsa kafin a dawo min dasu..........Uwargida Huwaila ita ke shigowa kullum da Yamma ta gasa min jikina tayiwa yara wanka, ita kuma jakadiya itake kula damu da safe su aunty Safiyya kuwa shatara ta arziki suka had'o mana nida tagwayena kowanne da akwatinsa saqe da kaya, na samu kyautuka muhimmai ranar suna kowa kokarinsa ya faranta min nida 'ya'yana taro akayi sosai kuma aka tashi daga taron cikin koshin lafiya
*Bayan wata hud'u*
Yara sunyi wayo sosai dan har an fara koya musu zama......a lokacin ne kuma Allah ya azurta Lawisa da nata rabon ranar da suka tabbatar da cikin ita da mijin nata suka dinga murna da farin ciki......Ina zaune a kan kujera da Hussain a hannuna yana min rigima Ya shigo tunda na ganshi cikin walwala nasan akwai magana.
Zama yayi kusa dani tare da kar'bar yaron yana jijjigashi yace."Wai kukan me yake."? nace"Watakila yunwa yake ji wallahi kaga hassan duk ya shanye ruwan nonon." Hannu yasa kan nonon yana latsawa, na ture hannunsa da fadin"Kai kam kafiye wasa." Yace."Sumayya ban yarda ba kodai mitsininsa kikayi nasan Hussani da hakuri fa.".
'Yar dariya nayi nace"Sai dai idan kaine ka mintsineshi." shiru yayi min yasa yaron a kafada yana jijiigashi! Mariya ce ta fito daga kicin hannunta rike da fida cike da madara....har kasa ta durkusa ta gaishe da sauri ta miko min fidar ta bar gurin, nace"Kawoshi na gwada bashi madarar ko zai sha. miko min shi yayi na kar'beshi sai harbe harbe yake ina sa masa fidar a baki ya kama yana tsotsa
Ajiyar zuciya muka sauke a tare dashi, dan tsokana yasa hannu yana jan kafar Hassan dake kwance a gefena,
Murya na rawa nace"Dan Allah kada ka tsokaneshi kasan rigimarsa tafi ta Hussani." yace.""Ai so nake suyi ta baki wahala idan kikayi zuciya sai kiyi musu kani ko kanwa."
Wani irin kallo na watsa masa." dariya yasa tare da lakuce min hanci.....nace"Haba kai yanzu idan na samu ciki sai kayi murna ka duba fa kaga irin wuyar da nake sha da yaran nan."
Yana mirmushi yace."Meye a ciki sumayya a wuya bata kisa ko yanzu kika samu ciki ina farin ciki wallahi nasan ke 'yar baiwa ce Allah zai rangwanta miki."
A sanyaye nace"Hakane amma dai ni inaso yaran suyi kwari tukkuna idan kuma Allah ya kawo sai nagode masa." Yace." Yawwa 'yar albarka kinsan Lawisa ma Allah ya bata nata ko.'' na kalleshi cike da farin ciki nace"Ya za'ayi na sani tunda ba fada min kayi ba.".
Yace."Yau muka tabbatar da cikin tana can sai murna take." Nace"Kai kuwa ai dole tayi murna wallahi nima na tayata farin ciki Ubangiji Allah ya rabasu lafiya."
Ya amsa da ameeen yana min kallon kasa-kasa.....walwalar fuskata na rage nace"zaka fara ko."? Yana munafikin murmushi yace."Ki kira wa'innan yaran su dauki babys d'in nan muje daki."
Zum'bura baki nayi nace"Ni babu wani daki da zanje." Matsoni yayi yana sumbatar wuyana yace."Idan kuwa hakane lallai za'ayi abun kunya dan zan iya danneki a falon nan babu abinda ya dameni da hadimanki."
A sanyaye na kalleshi, girarsa ya daga min daso ya tabbatar min da maganarsa
Mariya na kwalawa kira da sauri tazo nace Ki goya Hassan kuje can gurin Mamma." da sauri tace"To ranki ya dade." Mikewa yayi ya shiga daki......ban bi bayansa ba sai da na tabbatar da cewa Mariya ta tafi da yaran sannan na bishi dakin.
*BAYAN SHEKARU GOMA*
Alhamdulillahi abubuwa masu kyau da marasa kyau sun faru a cikin wannan shekarun da suka wuce a cikin abubuwa masu dadi da suka faru a cikin shekarun da suka gabata Allah mai kowa da komai ya azurta Doctor Aliyu da da zuria maza da mata guda goma Sumayya nada shida hudu maza biyu mata yayinda Lawisa keda hudu mata biyu maza biyu, bayan wannan baiwar da Allah yayi masa sai ya daukaka darajarsa ta bangaran aikinsa na likitanci gwamnati ta d'orashi a kan babban matsayi saboda irin gudumawar ya dinga bayarwa a zamanin daya wuce Doctor Aliyu Abdul-aziz babban likita ne da duniya tasan da zamansa..............Abubuwa na rashin dadi da suka faru a masarautar kuwa shine rashin Jajirtattun mutane da akayi wato Baba Waziri da Lawi mahaifin Sumayya, mutuwar wad'annan bayin Allah ta girgiza jama'a Maimartaba Sarki Abdul-aziz yasha kewa da alhini kafin ya barwa Allah sabida yasan shi kansa idan lokacinsa yayi tafiya zaiyi inda sukaje, sai ya kwantar da hankalinsa ya cigaba da gudanar da mulkinsa cikin tsari gami da bin dokokin ubangiji gefe guda kuma yana nunawa 'Ya'yansa Ali da Shatima yanda ake gudanar da mulki akan bigire na gaskiya da adalci! Aliyu da Shatima yanzu suna a matakin shekaru ar'bain da biyar a duniya kowanne ya mallaki hankalin kansa a cikinsu Allah ne kad'ai yasan wanda zai gaji mulkin masarautar...........
*Daga karshe nake cewa Ubangiji Allah ya za'ba abinda yafi alkairi a tsakaninsu".*
*'KWARYA TABI 'KWARYA*
*END🔚*
*ALHAMDULILLAHI*
_Jama'a nan na kawo 'karshen wannan littafi mai suna 'KWARYA TABI 'KWARYA Ina rokon Ubangiji Allah ya yafe min kusakuraina ladan dake cikin littafin Allah ya sadamu dashi bakid'aya masha Allah ina mi'ko sa'kon godiyata gareku masoyana wanda na sani da wanda ban sani ba ina godiya kwarai da gaske ina kuma alfahari daku mutuka ina rokon Allah ya bani ikon da zan cigaba da nishad'antar daku da kuma fad'akar daku..........Taku akoda yaushe take muku fatan alkairi🙋ðŸ¼â€â™€ï¸_
*_DAN DARAJAR ALLAH DA MANZON ALLAH KADA KI/KA HAD'A MIN DOCUMENT NA LITTAFIN NAN BAKU SAN YANDA NAYI NA RUBUTA ABUNA BA KADA KU HAD'A MIN DOCOMENT KUYI MIN SHARING A GRUOPS BAYAN KUN SAN NA KUDI NE KU BAR MIN LITTAFINA NA IYA HADA DOCOMENT DINðŸ‘ðŸ»ðŸ‘🻠KAJI TSORON HAKKIN DA BA NAKA BA_*
*Na kudi ne*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin littafin ga yanda abin yake........Completed #600 ne sai ayi min magana ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*